← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 276

Sashe 104

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya jima yana kallona kafin ya gyada kansa a nutse ya furta." To Allah Ya yi miki albarka, ya kuma kare faruwar hakan anan gaba, sannan kuma ki yi amfani da duk shawarwarin dana d'ora ki akai, kina kallon yadda iyalina suka karanci halina tsaf to sai mu jima wata matsala bata gifta mana ba suna bina a yadda nake so, ni kuma ba na zalintarsu daidai gwargwado ina sauke hakkin kowacce.

Ina so ki yi koyi dasu a dan zaman da ki ka yi tare dasu, ki d'auki darasi na zamantakewa tunda kina da abokanan zama to sai ku zama 'yan uwan juna, ku taimaka juna, ku ha'de kan yaranku waje daya, kada ku yarda wata 'baraka ta raba zumuncin yaranku a gaba za ku yi alfahari da haka.

Sannan kuma kada ki kara samun ciki ki zubar wannan maganar na nanata miki ki ri'keta da kyau domin ba ke ki ke rayawa ba, haka zalika ba ke kike kashewa ba, tunda har kin yarda za ki cigaba da zama dashi a hakan to Ina yi muku fatan alheri Ubangiji Allah Ya sa har karshen rayuwarku wata matsala ba zata sake faruwa ba."
Hawaye na ji sun ciko idona saboda tsananin mutuwar jiki.

Wato ana zaton wuta a ma'kera ashe Baban Saude mutumin kirki ne na gaske ban sani ba, lallai anti Yagana da mutanan da suke masa wani irin kallo sun d'auki alhakinsa domin kuwa mutum ne nagartacce mai mayar da d'an wani nasa, irin wad'annan mutanan masu tsage gaskiya da gudun abin duniya sun yi 'karanci a wannan duniyar.

Ina komawa d'aki anti Yagana ta kira ni a waya na daga tare da jin d'an faduwar gaba domin kuwa ban san dame take tafe ba.

Sama sama ta amshi gaisuwa kafin ta fara gaya mini dalilin da ya sanya ta kira ni a waya.

Na ce mata ai yanzu ma Baban Saude yake sanar da ni komai.

Sai ta ja tsaki da alama har yanzu ciki take da ni don dai na yi mata nisa ne babu yadda za a yi ta zo inda nake ta huce fushinta saboda sanin halin maigidan , shiyasa haushina da take ji ya sake ninkuwa.

Shiru na yi Ina sauraran duk maganganun da take yi uffan ban ce mata ba domin Ina iya yin magana ta ce na yi mata rashin kunya domin mu rabu lafiya duk abinda ta ce mini sai na ce to, ta kashe wayarta bayan ta gama gaggaya mini maganganun da ranta yake so da sunan jan kunne da gargadi akan zuwan da zai yi har tana cewa tasan ba ni da mutunci za a iya had'a baki da ni a wulakantashi da tozarci saboda yin hakan a wurin Baban Saude abu ne mai sau'ki dalilin da ya sanya ta kira ni kenan ta gaya mini sun yi waya dashi tun jiya kuma ya tabbatar mata da cewa da zummar sulhu zai zo.

Ajiyewar wayar na yi raina fes cikin zuciyata na ce da ke dashi dukkaninku ba kwa son gaskiya, ko yanzu ai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, na d'auka ai girman kai ba zai bar shi ya tako kafarsa ya zo ba, ai na ji dad'i mutuka da gaske da yadda Baban Saude yake da kafiya da dagiya akan ra'ayinsa.

Duk da kwarjini da haibar da yake da ita ina da tabbacin hakan ba zai firgita Baban Saude ba dalili shi ma mutum ne mai ra'ayin rik'au kuma mai tattare da wadatar zucci.

Washe gari da safe bayan mun karya kummalo na koma na kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeni ko kadan ba na tare da wata fargaba ko zullumin abinda zai faru idan ya zo garin shiyasa kwata-kwata ma ban sanya abin a raina ba don ni har so nake ma ya zo din naga yadda za ta kaya wannan shi zai nuna mini cewa yana sona da gaske ko kuwa duka karya ce da yaudara.

Sai wajan daya na rana na tashi rana gatse-gatse ina fitowa tsakar gidan da zummar wanke bakina da burushi na sami matan gidan suna ta aiki na yau na daban ne domin Sayyada na hanga a can cikin kicin ta dasa kujera tana ta suyar kaji.

Mama tana gyara alayyahu ita kuma anti amarya tana tace zo'bon da yake kan wuta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*69*
Ina gama wanke bakin na shiga cikinsu muna aikin tare cikin zuciyata Ina tunanin ko saboda zuwan mutumin nan ya sanya Baban Saude yin wannan hidimar.

Shiru dai na yi ban tambayi komai ba har muka kammala aikin gabad'aya towon farar shinkafa tas da miyar taushe wadda ta ji gyada da alayyahu gefe guda ga soyayyan man shanu nan da ya ji albasa.

Ga soyayyun kaji nan masu yawa wanda Sayyada ta yi aikinsu.

Bayan mun gama komai tsaf na share gidan na wanke shi tas lokacin Baban Saude ya fito daga dakinsa da zummar wankan Juma'a.

'yan samarin gidan ma daya bayan daya duk suka shigo suka yi wanka suka yi shirin massalaci.

Ana saukowa Baban Saude ya shigo da dadduma a kafad'arsa ya tsaya daga bakin kofar d'akin Mama lokacin muna ta aikin daura zobo a leda ya ce maza a fito da abincin nan akai wa almajiran massalaci kamar dai yadda aka saba.

Salmanu shi ma yaronsa ne shi ya shigo ya rataye daddumar a kan taga kafin ya kinkimi kular towon ya fita da sauri Abahuraira shi ma ya shigo ya d'auki kular da aka zuba miyar a ciki ya fita da ita.

Da yake girkin anti Amarya ne itace ta had'a masa abincinsa a babban tire ya ce ta kai d'akin dai ta ajiye zai sake fita domin yana da ba'ko.

Umarninsa ta bi ta yi yadda ya ce mata.

Muna cin abinci ina nazarin yanayin yadda Baban Saude ya tsara gidansa da rayuwarsa komai a tsanake babu harido babu hauka kawunan iyalinsa a had'e babu ba'kar gaba balle kishi mai tsanani.

Sayyada ce take gaya mini ai duk ranar juma'a akan yi abinci mai kyau a kai massalaci akalla ya fi shekara goma yana wannan aikin ladan amma a cewarta na yau na daban ne domin kajin da ya sayo sun ninka wanda yake saya duk Juma'a.

Jin haka ya sanya na gazgata zargina saboda zuwan Alhaji Tajo ne domin karramashi.

Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baban Saude yana da kyawun zuciya kuma ba shi da niyyar kashe mini aure ko tozarta mutumin nan
Sai dai idan har ni na bu'kaci hakan.

Bayan la'asar hud'u da arba'in da shida Baban Saude da kansa ya fita domin zuwa airport ya taro shi.

Kafin ya tafi sai da ya leko ya sanar da ni tukkuna sannan ya tafi.

To sai a lokacin ne jikina ya d'anyi sanyi na dan dinga jin fargaba amma ba sosai ba.

Wanka na yi na shirya cikin doguwar riga amma ban yi wata kwalliya ba turare kawai na fesa a jikina na zauna gefen katifa da wayata a hannuna ina dubata.

Tun ranar da ya d'ora hotunan d'aurin auransa ban kara ganin status d'insa ba, dama kuma ban ta'ba gani din ba, hakan sai ya k'ara tabbatar mini da cewa don na gani ne yasa tunda a lokacin ina ta neman hanyar da zamu shirya.

Koda na tuna irin wulakanci da rashin arzikin da ya dinga yi mini a lokacin sai raina ya 'baci na ja tsaki tare da gyara kwanciyata a katifar ina tunanin akan wannan tsohuwar matar ya ki'dime matar da ko wadataccen nono ba ta dashi k'aramin jiki ne da ita bata da wani tudu ta baya a tsuke take har gwara Hauwa da 'yar cikar 'kuruciya a tattare da ita.

Ai na godewa Allah da ya sanya duk su biyun babu wadda za ta nuna mini kyawun jiki ta ko'ina har yanzu da komad'ata.

Ina daga cikin d'akin a kwance na ji shigowarsu ina jin muryar Baban Saude sama sama amma ban ji abinda yake cewa ba.

K'amshin turaransa har d'akin da nake kwance k'amshin da hancina ya jima bai shak'a ba.

Zaune na tashi ina laluban mayafin rigar da take sanye a jikina gefe guda kuma gabana na d'an bugawa kad'an kad'an yanayin jikina ya fara sauyawa da wani lamari na daban..

Sai da na yi namijin ko'karin wajan ganin na rinjayi zuciyata don gudun kada ta kunyatani a gabansa.

Ba ni da halin cire son da nake masa a zuciyata domin da damar a hannunata take ni kuma nake sarrafa zuciyata to ina ganin da ba wannan maganar ake yi ba.

Ni kaina nasan Ubangijina ya jarrabe ni da kaunarsa inda Allah Ya taimakeni rauni na bai ta'ba barin na nuna masa mahaukaciyar soyayyar a fili ba, Ina ganin da ya fahimci haka wulakancin da zai yi mini sai ya fi wannan.

Kusan minti talatin da zuwansa Ina zaune a d'aki ni kadai ina ta tunanin mai yake faruwa a d'akin Baban Saude kuma ban ji ya kira ni ba, can na ji maganar Dada da sauri na tashi na fita na tsaya a bakin kofa tana d'akin Mama suna gaisawa ina tsaye a bakin kofa hannuna ri'ke da labule hankalina na bakin kofar d'akin Baban Saude takalma na gani uku a bakin kofar d'akin a zube ina tsammanin har da Babansu Fadila za a yi zaman domin na ji muryarsa a dakin.

Dada ta fito daga d'akin Mama tana magana wadda ban fahimci me take cewa ba ta dube ni muka had'a ido sai ta ja tsaki kafin ta furta." Dube ta da ido a tsaye kamar an kama 'bera a massalaci, ashe abin naki duk karya ce."
Na bita da kallo ina gyara yanayina da tunanin maganarta to mai ta hanga a tare da ni da har take fad'in wannan maganar.
Chapter 104 · 0% Book details