← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 271 OF 276

Sashe 271

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun bayan dawowarta babu wata matsala da ta sake faruwa yanzu kusan wata shida kenan cikina na da wata bakwai lafiyar Allah nake gudanar da hurd'odina babu nauyi irin nasu Hassan sannan laulayin da na yi ma takaitaccene a farkon samun cikin ne.

Babu wanda ya san ina sa juna biyu tsakanin anti Yagana da Sahura tunda ban gaya musu ba muna dai yin waya sa'i da lokaci.

Sai da Hadiza ta haihu tukkuna da su anti Yagana suka zo yan gidanmu suka fahimta lokacin ma ni kadai nake jin abinda nake ji nakuda ce nake yin ta a tsaitsaye Hadiza ta haifi namiji yaro lafiyayye mai kama da babansa sai ta dinga ba ni sha'awa wallahi ganinta ri'ke da jaririnta lafiya lau tiriri ya kare.

Kayan da Nabila ta had'awa su Hassan a lokacin haihuwarsu sama suna saman maigidan don haka ya ce da Sukairaju ya zo ya kwashe su suyi amfani da shi ya samu takwara domin kuwa kwana biyu da haihuwarsa ubansa ya yi masa hud'uba da Tajuden.

Yan gidanmu kaf sun halarci taron sunan Hadiza da yamma sai ga Hauwa da leda cike da kayan baby wai ai ta ji an ce yaro ya ci sunan maigidanta.

Ta sake ana ta wasa da dariya da ita babu kuma wanda ya nuna mata komai ni kaina janta nake yi da hira yadda ta saki jikinta sosai ya tabbatar mini da cewa ba ta fah
imci halin da nake ciki ba ni ma, ko da yake a zaune nake ba lallai ne ta gane komai ba.

Sai daf da magriba ta yi mana sallama ta tafi anti Yagana ta ce da Fati ta zazzage kayan da ta kawo a duba tsaf kada ta kunso wata jarabar ne.

Na dinga dariya ina fad'in anti Yagana kenan.

Set din kayan jariri ne uku da turaruka masu tsada da wani takalmi mai ban sha'awa bayan mun gama gani Fati ta had'a kayan ta mayar da su cikin leda.

Sati biyu suka ce za su yi kafin su tafi anti Yagana kuma ta ce kwana biyu kacal za ta kara ta kama hanyar gidanta na yi na yi da ita itama ta zauna ta huta sosai kamar yadda su Fati suka zauna ta ce ai ita babba ce da kunya kada lalacewar ta yi yawa mazajenmu su daina ganin girmanta.

Na ci dariyata kuwa na 'koshi mussaman da na tuna yadda suke yin wasan 'buya da maigidan tun musayar yawun da suka yi akan kamfani shi yana jin kunyanta itama tana jin nauyinsa.

Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biyani hakkina ba.

Aikuwa bayan tafiyarta da kwana biyar ciwon nakuda ya kama ni a gida ranar juma'a kaf kowa yana nan har yaran kuma da safe ciwon ya tashi ban fito daga d'aki ba na kira Dr Sailuba saboda dama tuntuni na yi nak'udata a tsaitsaya don haka zuwanta da minti ashirin da biyar na haihu lafiya lau yarinya mace ta dinga tsalla ihu da ya fargar da kowa Yara suka ki'dime suna murna Mama ta haihu Khalil ne ya ruga gidan Mamansa twin's kuma suka hau sama wajan Babansu bacci yake yi suka tashe shi da ihun murna Mama ta haihu.

Dr Sailuba ba ta bud'e d'aki ba kuwa sai da ta kammala komai ta gyara ko'ina amma still kusan awa guda da haihuwar yarinyar kuka take tsalawa har dai abin ya fara ta'ba ni na fara tambayarta anya lafiya ta ce mini lafiya lau don karon farko bata tsammaci matsala ba.

Tana bude d'akin suka dinga shigowa yan gidanmu su Fati da Hauwa da take jan kafa tsabar k'aduwa da tashin hankali kamar wadda ta yi targad'e a kafarta kallon farko da na yi mata na gane lallai akwai matsala domin duk yadda ta kai ga ganin ta gayyato dariya da annashuwa tasirin damuwar da ta tsinci a kanta a ciki ya danne abinda take kokarin gayyotowa duk wanda ya lura da ita zai gane cewa lallai a rikice take domin kayan bacci ne a jikinta da hijabin sallah.

Bakin kowa kamar audiga tun daga kan maigidan zuwa kan masu aiki yaran da 'yan uwanana sai murna da sambara suke yi don ma dai kukan da yarinyar ke tsalawa ya d'an rage karsashi da annashuwar shi ma ya fara tambayar Dr Sailuba babu matsala da confidence d'inta ta ce masa babu wata matsala lafiya ce.

Hauwa ta kar'bi babyn hannunsa tana juyyata can kuma ta dan daga mata idanuwanta tana gwalesu sosai ta dubi ta d'aga rigar jikinta tana tatta'ba jikinta da hannunta sai ta dubi
Dr Sailuba tana fad'in." Ki duba sosai Dr kada ki dinga yin abu daka yarinyar nan bata da lafiya."
A d'an sanyaye ta kar'beta daga hannunta har zuwa lokacin kukan take tsalawa ta dan jima tana jujjuyata
Kafin ta dube ni da sanyi jiki ta furta." Za mu je asibiti domin dubata sosai kukan ya d'an so ya yi yawa sannan jikinta ya d'auki zafi akwai abinda nake zargi."
Gabad'aya ni da shi sai jikinmu ya yi sanyi muka dubi juna.

Ya yi saurin kar'be babyn tana tsala ihu ya d'an dubi Hauwa dake tsaye a gefansa itama shi take kallo karaf ta ce." Ku je asibitin sai a dubata gaskiya bata da lafiya." Na ga sanda ya wurga mata wata muguwar harara ya kawar da kansa cikin wani masifaffan yanayi da tashin hankali.

A takaice dai a ranar a asibiti muka kwana domin dai gado aka ba mu babban likita ya bincike mana ita tsaf sikila ce dole akwai buk'atar zamanmu a asibiti na wani lokaci domin kula da ita.

Tashin hankali wanda ba a sa masa rana.

A daran ni da shi kuka domin dai da farko har na fi shi dauriya na dinga tausarsa da kawo masa misalai tare da gaya masa kada ya butulcewa Allah kada kuma ya nuna Allah bai yi masa daidai ba.

Ya kasa jurewa hawaye yake d'igarwa domin dai bayanin da likitan ya yi mata babyn sikila ce sosai.

Hauwa kuwa ta kira shi a daran sm da kyar na bashi baki ya d'auka don gabad'aya ba shi cikin hayyacinsa ban ji me take gaya masa ba sai gani na yi ya tashi tsaye jikinsa na wani irin kyarma yana ce wa." Ba ki kunya da nauyin gaya mini wannan maganar ba Hauwa." Itama na ji ta cikin 'karaji tana fad'in." In sha Allahu rabbi sai ta mutu da izinin Allah hakkina ba zai barka ba wallahi ba zan daina mi'ka kukana ga Ubangiji ba ai ba cikin haihuwar ne ba ni dashi ba ni ma, yarinya kuma nafad'a maririciya kuma mutuwa suke yi kada ma ku sanya rai a kanta domin mun ga haka ya fi sau d'ari.

Jikinsa ya cigaba kyarma da wata kaurarriyar muryar da ban san shi da ita ba ya furta." Ina ce sai ina auranki tukkuna zan kwanta dake ki samu cikin da za ki haihu shikkenan na sake ki Hauwa saki biyu babu wata dangantaka ta aure a tsakanina dake yanzu na sake ki saki biyu.........

Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
*A kar'ba da ha'kuri don Allah hakan tana iya faruwa da rayuwarsu ina fatan dai ba ku mance tushen labari ba.

Sakon littafin gudun aure ya isa saura k'arashe in sha Allahu Ina mutukar godiya....*
*GARKUWAR MATA.
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*176*
Na ji komai da kunne na babu buk'atar neman karin bayani ni gabad'aya ma abinda yake gabana lafiyar yarinyarta akwai tsananin damuwa da fargaba a ce ka gama goyon ciki da wahalhalunsa ka haife ka fuskanci wani k'alubalan na mussaman sai yanzu gane wannan shine babban dalilin da ya sanya likitoci suke iyakacin bakin kokarinsa wurin ganin sun dakile yawaitar haihuwar yaran da suke d'auke da wannan lalura.

Doke ce a yanzu waliyya da mahukunta basa d'aura aure sai da shedar daidaituwar jini mussaman ga saurayi da budurwar da ba su ta'ba haihuwa ba akansu dai wannan dokar ta fi tsananta akwai sau'ki akan namijin da yake da iyali da kuma bazawarar da ta haihu a wani wajen tana da yara maslaha ce a tsakaninsu ko da su
yi aure sai su d'auki matakin gujewa samun ciki.

Duk da yake duk tsumi da dabara ba a isa a yi wa Allah wayo ba wahalar dai da tiri-tirin shine abin gudu.

Na haihu ina murna ban ta'ba tunanin zan sake haihuwar sikila ba ganin na jera haihuwa har sau biyu lafiyarsu lau gabad'aya ni da shi tunda aka samu cikin yarinyar nan ba mu ta'ba zama mun tattauna mas'alar da za ta iya kasancewa a rayuwarmu ba saboda duka tunaninmu daya wata'kila Allah ya d'auke mana tunda mun yi sau biyu a jere dukkaninsu lafiya lau.

Sanin gaibu sai Allah kuma duk abinda ya tsara shine daidai kuma dole a yi godiya gare shi.

Lamarin Hauwa kuwa gabad'aya kaina ya kulle na gaza kuma na yi rauni akanta domin duk kaifin tunanina k'wakwalwata ta kasa hakaito mini a wane mizani zan ajiyeta a bayyane komai yake bata da abokiyar gaba sai ni kuma a duk lokacin da sarki Allah ya bata sa'a a kaina don ta d'auki makami ba wani abu ne.

Asibitin na mussaman ne don haka da gari waye Baba Tabawa kawai na ce masa a kawo mini na kuma kira Fati a waya na ce ta had'a mini kaya da duk abinda zan buk'ata tunda ba su tafi ba suna nan likitan dake tsaye kan yarinyar ya bada tabbacin kan cewa a k'alla mu yi sati ko kwana goma kuma alhamdulillahi kwana daya kacal da muka yi yarinyar ta sassauta kukan da take yi zafin da jikinta yake d'auka ma ya yi sau'ki ta kuma samu bacci.

Hakan ya sanya shi tafiya gida domin yin wanka tunda tare muka kwana cikin tararrabi da zullumin abubuwa masu yawa ya dinga ba ni tausayi daga zarar na daga kaina na dube shi hakika Allah ba yadda baya aiwatar da ikonsa a kan bayinsa.
Chapter 271 · 0% Book details