← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 276

Sashe 224

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuma Usaini haushi ya ji yadda suka tsayar dashi a bakin gate suna tuhumarsa domin ba mu yi kama ba ko daya gashi kuma ya ce musu shi kanina ne kuma zuwansa daya gidan shiyasa suke yi masa wanna titsiyar Hamusu suka fi shedawa."
Ayuba ya biyo shi a baya yana dan bashi ha'kuri na ce ya je kawai babu komai suma suna kan aikinsu ne babu lefi don sun ga bak'uwar fuska sun nemi dalili.

Da yake safiya ce ko ruwan da na ajiye masa bai sha ba muka gaisa sosai da bayan rabuwa zafin nemansa ya sanya shima ko gidana na Abuja bai taba zuwa ba kullum yana kasuwa a sanin da na yi masa tun Yana yaro manemi ne baya zama duk wasu lissafe-lissafe da za mu yi ta waya muke yin komai kamar dai yadda muke yi da Hamusu abinda ya gaya mini shima Usaini haka zai gaya mini sun yi bala'in cirar tuta a wajena dalili kuwa anan shine ni kaina sai dai na ce dukiyar itace tawa ta farko kenan da na zuba domin gudanar da kasuwancin abinda zai ru'banya daga baya kuwa duk kokarinsu ne kuma duk inda suka hango cigaba da sauri za su gaya mini a jarraba ko za a samu nasara.

Shekara na yi kuwa za a yi lissafi a fitar da riba da uwar kudi a sallami kowa hakkinsa.

Usaini yana tura kayanmu gari-gari ta hanyar yanar gizo an san shi sosai kamar dai yanzu da yake gaya mini ba'ki sun zo daga nijar domin sayan kaya ba ni tamtama a online suka had'u."
Ya dinga jan Minal da wasa tana janyewa na rashin sabo har sai da ya samu nutsuwa tukkuna na dube shi a tsanake na ce."kasan dalilin kiran ka da na yi?"
Ya girgiza kansa a hankali yana fad'in.

A a anti amina Allah ya sa lafiya."
Na ce." Lafiya lau kuma alheri ne."
Sai ya saki fuskarsa sosai har da gyara zama yana fad'in." To Ina jinki anti ko za mu sake bude wani shagon ne?"
Na ce." A a matar aure na yi maka."
Saranda ya yi ya zare ido yana fad'in." Matar aure anti a ina take kuma? ban gama gini na ba dalilin da ya sanya kenan na janye idona daga kan 'yan mata domin ba ni so na fara soyayya da budurwa iyayenta su ce na fito.

Ni kuma nafiso sai na kammala komai a tsanake sai na nemi mai hankali daidai da ni na aura."
Murmushi na yi Ina kallonsa yana ta jero mini bayani wanda na tabbatar da cewa gaskiya ce tsantsa kuma duk maganar da ya furta tana fitowa ne da can kasan zuciyarsa.

Na ce." Maganar gini mai sau'ki ne Usaini don ma dai ka d'auki irin na zamani da kyale-kyale ai da tuni ka gama ko ba shine wanda ka ta'ba turo mini ta waya ba kwanaki."
Ya ce." Eh shine gidan anti amma yanzu aiki ya kara nisa."
Na ce." To alhamdulillahi Usaini wata yarinya ce na yi maka sha'awarta nutsatstsiya kuma 'yar Malamai idan har Usaini ya samu nasarar mallakar yarinyar nan ina yi masa albishir da cewa ya gama dacewa da ma'aratussaliha."
Ya yi murmushi yana fad'in.'' Kai anti Amina wannan yarinyar a ina take yadda na ji kina kwarzantata wallahi har kin kwadaita mini ita a cikin raina."
Nasa dariya ina cewa." Ka ji d'an gari ko, sai ma ka ganta doguwa chocolate color ga ka farar fata yaranku za su zama wata kala masu kyau."
Ya sunkuyar da kansa yana murmushi."
Na ce." Ka amince kuma ka bar mini wuka da nama a hannuna?"
Ya gyada kansa yana fad'in." Na amince anti Amina wallahi ba ni da ja kuma ba ni da haufi a kan ki na yi farinciki da wannan zabin da ki ka yi mini tun banga yarinyar nan ba har ta zauna a zuciyata.

Fuskata ta kara yalwata da annashuwa na ce." Aikuwa na gode sosai na ji dadin wannan alfarma da ka yi mini amma yau din nan nake so ka sanar da Ummanku duk abinda yake faruwa kuma ina son sanin matsayin jininka."
Ya ce." Zan gaya mata a yau din in sha Allah.

Matsayin jinina kuwa( O) ne genotype (AA)"
Wani irin sanyi ya sauka a zuciyata shikkenan an samu yadda ake buk'ata ta wannan bangaran akwai dacewa da cancanta wancan bangaran ne kuma ban san wainar da suke toya ba.

Gabana ya fadi na daga kai na dubi agogo sha daya saura kuma yadda suka tsara jadawalin d'aurin auran bayan an yi sallar Juma'a ne.

Na saki ajiyar zuciya ina fad'in ." Ma sha Allah ta kowane bangare an samu daidaito idan har Allah Ya kaddara wannan auran Usaini ina yi maka murna sosai domin ka yi mata."
Ya ce." Na gode sosai anti Allah Ya saka da alheri ya kuma kara girma abinda ki ke yi mana na zumunci Ubangiji Allah sanya miki a mizani Allah Ya jikan iyaye da kakanni."
Na dinga amsawa da Amin Amin Allah Ya taimake mu gabad'aya."
Muka yi sallama kafin kafin ya tashi na gaya masa zuwa dare zan kira shi domin karin bayani.

Ya kama hanya ya tafi na zauna cike da nazari da zullumi hankalina kuma yanzu ya yi can garin bunkure ko a wane hali ake yanzu bai kira ni ba nasan kuma tuntuni ya isa garin tunda babu wata nisa.

Na d'auki wayata gabana na d'an fad'uwa na lalubi lambarwa wayar na shiga sai dai har ta katse bai daga ba.

Na sake kira a karo na biyu nan ma bai daga ba jikina ya mutu na ajiye wayar da rashin kuzari."
BUNKURE.

Cike gidan yake zuri'ar Malam D'aha 'ya'ya da jikoki kadai sun isa gayya ba sai sun gayyatowa kowa ba.

Amma da yake wannan sha'anin na mussaman ne a gare shi gidan cike yake da nau'in ba'ki daga gari gari nasa da na matayensa mussaman uwar bikin uwargidansa mahaifiyar amarya wato Inno.

An gama towon d'aurin aure suna ta malmale shi a leda ana zuba shi a manyan kuloli gefa guda kuma kirigar tukuwanan miya ne guda biyu kan murhu suke ta cin wuta suna zab'abbaka da tashin kamshi mai shanana a saman miyar.

Yaran mata surukan gidan suna can bakin turgijejiyar bishiyar darbejiya da ba a samu nasarar tun'buketa ba a lokacin da aka sabunta gidan suna ta d'aura zobo a leda suna zuba shi a wani mazubi mai girma.

Kowa ka gani cike yake da annashuwa da farinciki daka kan iyayen 'ya'yansu da jikokinsu da surakansu.

Zaure malamin kuwa daga can bayan gidan akwai kofar da aka yi masa ta mussaman domin ba'kinsa wanda Malam Rabi'u ya buk'aci da a yi hakan dalilin gidan akwai matansu babu cancanta maza ma bambamta na shiga gidan kai tsaye duk da sashen malamin daban yake amma dai tilas ta tsakargidan za a bi kafin a isa zauran nasa kuma wasu lukutan iyalansu na fitowa.

Ta wannan kofar suka shiga zauran malamin shi da Dr Iliyas ba kowane ya san da zuwan na su ba.

Malam D'aha na sanye da manya kaya babbar riga da 'yar ciki shadda mai kyau daidai gwargwado da d'inki manya cike yake da Kamala da nutsuwa amma kana duban fuskarsa za ka gane cewa lallai yana cikin farinciki dalilin wanzuwar wani lamari da wata'kila ya jima da shi a zuciyarsa.

Tun bayan gaisuwar da suka yi da shi sai jikinsa ya kara mutuwa kwarai da gaske ya ji a ransa baya buk'atar wannan annashuwar da take fuskar malamin ta dusashe
domin kuwa lamarin da suka zo dashi gare shi babba ne wanda zai iya rushe duk wata walwalarsa.

Lallai ne akwai buk'atar zama akan wannan mas'alar mai sark'akkiya kamar yadda mai d'akinsa ta gaya masa ya makara a yanzu ba lallai ne malamin ya yarda da uzurinsa ba tunda ai ya jima da bashi yarinyar mai yasa bai kawo tasgaro ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi
Jikinsa ya yi tubis bakinsa ya mutu d'akin ya d'auki shiru bayan gama gaishe-gaishe daga shi har Dr Iliyas din sai zare ido suke yi domin dai malamin bai fito ba sai da shirya Kuma yawanci irin wad'annan malaman masifar kwarjini ne da su da cika ido.

Dr Iliyas duk 'kumaji da karsashinsa na k'wararran likita sai da jikinsa ya mace ganin yadda wanda ya gayyato shima jikinsa ya yi la'asar sai rarraba Ido yake yi yana sinne kai wannan lamari yana da wahalar fahimtarwa a wajen irin wad'annan mutanan da tauhidi ya yi wa k'awanya da kuma rashin samun ilimin boko mai zurfi ga kuma rayuwar karkara abin dai goma da ashirin.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700....VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*151*
Suka yi shiru gabad'aya jikinsu a mace kamar ba wad'anda suka zo d'aurin aure ba mussaman shi angon da gabad'aya rashin nutsuwa ya gama bayyana a tare da shi.

Ana haka Malam Nuhu ya shigo shine babban d'a ga malam D'aha daga shi sai Rabiu amma shi ba a cikin gidan yake zaune ba yanzu da can dai ya zauna dai a gidan kafin daga bisani ya gina nasa a gaba da gidan Malam din da kad'an
Sa'ida lokaci yakan tafi cira ni Katsina idan an samu amfanin gona ya je ya kasa ya sayar matansa hud'u daya ta rasu sai uku yanzu da yara ashirin da bakwai.

D'aurin auran ya kawo shi ya kuma kwana biyu cikin iyalinsa kafin ya koma.

Akwai sanayya a tsakaninsu tun lokacin kuruciya amma dai ba kamar yadda suke da Malam Rabi'u ba domin dai shine sa'ansa.

Malam Nuhun ya d'an girme shi tunda sakon Malam Rabi'u ne girman dai ba wani mai yawa bane sai dai da yake shi mutumin karkara ne duk ya manyata sosai ya tsofe ga d'auwaniya da lissafin rayuwa ga hidimar iyali duk mai mace uku a yanzu da yara sama da ashirin da biyar kuma yana ciyar dasu kowace rana babu tangard'a lallai shi ya kamaci da a kira namiji dalili anan shine da yawa maza mace daya ma suna gaza ri'ke ta balle mace biyu da yaranta.
Chapter 224 · 0% Book details