Sashe 256
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na bar ta a kicin din goye da Hassan ya yi bacci na fito falon na same su a zaune Inna Uwani ta d'auki Usaini yana saman cinyarta da abin wasansa a hannu.
Na d'an saki fuskata ina yi musu barka da zuwa na zauna kujerar dake kallonsu yaran gabad'ayansu suka shigo Khalil twins da Minal wurina suka rugo a guje k'ananun shi kuma Khalil din yana ta dariya kafin ya d'an risina yana fad'in." Mama ina yini?"
Na amsa da kulawa ni ma ina dariya na ce." Kai ya na ga duk ka yi zuru-zuru azimin nan fa bai wajaba a kan ka ba."
Ya sa dariya yana fad'in." Ko bai wajaba a kaina ba ba zan asha ko daya ba Mama.
Minal tana ta'ba mini cinyata ta ce." Mama ni kin ga haka na yi." Ta had'a yatsunta biyar ta d'ora d'aya a kai."
Na bude baki cikin mamaki ina fad'in." Da gaske." Karaf Usai ta buge hannun tana cewa." Ma'karyaciya ko daya ba ta yi ba wallahi." Cikin wasa ta yi maganar don har tana dariya ma.
Abinka da yarinta ita kuma Minal din sai ta fashe da kuka tunda dama dangwalolo ce.
Nan da nan Hauwa ta 'bata fuskarta na ji lokacin da ta ja tsaki mai tsayi.
Ina Uwani na fad'in." Ke kam Usaina kin fiye saurin hannu wallahi menene abin duka Kuma?"
Khalil da sauri ya ce." Ba dukanta ta yi ba fa Inna."
Hauwa ta harareshi tana fad'in." Ba mu da ido ko kaine kake da Ido don ubanka zaman da suka yi a can ma kenan ba dukanta take yi ba."
Ya yi shiru yana yin fuskarsa ya canza.
Na ce." Ai saurin hannu gare ta na gaya mata kuma 'kanwarta ce."
A d'an sanyaye ta ce." Ban doke ki ba ko Minal?"
Sai ta d'aga kanta.
Tsakanin yara ba a shiga Usai din ta sanya hannu tana goge mata fuska.
Daga haka na ce." Ku je dakinku ku zauna kafin mu gama gaisawa..
Suka kama hannunta suka bar wajan.
Cikin kulawa na fara gaishe da Inna Uwani itama ta amsa a d'an sake ta yi mini ta'aziyya tare da jajanta mini rashin da aka yi.
Haka itama Hauwan mun gaisa babu yabo babu fallasa ta yi mini gaisuwa kafin ta dubi Khalil tana d'an harararsa ta furta." Ba ni ledar kayan nan?"
Na dube shi da sauri wata babbar leda ce da ya shigo da ita sai ya ajiyeta gefan kujera.
Ya d'auka ya mika mata ta kar'ba kafin ta kalle ni tana fad'in." Babansu ne ya bada kudi aka saya musu 'yan kanti wurin Sadiya wannan shekaran ta kawo kaya sosai ai baki mance ta ba ko?"
Na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba
Na gyada kaina a nutse ina fad'in." Ban mance ta ba." Sai ta mi'ko mini tana ce wa." Na ga sun yi kyau sosai set takwas ne kowanesu hud'u."
Na kar'ba na ajiye a gefena ina fad'in." To madallah."
Suka amsa tare kafin ta cigaba da cewa." Takalma ne kawai babu sizi d'insu a wurinta shine ban ce ta aiko ba amma gabad'aya yaran an saya musu da mayafai sauran suna wurin telansu yadda ya ce cikin satin nan zai kawo."
Na ce." To shikkenan wannan na Hasan da Usaini ne kenan?" Ta gyad'a kanta na ce." Ina na su Hassana?" Sai ta d'an diririce kafin ta ce." Yana can gida zan aiko miki da su gobe ko kuma an jima da daddare.
Shiru na yi ban ce komai ba.
Hadiza ta fito daga kicin da yaron a bayanta cike da walwala a fuskarta ta zauna suna gaisawa.
Inna Uwani ta yi caraf ta ce." Wannan kamar 'yar uwar nan taki ko?"
Na ce." E, itace Hadiza ba?" Sai ta ri'ke bakinta tana fad'in." Itace ta lalace haka sai ka ce wadda take d'auke da siga ko kanjamau!"
Maganar ta dake ni sosai cikin fad'uwar gaba na kalleta bakina sai ya yi nauyi na kasa ce mata komai.
Hadiza cikin gaggawa ta tashi ta bar wajan domin itama da alama maganar da Inna Uwanin ta yi akanta ba ta yi mata dad'i ba.
K'asa na yi da kaina zuciyata na hantsilewa akwai dalilan da suka sanya nake d'agawa matar nan 'kafa ba wai don tana uwar kishiyata ba ina kallonta kamar Hajja tunda ciki daya suke amma an kusa kaiwa matakin da zan fara mayar mata da raddi a duk lokacin da ta yi mini wani rashin hankalin.
Ya sauko ya same mu a zaune a falon ya zauna gefana yana kallon Inna Uwani da ta k'irkiri yi wa Usaini wasa har da yi masa rawa tana dariya shima yaron yana yi.
Hakan kuwa ya yi masa dad'i sosai aka ce wai mai d'a wawa sai ya shiga washe bakinsa tana fadin." Yara duk sun yi wayo kamar ba biyu ba sun yi kyau uwarsu na da kafar nono mai kyau."
Ya ce." Haka aka yi goyon 'yan uwansu ma." Ta miko mini yaron tana fad'in." Ai ban mance ba.
Ubangiji Allah Ya raya mana su domin su zama cikon addinin musulunci duniya kuma ta amfana da su."
Ya dinga amsawa da Amin ya rabbi Inna Uwani Ina godiya sosai."
Suka tashi tafiya bakina ya mutu kwarai dangane da salon da suka shigo da shi.
Da k'yar na ce su gaida gida ya tashi ya bi bayansu kafadarsa sa'be da yaron.
Ina nan zaune ya dawo ya zauna cikin walwala a ganinsa mun fahimci juna tunda gashi har ya sakko ya gan mu kuma yaronsa na hannu Inna Uwani tana yi masa wasa wannan ne dalilin da ya assasa masa annasuwa da farinciki bai san da cewa wani sabon salo ba ne.
Na zazzage kayan yaran ina dubawa.
Eh rigunan manya ne kuma sun yi kyau sosai zan iya kar'ba na yi musu amfani da shi tunda an riga an saya na su Hassana ne ban ga ni ba.
Na juya ina tambayarsa "Ta kawo mini kayan su Hassan ban ga na su Hassana ba?"
Ya dube ni da kulawa yana fad'in." A a ba ta had'o da su ba ne?"
Na ce." Eh" Sai ya dan yi jim kafin ya nutsu yana kallona ya furta." Ki bar mata su su yi sallah a hannunta idan hutun makaranta ya 'kare sai su dawo gabad'aya jiya ta fara gaya mini cewa tana son yaran su yi mata hutu.''
Girgiza kaina na yi tare da cewa." A a, yaranta dai ka kai mata su amma nawa yaran su dawo gidansu ba ni son abinda zai daga mini hankali a yanzu dai cikin ibada muke abinda ba zai yiwu ba ne.''
Ya d'an 'bata rai yana fad'in." Ke dai duk ta inda aka biyo miki ba a yi miki gwaninta Amina menene lefin nan da can kuma duk gidana ne akwai buk'atar a ko'ina yarana su sake su kuma yi sabo, ki yi hakuri ki bar mata su hutu kawai ta buk'aci da su yi a hannunta sai su dawo, ki duba kawaicin da ta yi miki a kan nata yaran mana."
Na sake girgiza kaina a karo na biyu na furta." Na gaya maka fa ba zai yiwu ba ai ni ban buk'aci zaman yaranta ala dole a tare da ni ba.
Kai ka kawo mini su kuma ba zan hana su zama ba tunda gidan ubansu ne.
Maslaha anan shine ka kwashi yaranta a kai mata tunda zahiri ana shiga hakkinta alamu sun nuna kad'aici ya isheta hayaniyar yara take buk'ata.
Kowa ya rike nasa shine zance na gaskiya."
"Kamar yadda na isa na bata umarni ta bi ke ma haka za ki bi.
Na gama yanke magana yara za su yi hutu gidan Hauwa idan sun 'kare su dawo ku cigaba da zama gabad'aya tuntuni yaranta dake suka saba kuma suna kaunarki babu wani dalili da zai sanya ni raba su dake saboda suna sonki itama ta yarda da hakan."
Yana gama fad'in haka ya d'ora mini yaron saman cinyata ya kama hanyar samansa yana magana." Idan Hakan bai yi miki ba ni ma sai ki raba ni biyu ki d'auki b'angaran da kike so a jikina sai ki bata rabin tunda duk a kaina kuke wannan 'kiyayyar junan idan na mutu kowa zai huta ai."
Na dinga kallonsa har sai da ya gama hawa steps na daina hangensa na dawo da kallona kan yaron da yake ta zura hannunsa cikin rigata nono yake nema.
Babu kuwa halin ba shi domin tunda suka fara wayo nake had'a musu kamu irin wanda Sultan ya sha yana kan matakinsu balle yanzu da ake yin azimi ba ni yarda su tsotse ni da tsotsan jaraba.
Bai sauko ba sai daf da za a sha ruwa mun gama aiki Hadiza na gyara kicin din muka dinga jin kuka a falon na fito da saurin gaske. wanda ya yi daidai da saukowarsa Minal ke kuka tare da Sultan Hauwa ta turo mai aikinta Ladidi wai su tafi tare.
Sauran sun yi cirko-cirko.
Kuka fa sosai Minal ta ri'ke hannunsa tana fad'in." Baba ba kaine ka ce mu zauna a can ba sai Mama ta dawo, to ina za mu je ai nan ne gidanmu Ladidi za ta d'auke mu."
Sultan da tafiyarsa ta yi k'wari sosai ya taho da d'an gudu ya rige gefan rigar uban yana kuka ya sunkuya ya d'auke shi yana kallon Khalil ya ce." Je ka dauro alwala lokacin sallah ya yi." Yaron ya juya da sauri ya bar wajan.
Sai ya dubi Ladidin yana fad'in." Je ki abin ki idan an jima zan shigo da yaran."
Ta risina da sauri kafin ta juya ta kama hanyar fita.
Khalil ya fito da alwala sai ya dire Sultan din a kasa ya ce." Ri'ke hannunsa muje massalacin tare."
Ya yi gaba da sauri su kuma suka bi bayansa..
Na dube su Usaina ta ri'ke hannun Minal din tana zaune dirshen 'kasan ties amma kukan ya tsagaita.
Na ce." Ya isa haka ta shi kuje ku yi alwala a yi sallah sai a ci abinci ko?'
Ta daga mini kai tana sakin ajiyar zuciya ta tashi 'yan uwan suka tasa 'keyarta zuwa dakinsu.