← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 276

Sashe 21

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Falalu ma ya kama hanyar fita yana cewa." Hajiya idan da buk'atar wani abu sai a kira ni."
Ban iya ce masa komai ba saboda tunanin da ya yi mini yawa
Ido na zuba masa ya na kwance sambal a gado bacci yake yi numfashinsa na fita a hankali a hankali lokaci guda kwarmin idonsa ya rufta.

Ya ba ni tausayi sosai dalilin da ya sanya ma kenan na kasa matsawa nan da can.

Ina zaune a gefensa tunani ya yi mini yawa.

Wato mu a wautarmu idan Ubangiji Ya baka kudi baka da wata matsalar rayuwa bayan kuma ba haka abin yake ba an ce ma wasu masu kudin koyaushe cikin fargaba suke ga tarin makiya da mahassada bayan lissafi na rayuwa da yadda za a juya dukiyar ta kara bunkusa.

Shi wannan mutumin kaf d'insa abin a tausaya masa ne, a yanzu da nake gefansa a zaune nake yin nazari a kan rayuwarsa.

Gashi nan sai kudi da kadarori sanayya da d'aukaka shahara a duniya duk Allah ya yi masa.

Amma bashi da magaji ma'ana yaran da ko bayan ya rasu zasu gaje shi.

A k'alla yanzu shekarunsa sun haura arba'in da biyar wanda a iya sanina idan talaka ne a matakin shekarunsa muddin ya yi auran wuri ya aurar da 'ya mace idan da ita ya fara. yanzu ne na gane dalilin da ya sanya ya d'auki son duniya ya dora akan Yusi ko bai fad'a ba akwai wani ciwo da yake d'ankare a zuciyarsa.

Gani dai kusan wata uku a gidansa zazzabi kwana daya ban ta'ba yi ba sai ma kibar da nake shigarwa wannan kadai ya isa ya tabbatarwa da jama'a cewa babu mahalu'kin da yake mutuwa sai kwanansa ya kare.

Ni kaina da farko na tsorata amma yadda iyaye da 'yan uwa suke kara mini kwarin guiwa akan tawakkali da yarda da kaddara shine dalilin da ya sanya na barwa Allah ikonsa tunda ko na zauna da Alhaji Tajo ko ban zauna dashi ba idan kwanana ya kare dole na mutu.

Hakika ya bani tausayi sosai ta wannan gefen domin haihuwa rahama ce kuma baiwa ce, kowane dan Adan zai so ya bar magaji bayan babu shi a duniya
Na daga kaina can na hangi Yusi kan sofa ya bingire bacci yake yi sosai.

Ni kam gabad'aya idona ya soye nazari da lissafin rayuwa ya dabaibaye ni.

Gefen asuba bacci ya shammace ni, na bingire a gefansa ba tare da na san haka ba.

Sai ji na yi Yana dan ta'ba hannuna da kiran sunana.

A firgice na tashi zaune da sauri shi ma ya tashi yana ri'ke ni." Menene salati ake yi idan an tashi daga bacci." yafad'a cikin taushin murya.

Na sauke ajiyar zuciya ina dubansa a hankali na ce." Ya jikin naka?"
"Alhamdulillahi Ya furta cikin nutsuwa.

Na ce." Allah Ya kara afuwa.

Ya dubi gefan da Yusi yake kwance yana cewa." Anan kuka kwana ke da Yusuf?"
Sunkuyar da kaina na yi a nutse na ce." E, jiyan ne jikin naka ya rikice sosai baka ma san wanda yake kanka ba."
Ya furta." Shine ki ka ji tausayi na ki ka kwana kusa da ni?"
Shiru na yi ban iya bashi amsa ba.

Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode my wife Allah Ya yi mini albarka." Daga hakan sai ya sauka daga gadon ya nufi bandaki.

Na janye idona daga hanyar da ya bi, jikina duk a salube na tashi Yusi domin ya yi shirin massalaci.

Ya ce zai je tare da Baba.

Ban matsa masa ba, na kyale shi a d'akin ni na kama hanya na fita da tunaninka masu yawa a tare da ni.

Ni a jikina nake jin canzawar yanayi game da mutumin nan.

Wani yanayi ne wanda na kasa tantance shin tausayinsa nake yi ko kuma sonsa nake yi ni dai ban sani ba amma ina jinsa a raina, ina kuma jin mugun tausayinsa yadda yake mu'amulantata cikin sau'kin kai hakan yana k'ara karya lago na.

Uwa uba k'aunar yarona da yake yi tamkar shine ya haife shi.

Ko yanzu da nake wanka Allah-Allah nake na gama na shirya na koma d'akina domin sanin halin da yake ciki, ni kaina mamakin lamarin nake tsakanin jiya da yau mutumin ya tsaya mini a zuciya.

Cikin doguwar riga mai adon duwatsu na shirya a jikina hankalina na sake komawa d'akin nasa.

Sai na tarar dashi a zaune har ya yi wanka yana cikin kananun kaya singiliti da boxar wasu wuraran na jikinsa duk a bayyane.

Falalu yana fifita masa shayi shi kuma hankalinsa na kan wayarsa shigowata ta d'auki hankalinsu gabad'aya.

Ni Kam jikina ya yi sanyi ganinsa a haka, sai na dinga jin nauyin had'a Ido dashi, duk da ba yanzu na saba ganin namiji da irin shigar jikinsa ba, amma dai shi din kwarjini yake yi mini.

Na ji shi yana cewa da Falalun ya je kawai tunda na shigo.

Ya zo ya gifta ni yana gaishe ni na amsa cikin nutsuwa.

Ya bude d'akin ya fice, cikin sanyin jiki na k
rasa kusa dashi na dan zauna kan kujerar dake fuskantarsa ina gaishe shi da tambayar jikinsa, ya amsa hankalinsa gabad'aya a kaina.

Kallona yake yi sosai wanda ya sanya jikina kara mutuwa.

Saukar numfashinsa na ji a hankali ya furta." Yusuf ya tafi makaranta ko?"
Na dube shi ni ma cikin kulawa na ce." Ai kai zan tambaya Yallabai." Sai ya yi murmushi yana cewa." Ai sai da na rarrashe shi tukkun ya tafi ya shirya wai saboda Baba bashi da lafiya ba zai je ba zai zauna ya kula da ni."
Murmushi na yi tare da cewa." Yusi kenan, na jima ban ga mutumin da ya saki jiki dashi kamarka ba."
Murmushi ya yi bai ce komai ba, tsayin minti goma d'akin ya yi shiru sai saukar numfashinmu a hankali na ji maganarsa yana cewa." Ina son Yusuf sosai Ina ji kamar ni na haife shi, Amina ni ma za ki yi mini alfarmar haihuwa ko?"
Yadda ya yi maganar kowaye kai dole ya baka tausayi.

Na ce." Ai Allah ne yake bayarwa ranka ya dad'e, kuma indai muna tare Yusuf naka ne, ai ban isa na raba wannan k'aunar ba."
"Na aminta da hakan my wife ni yaushe za ki ba ni nawa?" Ya furta cikin kyakykyawan lafazi. shiru na yi ban iya bashi amsa ba.

Ya nisa kafin ya sake cewa." Kin san ciwon nan nawa har da fargabar yadda zan tunkareki da buk'atata domin na lura da gaske bakya 'kaunata.

To kin ga wannan lamarin yana buk'atar soyayya.

Da gaske haihuwa nake so wallahi."
A hankali na dube shi tare da cewa." Ka daina cewa ba na k'aunarka don Allah."
Ya ce." To, na daina cewa, amma idan da gaske kina kaunata ki watsar da makamanki kamar yadda na watsar da nawa makaman mu yi rayuwar aure domin zama cikakkun ma'aurata.

Sannan ki taso ki zo nan kusa da ni."
Cikin 'yar shagwaba wadda ma ban san ina yi ba na ce.'' Ba ka ce sai an auna ni ba, ni ba zan iya kusantar inda kake ba yanzu saboda kada na shafa maka ciwo."
Ya yi mini wani irin k
llo wanda na kasa gane na menene cikin taushin harshe ya furta.

Ni da kike cewa mai kanjamau fa!

Ni fa babu wata mace dana sani Amina.

Amma kefa maza biyu ni ne ai abin tausayi, kuma dole na ji wa kaina haushi.

Ban iya ce masa komai ba.

Ya ce." To, tunda kin ki zuwa ni bari na zo." Ya ajiye wayar hannunsa ya nufo wurin da nake zaune.

Hannun kujarar ya zauna.

K'amshin turaransa ya buge ni.

Ni dai Ina masifar son kamshinsa ba tun yau ba.

A rikice ya riko kafadata yana ko'karin rungume ni ya ce." Ina son wannan 'kamshin na jikinki Amina.

Za ki mallaka mini kanki ko?"
A tsorace nake don ban yi tsammanin cewa daga ya zo zai rungume ni ba, bayan haka ma sai hari yake kaiwa k'irjina wanda na fahimci tunda na zauna a d'akin hankalinsa yana kai.

Na cire hannunsa da yake ta mammatsa mini jiki a sarke na furta." Baka da lafiya fa Baba sannan ga tea dinka can zai yi sanyi."
Idonsa a lumshe ya kwanto gabad'aya a jikina ya sakar mini nauyinsa yana nishi wanda ya yi masifar daga mini hankali lokaci guda na ji yanayina ya fara canzawa.

Wani masifaffan shau'ki na shiga wanda tunda uwata ta haifo ni ban ta'ba jin irin yanayin ba.

Ban san yadda aka yi ba kawai na tsinci kaina da tallafar kansa na matse tsam! a kirjina.

Yayin da yake yin nishin ni ma shi din nake yi.

Lamarin da ya kara dagula mana lissafi gabad'aya domin yadda na yi masa ya k'ara kidimashi ainun!

Ya sake rikicewa Yana ko'karin saka bakinsa cikin nawa.

Ni da shi din gabad'aya muka kasa sarrafuwa domin kamar wad'anda aka haifa tare muka zama ita kanta kujerar da muke kai sai da ta jiki karshe ma rigib mukayi a kasan kafet wanda hakan ya zamo silar rabuwar gangar jikinkinmu tare da dawowa hayyacinmu a lokaci daya.

Bayan rabuwar gangar jikinmu sai ya tsira mini idanuwansa wanda babu alamun risina ko kunya a cikinsu.

Ni kuma sai hakan ya kara jefe ni cikin jin kunya da nauyi har nake zargin kaina da bashi kwarin guiwa har ya aikata abinda ransa yake so.

A ganina da tun farko na nuna ban yarda ba, ba zai samu sararin yin abinda ya yi ba.

D'ankwalin abayata da ya sum'bule ya fadi a kasan wurin na d'auka na d'ora a kaina tare da dan gyara shi yadda zai rufe tudun kirjina, na tashi guiwa a sabule na kama hanyar fita kamar na rushe da kuka haka nake ji a cikin raina....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
Chapter 21 · 0% Book details