Sashe 244
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Kafin na shigo na ga alamar muna da ba'ki tun daga haraba hakene?"
" 'Yan gidanmu ne!" Na fad'a a takaice.
Ya saki fuska yana fad'in." Sun zo taya mu murna kenan, na ji dad'i sosai kuma idan na ci abinci zan sakko 'kasa mu gaisa sai a yi musu magana."
"To." Kawai na ce na tashi tsaye.
Ya rike hannuna na koma na zauna kusa da shi.
B'akin lallen da ya zanu a saman fatar hannayena ya shiga dubawa.
Ya bud'e tafikan hannayen yana kallo yatsun ya yi marron sosai zanan fulawar ya fito.
Ya dinga sauke ajiyar zuciya yana fad'in." Ya yi kyau sosai mu ga na 'kafafun." Gim na yi kawai ta yaya zan iya nuna masa k'afafuna na cikin safa.
Ya sunkuya kuwa ya cire safar yana ta dubawa na zubawa 'keyarsa ido takaici da haushinsa ya ishe ni.
Maganar Nabila idan har ta yi nisa akwai wani gagarimin lamari da zai faru tunda shi bashi da tunanin yin nesa da mu'amula mai tsayi da ita bayan gaisuwa.
Ai tsakanin mace da namiji idan sha'kuwa da tausayi suka shigo ciki akwai alamun kauna.
Ya nuna son cigabanta da tausaya mata tunda idan an yi magana sai ya ce business d'inta ne a saya a wurinta kada a je waje a saya.
Ya d'ago da wani irin yanayi na yi saurin d'auke kaina ya tsira mini ido har yanzu hannunasa yana cikin nawa ya ce." Za ki ba n
i abinci ko na tafi na kwanta a haka?"
Na furta." Duk yadda ka ga ni, amma ai ba ni ce mai baka abincin ba."
Ya ce." Kwana biyu itama tana ta ciwo kullum a kwance take ciki ne da ita ba kuma sosai take sarrafuwa ba ke kuma kin ga kina da masu aiki." Na katse shi da gaggawa ina fad'in.'' Na hana ka d'aukar mata aiki ne? tana da lafiya bata da lafiya ba abinda ya shafe ni ba ne.
Cikin dai masu aikin gidan nan Wallahi babu wadda za a d'auka.''
Ya ce." Ba a ce dama za a d'auki ko daya ba, za a kawo mata nata masu aiki itama."
Na d'auke kaina ban ce komai ba.
Ya ce."
A kawo mini abincin dai ko ba shi da yawa kada abin ya yi mini yawa kuma." Na tashi kawai na tsinci hannunsa saman tudun mazaunaina.
Na juyo da sauri ina kallonsa.
Ya cire hannun shima yana kallona.
Wato da bai samu sararin d'ora hannunsa a kirjina ba kamar yadda ya saba sai Allah Ya bashi sa'a ya d'ora a na baya.
Ya furta." Menene fuskata za ki buge na tare."
Na janye idona daga kansa kawai na wuce cike da mamaki wai tambayata yake yi menene saboda na kalleshi wato shi bai d'auki abinda ya yi a matsayin wani abu ba."
Ina saukowa na tarar da ita ta zo ana ta hira da ita.
Usaini ma yana hannunta.
Hasan din na goye bayan Taburni yana bacci.
Ta miko mini shi tana fad'in." Tun d'azu yake neman nono."
Ban ce komai ba na kar'be shi na zauna gefan Hajja wadda suka ta hirar duniya da Ya Falmata tana ta basu labarin rikici da masifar tashin hankalin da aka shiga a maiduguri lokacin farkon boko haram.
Khalil na sanya ya d'auko mini wayata a d'aki na kira Fati na ce su zo gabad'aya za su gaisa da maigidan.
Ta ce mini abinci suke ci da sun kammala za su zo.....
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*162*
Ganinta a zaune ya sanya na share kawai ban kai masa abincin ba idan ya koma gidanta sai ta bashi abinda taci su kwanta duk rashin moruwarta da yake fad'i ai ba zata kwana da yunwa ba.
Na ji tana magana da Hajja kan zuwa inna Uwani gobe wai sun yi waya Hajjan ta bata amsa da cewar itama ta sanar da ita.
Ya sauko cikin mutunci da kulawa ya zauna a falon bayan shigowarsu Fati gabad'aya ya gaisa da su har yana jan su Hassanar gidanmu da tsokana haka dai suka dinga sinne kai irin na rashin sabo yadda ya zauna ya kula su shine abinda ya d'an sassauta mini zuciyata domin kuwa ko babu komai bai 'kyamace su ba ya nuna suma cikakkun mutane ne masu kima da karamci zuwansu ya sanya shi farinciki har yana mik'a godiyarsa wannan yana daya daga cikin kyawawan halayensa karrama mutum duk rauni da rashinsa baya ta'ba nunawa na 'kasa da shi cewa shi ba komai ba ne, fuskarsa a sake zai mu'amulanci mutanan da ya tabbatar da cewa ya fi suttura da rufin asiri.
Mun d'an jima tare da shi a falon da su ma gabad'aya kafin ya yi wa Hajja sallama ya fita.
Jim kad'an itama ta tashi ta bi bayansa bayan ta yi mana sallama kamar dai gaske ta saki jikinta tana walwala tamkar babu komai a zuciyata Hauwa kenan .
Yusi kuwa kam ganina da shi biyu tunda suka zo yana can tare da Adamu sai da gari ya waye tukkuna suka shigo su biyu da akwatina hud'u jiyan ba su samu damar kawo kayan ba.
Muna d'aki gabad'aya anti Yagana Ya Falmata da Sahura.
Yusra tana bacci saman kujera bata tashi ba.
Na bi su da ido har suka gama shigo da akwatinan kayan suka ajiyesu a gefe ban ce komai ba.
Muka gaisa da su suka zauna cikin nishadi da jin dad'in had'uwa da juna wannan so da k'aunar da suke yi wa junansu har mamaki yake ba ni.
Hassan na hannun Adam Usaini shi kuma yana hannun Yusi na ji shi Adam din yana fad'in." Mama Baba ne ya ce mu kawo miki kayan nan akwai wasu kayan ma da za mu d'auko da yamma anti Nabila ta ba ni lambar wayar direban idan suka iso zai kira ni."
A takaice na ce." To shikkenan."
Ya mi'kawa anti Yagana yaron da yake hannunsa ya riga Yusi fita shi yana zaune kamar akwai magana a bakinsa na dube shi ina fad'in." Kai ma ka zama munafiki ko?"
Ya dube ni da sauri yana fad'in." Munafiki Mama?" Na gyad'a kaina ban ce komai saboda takaici to bayan wad'annan kayan akwai wasu kenan.
Ya Falmata ta b'ata rai tana fad'in." Menene abin munafurci Amina."
Na ce." Haushi yake ba ni wallahi idan yana yin wani abin Ya Falmata yaron nan baya goya mini baya ya manta da ni ma gabad'aya."
Ta kama dariya tana fad'in." To yanzu me ya faru da kike barar goyan baya daga gare shi a da can fa shine shalele ko don yanzu kin samu wasu shine za ki cillar dashi."
Na ce." Shi ya fara cillar da ni ai Ya Falmata."
Murmushi ya yi kawai bai ce komai ba ya mika mata yaron yana fadin." Bari na je na same shi Mama zan dawo sai mu yi magana ko idan na yi lefi a yi hakuri.''
Hararsa na yi yasa dariya da sauri ya fice.
Sahura ta fito daga toilet wanka ta yi ta ta zauna tana shafa mai.
Na dube ta a hankali wata irin ki'ba ta yi zamanta a gefena da d'aurin kirji na sake gazgatawa na ce." Wai ke maganin ki'ba ki ka sha ne?"
Anti Yagana ta ce." Kin riga ni magana Amina na ce ko idona ne yake yi mini gizo ne."
Dariya kawai take yi tana fad'in." Kwanciyar hankali ne kawai.
Ya Falmata na fad'in idan haihuwa ma ta tsaya ana samun canji irin haka."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokacin na dubi anti Yagana ina fad'in." Wai ya kuka yi da maigidan nan ne?"
Ta yi shiru tana d'an kallona kafin ta ce." Na same shi ne domin na yi masa godiya bisa abinda ya yi miki na alheri da farko na yi tunanin ke kad'ai ya ware ya bawa tare da yaran nan sai daga baya kuma da yayi mini bayani na gane dalilinsa wallahi abin ne ya ba ni tsoro Amina shiyasa na gaza ha'kuri na ce bari na yi magana akai saboda ina jin tsoron k'aramar magana ta zama babba a zo ana ta maganganu marasa kyau a kan ki."
Ya Falmata ta b'ata rai tana fad'in." Akan wane dalili za ki tare shi da wannan maganar Yagana kin yi kuskure anan gaskiya tunda ta zo ta gaya mana na ce ta kar'ba tunda ba ita ta ro'ka ba shi ya bata.
Amina mahad'in arzikinsa ce don ya dauki 'karamin kamfani ya bata bai nakasa kansa ba kuma yana da ninikin abinda ya bata din amma shine ki ka zame jiki ki ka tare shi ba ki ji nauyi ba don Allah Yagana."
Ta gyad'a kanta tana ce wa." Ni fa ba da wani abin na yi masa magana ba Ya Falmata kin san irin haka yana haddasa rigima tsakanin iyali ki ga gida ya rikice ana ta fad'a kuma da yawa wasu mazan sune suke asassawa wajan fifita wani bangare.
kuma ba ita kad'ai ce matarsa ba Hauwa yar uwarsa ce kuma matarsa itama tana da yara tana kuma da hakki."
Ta ce." Lokacin da zai yi mata kyauta kin sani ne Yagana? ke dai ba yar uwarki ki ka sani ba me yasa ba za ki goya mata baya ba bisa abin alherin da ta samu kin ga kenan anan gaba zaki sanya masa shakku idan ya yi niyyar yi mata wani alherin."
Ta yi shiru bata ce komai ba.
Na gane dalilinta na magana kuma tana da hujja amma yanzu tunda ya fito ya fad'i da bakinsa ni ya bawa ba yara ba shikkenan.
Na ce." Ya ji haushi har yana ta fad'a wai babu wanda zai nuna masa yadda zai yi da abinsa.
Ya gaya mini dalilai masu muhimmancin da ya sanya shi ba ni kyautar wannan kamfani.