Sashe 239
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta k'aramar k'ofa muka fita gabad'aya can muka hangi mota za ta shiga gidan Momi Hajiya Maryam kenan duk da ban gane wanda yake ciki ba amma ganin motar ta tsaya ya sanya ni ma na tsaya.
Adam ya fito daga cikin motar ya karaso har wajan da nake tsaye yana dariya yake ce wa." Mama ina yini, ina za ku je haka da daddare, da yaran duka?"
Ni ma cikin murmushi da kulawa na ce." Za mu duba babanku ne baya jin dad'i."
Yanayinsa gabad'aya ya canza ya furta." Ai ba mu sani ba wallahi me yake damunsa?" Ya fad'i maganar a rikice da damuwa a fuskarsa.
Cikin nutsuwa na ce." Mura ce da zazza'bi ka kwantar da hankalinka Adam ba a kwance yake ba."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Mama mura ai ciwo ne mai tsanani tunda har Annabi Muhammadu s.a.w ya yi magana akanta bari na yi magana da anti Nabila tana cikin mota na je daukota daga airport ne sai na zo mu je tare na duba shi."
Na gyad'a kaina ban ce komai ba shi kuma ya juya a gaggauce ya nufi inda motarsa take.
Mamaki nake yi ashe har yanzu Nabila na gidan tare da su.
Ko da yake hakan ma ya yi daidai tunda har suka aminta da zamanta wata'kila ta fi sauran 'yan uwan maman nasu gaskiya da kuma k'aunarsu tsakani da Allah duk dai ba a tona zuciyarta an gani ba A
amma dai tsayin wata kusan takwas da rasuwar Maryam take zaune tare da su ban ta'ba jin wani k'orafi ba nasam idan da akwai matsala to tabbas Nusaiba za ta gaya mini."
Ga mamakina sai na ga sun fito daga motar tare da ita.
Duk da dare ne amma akwai haske manyan fitilu mabambamta a estate din ta hasken nake hangenta tun daga nesa a yayin da suka jero da tare da Adam din ta ci wata uwar kwalliya cikin wani lece wanda aka yi masa d'inki riga da siket matsatstsu ta k'ara ki'ba ta cika ta ko'ina d'inkin da yake jikinta ya gama bayyana hallitun jikinta tunda ba ta yi amfani da babban mayafi ba da takalmi mai tudu a kafarta wanda yake hade da wata madaidaiciyar jaka mai adon duwatsu masu kyalli.
Kana dai ganinta ka ga manyan zawarawan da suka ci suka kuma tayar da kai zawarawa irin na Abuja masu kafacity amma yanayin dressing dinta ya gama bayyana cewa ba ta da mafad'i domin kuwa da da akwai shi ina ganin hakan ba zata faru ba.
Irinsu na nan da yawa da suke 'batawa zawarawan da suke gefe a killace domin kare kansu.
Na janye idona a daidai lokacin da suka 'karaso wajan da muke tsaye da yaran.
Cikin sakin fuska da kulawa ta furta." Hajiya Amina mun yini lafiya ya yaran duka yanzu Adam ke gaya mini Yallabai babu lafiya wallahi ni ma dawowata kenan gida sati na biyu a dubai."
Na ce." Lafiyarmu lau alhamdulillahi ya su Hanif wallahi kuwa amma da sauki ai ba akwance yake ba mura ce da zazza'bi ke damunsa.
Da yanayi na alhini irin na al'ada ta furta." Mu je ni ma sai na duba shi, Ubangiji Allah Ya kara sau'ki."
Na ce." Amin Ya Allah." Kusan tare muka jera tafiyar ni da ita.
Adam ya bi yaran suka yi gaba tunda sune suka san gidan ina jinsa shima yana tsokanar Usai akan dai tsotsar hannu tana ta zum'bura ba'ki idan ya riko hannunta ta fizge ta koma gefe.
Nabila sai dariya take yi tana fad'in.
Usai iya rigima kenan ashe ba ta daina tsotsar hannun nan ba."
Murmushi na yi wanda babu nisha'di a cikinsa na ce." Tukkuna dai zata daina idan girma ya zo da sauki ma a hakan ai ta rage.
Gidan bai kai wanda nake ciki girma da tsaruwa ba.
Amma dai daidai gwargwado an narka masa dukiya shima tun daga wajensa zuwa cikinsa komai na iko ne falon ya tsaru da sabbin kayan more rayuwa kamar dai yadda na gani a hoton da ya d'ora.
Suna zaune shi da ita a falon tana gefansa a zaune ta yi gayu sosai cikin shadda da surfani an yi d'auri mai hawa-hawa sannan an sha yari da sarka da abin hannu.
Da yake shadda ce sai ta kara mata kumburi da kwarjini ramar ta 'buya.
Yana cikin jallabiya da Loptop dinsa a gabansa gefe guda kuma fulas din shayi ne a ajiye da karamin cup a kusa da shi.
Muka shiga tare gabad'ayanmu.
Ta yi wani bala'in shan kunu ta amsa sallamar sai kuma ta yi kasa da kanta.
Shi kam rufe computer ya yi ba shiri saboda yaran gabad'aya kaf wurinsa suka nufa.
"Baba sannu, Baba ina yini baba ya jikin naka?"
Abinda suke ta fad'i kenan Minal har tana ta'ba wuyansa tana cewa." Zazza'bin ma ya sauka ko?" Tana kallon fuskarsa
Yana dariya ya ce."DIN bai sauka ba tunda kun zo zai gudu garinsu.
Hassana ta ta'ba wuyansa a karo na biyu kamar yadda Minal din ta yi ta ce." Babu zafi jikin naka Baba Allah Ya ba ka sau'ki."
Ya amsa da Amin yana ri'ke hannunta, ita kuma Usaina fad'i take yi Baba maganarka wani iri kasha tomtom kaji baba!"
Na ce." Wai ba za ku samu nutsuwa ba ne haka ake duba mara lafiya?"
Suka nutsu tare da samun waje suka zauna.
Khalil ya nufe shi da Sultan a hannunsa yana fad'in." Baba barka da dare ya jikinka?" Ya amsa yana cewa." Na ji sau'ki Babana." Ya mika hannunsa ya kar'bi Sultan da yake ta wangale masa
baki yana dariya da gwalantun kiran sunansa.
Khalil din ne ya fara gaisheta a hakimce ta amsa tana wani fizge kanta.
Daga nan kuma yaran suka shiga gaisheta ganin yadda yayansu ya yi ta amsa tana ta'be baki.
Maganar Nabila ta katse nazarin da nake na ji tana ce wa." Allah Ya taimake ka an yini."
Ya dube ta babu yabo babu fallasa ya amsa da lafiya a takaice ya ce." Yau ki ka dawo ne?"
Ta furta." Eh wallahi dawowata kenan Adam ya d'auko ni a airport."
Ya yi shiru bai ce komai ba Adam ya shigo dama a waje muka bar shi lokacin da za mu shiga an kira shi a waya.
A nutse ya k
rasa gabansa ya durkusa har kasa yana gaishe shi ya dafa kansa yana amsawa da kulawa ya ce." Mama na gani da yaran gabad'aya ashe ba ka ji dad'i ba Ubangiji Allah Ya kara afuwa."
Ya furta." Na ji sau'ki ai tunda na sha magungu
a sai dai rashin karfin jiki kuma na gode sosai Allah Ya yi muku albarka."
Ya amsa da "Amin.
Ita ta fara tashi tana d'an duban Hauwa ta ce." Madam ina yini ba mu gaisa ba."
Shiru ta yi ba ta amsa ba.
Sai ma ta d'auki wayarta tana dubawa.
Adam ya dinga fad'in." Ina yini tana jinsa sarai sai daga can kuma ta amsa ba tare da ta dago kanta ba.
Nabilan ta yi gaba da zummar fita kafin Adam d'in ya bi bayanta.
Falon ya rage mu kad'ai Hauwa dai ko nahiyar da nake bata kalla ba balle na samu arzikin gaisuwa abin ya ba ni dariya sosai wai ita matar gida tunda ni na zo a ganinta ni zan gaisheta.
A marairaice na ce." Ya jikin naka?"
Ya tsira mini ido cikin wani yanayi kafin." Ya furta." Ba zan ce miki komai ba giwa, wato idan zan rasu baki damu da ni ba ko?"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali cikin 'yar shgawaba na ce." Ka duba wayarka ka ga iya adadin kiran da na yi maka gabad'aya ni da yara yini muka yi da damuwa ba ka shigo ba kuma ba ka ce za ka yi tafiya wani waje ba.
Ya lalubi wayarsa yana cewa." Wajen da ba k'asa nan ake gardamar kokawa bari na duba."
Ya shiga duba wayar yana fad'in." Ban ga kiran ki ba kin kare kan ki ne kawai."
Ya miko mini wayar yana cewa." Duba ki ga ni."
Girgiza kaina na yi a nutse na ce." A a ba sai na duba ba, amma fa babu buk'atar rantsuwa na kira ka ya kai sau bakwai da ta shiga sai a katse kiran babu matsalar network my love katse mini kiran aka dinga yi."
Ya furta." Ya ban ga alama ba."
Kai tsaye na ce." Wata'kila kai ne ka goge?"
Ya dube ta tana zaune tana jin mu da wayarta a hannu kanzil ba ta ce ba.
Ya girgiza kansa tare da ajiye wayarsa a gefansa.
Shiru bai yi wata magana ba sai hayaniyar yaran Sultan tuni ya sauka daga cinyarsa ya shiga cikin 'yan uwansa.
Ya dube ni muka had'a ido sai kuma ya dube ta tana zaune gim ya d'aure dai ya furta." Gaba kuke yi ne da junanku?"
Kallonsa ta yi kafin ta ce.'' Ba dabi'ata ba ce amma tsakani da Allah Amina ba gidana ta zo ba, me ya sa take yi mini wani irin kallo, ni da naje gidanta haka na yi mata a gabanka fa na gaisheta ta yaya kake ganin za mu zauna lafiya da juna bayan duk abinda ta yi daidai ne a wajenka baka nuna mata kuskuranta."
Ya d'aga mata hannu yana cewa." Ya isa ban ce ki gaya mini magana ba, duba da kyau akwai yara ba ni son rashin hankali."
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.
Ya yi 'kwafa kafin ya cigaba da ce wa." Kin had'e fuskarki tamau! kina amsa gaisuwa da k'yar a matsayinki na wadda aka zo gidanki hakan shine daidai ko kina tunanin ban ga irin wulakancin da ki ka yi wa yaron nan Adamu ba."
Ta dai yi shiru ba ta tanka ba.