Sashe 204
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban saurareta ba na shige dakinsu Baba Tabawa tana ta kici-kicin bashi kamun data dama masa yana cinyarta a zaune yana kamo hannunta.
Na sake sauke ajiyar zuciya ta jin dadi ganinsa kalau har ma yana d'an wasansa.
Na zauna har sai da ta gama bashi ta gyara masa jikinsa da bakinsa tukkuna na bude maganin na fara nuna mata yadda za ta bashi koda ta kammala sai ta sanya shi a kafad'a ya yi gyatsa sannan ta d'auki towel dinsa ta goya shi.
Yana ta gwalantu irin na yara.
Fitowata daga d'akin ya yi daidai da lokacin shigowarsa.
Dama ya ce da wahala ya kwana.
Na yi kokari sosai wajan daidaita yanayina na yi masa barka da zuwa ya amsa da kulawa yana fad'in.'' A kawo mini abinci Amina." Ya kama hanya zai hau samansa da wata leda viva a hannunsa.
Yaran gabad'aya suka fito daga kicin har da Mairo jin maganarsu ya sanya ya dakata ya tsaya aikuwa suka nufe shi da sauri ya rirri'kesu yana dariya suna ta jero masa sannu da zuwa.
Ina kallo ya dubi Khalil cikin nazari ya riko hannunsa yana fad'in." Kai matsalata da kai zurfin ciki da miskilanci ko akwai abinda yake damunka?"
Ya yi shiru yana sunkuyar da kansa.
Karaf muka ji Minal na ce." Sultan ne ya mutu ko Hassana, shikkenan ya mutu, shikkenan ya mutu." Ta dinga fad'a tana tafa hannunta.
Na ji kamar an rad'e mini guiwata da tar'barya.
Nusaiba ta fito daga kicin din ganinmu a tsaye ya sanya ta d'an daidaita yanayinta ta dan risina tana fad'in.''Baba sannu da zuwa?"
Ba a hayyacinsa ya amsa ba saboda maganar Minal ta dake mu gabad'aya sai Khalil ya fara hawaye.
A lokacin ne ya kara kid'imewa yana fad'in." Sultan ne ya rasu Amina?".
Na ce." A a lafiyarsa lau me yasa za ka yarda da maganar yara." Ni kaina na fad'i maganar ne wadda nake da tabbacin cewa ba zai yadda da ita ba amma don ya gazagata na ce da Mairo ta kira Baba Tabawa.
Ta kuwa fito da yaron goye a bayanta na ce." Kwanto mini shi." Ta yi yadda na umarta tana gaishe shi ya amsa babu sukuni.
Inda yake na nufa da yaron a hannuna yana ta bacci.
Na ce da yaran su je su yi sallar Isha'i su ci abinci da sauri suka bar wajan shi kuma ya kar'bi yaron muka haura saman a tare.
Leda viva dana kar'ba a hannunsa a lokacin da zai kar'bi yaron a hannuna na ajiye can gefa ya zauna da shi a hannunsa yana dudduba shi yake fad'in na dawo da farinciki sakamakon albishir din da Dr Sailuba ta yi mini Amina amma kuma me yasa za a yi mini a haka har yanzu a cikin gigita nake wallahi dalili ta yi mini bayani shima bai ji dad'i ba yana zazzabi hak'ori hakane ko?"
Na ce." E, yau tun safe ya tashi da zazzabin dalilin da ya sanya ni kiran Dr Sailuba kenan amma tsakani da Allah me yasa zaka yarda da maganar yara?"
Ya furta." Me yasa ba zan yarda ba lallai ne fa akwai abinda ya samu yaron nan ko ga yanayin yadda na ga tsoro da firgici a idon Khalil yarinyar nan Minal ba za ta yi karya ba."
Na ce." Ai ga yaron nan a hannunka ka duba shi sosai ka gani."
Ya kuwa fara duba shi har da cire masa kayan jikinsa ya bar shi da pampas yana jujjuyashi shi kuma sai dariya yake yi cikin ikon Allah zazza'bin ya sauka don dana ta'ba jikinsa babu zafi.
Na yi murmushi ina kallonsa na furta." Me ka gani a tattare da shi."
Ya saki ajiyar zuciya yana fad'in." Ban ga komai ba amma har yanzu ban yarda ba akwai abinda ake b'oye mini."
Na ce." Don Allah mu bar maganar nan mu yi wata ka ji."
Ya tsira mini ido na dan wani lokaci kafin na ji yana fad'in." Kin kyauta Amina ke ba za ki daina abinda ki ke yi ba ko?''
Nasan akan abinda yasa ya fadi haka na ce." Ka yi hakuri don Allah ina da ciki Dr Sailuba ta gaya maka ko?''
Ya gyad'a kansa yana cewa ta gaya mini amina amma mai yasa ki ke yi mini haka ba na fa jin dad'i tuntuni na gaya miki mai zai sanya abin alheri ya same ni a dinga b'oye mini wannan zalinci ne da d'aukar hakki wallahi."
Na ce." Ka yi hakuri ba zan sake ba."
Yaron na kar'ba ina mayar masa da kayansa.
Shi kuma ya cire agogon hannunsa ya zare gilas din da hular kansa ya tashi tsaye tare da cire babbar rigar ya ajiye saman gado.
Toilet ya nufa bai sake ce mini komai ba na sauka kasa da yaron na mayar dashi wajen mai rainonsa.
Kicin din na nufa sun kammala komai na shirya masa abincin kamar yadda ya buk'ata da ya shigo
Na same shi yana sallar Isha'i na ajiye tiren a wurin da yake zama sai da ya jima saman daddumar yana addu'a kafin ya shafa ya taso yazo ya zauna na fara ko'karin zuba masa abincin yana ta kallona.
yana ci muna hira gidan Malam 'Daha da irin sallahun gaisuwa da godiyar da suka bashi zuwa gare ni.
Nan yake yi mini bayanin abinda yake cikin leda viva da take ajiye gefe naje na daukota kayan dake ciki na fito dasu sassa'ken gargajiya ne da saiwowi gasunan kala daban daban.
Ya fara yi mini bayanin yadda za a yi da ruwan rubutun dake d'aure a waya farar leda irin mai zurfin nan za a dafa maganin a tace a sha tsayin sati daya kullum karamin kofi d'aya.
Babu maganar sauran asiri a tattare dashi kamar yadda malamin ya yi masa bayani matsalar dai aka samu har ta ta'ba masa lafiyarsa wannan mummunan d'aurin da aka yi masa tunda dama an yi shine akan manufofi da yawa.
Idan har an dage da magani da kuma addu'a karfi da mazantakarsa zai dawo fiye ma dana baya.
Sai dai ya ce kada wata mu'amula irin ta aure ta wanzu har sai an gama shan maganin tukkuna.
Ai a daran ban bari gari ya waye ba na dafa maganin na tace shi sosai na zuba cikin wani dogon jug guda biyu na kai saman nasa na ajiye kullum da safe za a sha kofi d'aya idan ya yi karin kummalo.
Da safe kafin na fita falo Sahura ta kira ni a waya cikin annashuwa da farinciki take fad'in." Amina don girman Allah ki taya ni da godiya wurin Yallabai jiya na kar'bi takardar gidan da ya yi mini alkawari zai ba ni anan hotoro wajan ma'aikatarmu gida mai kyau Amina ginin zamani gashi ya sanya an zuba mini komai tarewa kawai zan yi."
Sai ta rushe da kuka.' har sai da na ji wani iri a raina na ce." Haba Sahura menene kuma na kuka don Allah ai kin wuce haka a wajenmu don girman Allah ki daina wannan kukan ba na so."
Na ji ta tana fad'in." Ya zama dole na yi kuka Amina na dad'i ne wallahi na rasa inda zan tsoma raina ba ki ga gidan ba mai yalwa da wadatattun d'akuna ga ababen more rayuwa kuma wai gidana ne mallakina."
Na ce." To menene a ciki ai komai rabo ne, ki godewa Allah kawai."
Ta ce." Shine abin godiya a koyaushe amma dai ya zama tilas na godewa wanda ya zama sanadi."
Sallama muka yi da ita ban kuma yi kasa a guiwa ba yanzu zan je na sake jadadda masa godiyata.
na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Sai da na leka su Baba Tabawa tukkuna na duba Sultan ta yi masa wanka yana ta bacci cikin net dinsa muka gaisa sosai da su ina tambayar jikinsa ta ce ai ya warware sosai don jiya ma kwata kwata bai kwana da zazzabin ba har gari ya waye.
Na godewa Allah a cikin raina na fito saman zan nufa na samu Hauwa a kan kujera ita kadai a falo a zaune muka kalli juna na ganta a hargitse duk ta muzanta na janye idona da sauri daga kanta ai hausawa suna cewa.' Duk wanda ya hana uwarsa bacci to shi ma watarana bai zai rintsa ba kana ganinta kaga wadda take cikin tashin hankali da damuwa ashe tana son yaron ta cillar dashi ta tafi gashi yanzu 'kiri-'kiri tana kuka da nadama 'ya'yanta suna gudunta har dai mai suma saboda ta daukeshi Khalil da Minal kuwa ba na tsammanin ma suna yi mata magana domin duk gidan kamar mujiya haka ta zama.
Ina hawa saman ya ce na had'o masa shayi haka na sake sakkowa na shiga kicin na had'o kayan shayin na fito still dai tana zaune a kujera shiru ta d'an ba ni tausayi amma kadan ban kalleta ba na ji ta kira sunana na tsaya tare da dubanta.
Maganar dai jiya ta sake maimaita mini kada na gaya masa don ta d'auki sultan ya suma."
Na b'ata Raina ina fad'in." Wai me zai sanya na gaya masa ne Hauwa? me ki ka d'auke ni ne?" idan har ya san abinda ya faru to ki tabbatar babu yawuna smma ai kin san a gaban yara aka yi kuma irin wannan lamarin da wahala ya 'buya."
Ta yi shiru tana gyad'a kanta ba ta ce komai ba.
Na kad'a kaina kawai na haura saman da mamakin yadda ta yi sanyi ta zama wata Saliha bana tsammanin ma jiya ta rintsa saboda yadda na hangi tashin hankali a idonta.