← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 276

Sashe 161

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin jajantawa kanta da alhini take gaya mini wai Idiris an yi musu rabon gado wata tsohuwar gonar mahaifinsu aka gano a wani k'auye shekarun kusan talatin da biyu da ya sayi wurin ya jefar abinka da mutanan da tunda ya sayi wurin babu wanda ya ta'ba d'auka a cikin manyan yaransa ya nunawa ko 'yan uwansa ba su sani ba tun a wancan lokacin ya kai takardun wani tsohon banki da ya daina aiki a yanzu da yake dukiyar ta halak ce bincike dai har mahukunta suka tabbatar da gonar mahaifinsu ce tunda da sunansa a rubuce a takardun da aka binkito takardun gonar a bankin Yanzu dai tana gaya mini an sayar da gonar miliyar sittin da biyar Idiris ya samu miliyan takwas shine wai ta ga alamar wai yana neman aure.

Na ci dariyata na k'oshi cikin zuciyata ina fad'in." Idan ban da tarangahuma ta da namiji fisabilillahi nawa miliyar takawas take da har za a rakito aure a kanta.

Matsalar Malam bahaushe kenan daga zarar ya dan samu fargaba ko yaya ne sai ya ce aure zai kara.

A tunanina wannan dama ce da idiris ya samu da zai juya kudin domin dogaro da kansa.

Ba a ce masa kada ya yi aure ba amma ya bari ya tsaya sosai da k'afafunsa tunda zahirin gaskiya Sahura tana kokari sosai kusan ita dashi rabi da rabi suke yi kan harkar karatun yaran ma ta fi shi kokari sosai da sosai ni kaina duk wata na kan tura mata abinda ya sawwaka tunda nasan tana da d'awainiya sosai.

Wannan dalilin ne fa ya sanya wasu matan cire tausayi da imani akan mazajensu domin wallahi duk namijin da ka nunawa soyayya daga karshe yana samun dama zai yi kokarin jefa ka a rana.

Ganin ban bata amsa ba sai kawai ta kira na dubi agogo goma da ashirin da biyar na dare.

Lallai abin yana damunta tunda ta gaza ha'kurin bari gari ya waye
Na daga ina fad'in." Sahura." Ta ce." Shine don wulakanci na turo miki sa'ko kin bade kin saurara kimanin minti goma ina ganinki a online din amma ki gagara ba ni amsa." Muryarta na d'an rawa ta kai k'arshen maganar.

Ta d'an ba ni tausayi na danne dariya da nake so na yi na ce." Wallahi na saurara Sahura kaina ne kawai ya daure shiyasa ki ka ji na yi shiru mamaki ne ya ishe ni, in banda abin Idirs nawa miliyan takwas take da zai rakito aure maimakon ya juya kudin su ninku ba mu hana shi ba amma ai sai ya bari mu murmure tukkuna."
Ta furta." Wallahi da ni yake zancen Amina muddin ya ce zai yi aure a irin wannan yanayin sai dai ya sake ni domin ba zan iya zama da butulu ba."
Na ce." Ki saurare ni Sahura, ki bi komai a hankali dan Allah, kin san yanzu idonsa a rufe yake yana ganinsa da 'yan canji zai iya aikata komai.

Kada fushi ya sanya ki zo kina nadama daga baya, ki yi hakuri ki bi a sannu ba ni son wata matsala ta faru dake."
Sai kawai ta fashe da kuka tana fad'in." Wallahi Amina ban ta'ba tsammanin Idiris zai mini haka ba, ki duba ki ga fa irin wahalar da nasha da yawon haya da ba don kin ba ni wannan gidan ba da tuni fa muna can zaune a wannan tsukakken gidan da masu shi suke yi mana wulakancin duk lokacin da suka zo kar'bar kudinsu.

Kin dai sani ke kanki kin sha cika mana kudi idan lokacin biya ya yi.

Yanzu yana ganin bashi da matsalar biyar kudin haya.

An aurar da Yusura kuma ina d'aukar albashi tare da samun kayan abinci sa'i da lokaci a wurin aiki shine ya sakar mini wahalar gida ta sauran yaran da ya samu kudinsa bai yi tunanin komai ba sai na aure yanzu don Allah Amina idiris ya yi mini adalci."
Na ce." Bai yi ba wallahi, kuma ya yi butulci, ai shine na ce miki ba mu hana shi ya kara aure ba amma ya bari ya tsaya da k'afafunsa sosai yanzu ba lokacin da zai rakito wata ba ne.

Amma kin san yawanci tunaninsu daban ne da namu kuma idan idon su ya rufe akan mace suna aikata komai a yanzu Sahura ba fata nake yi ba don Idiris ya rabu dake ba wani abin ba ne wallahi tunda baya hankalinsa."
Cikin dusashewar murya ta ce." Na gaya miki wallahi duk ranar da ya daura aure da wata to ni kuma na gama zama da shi har abada kuwa."
Bata bari na yi magana ba ta datse waya.

Na yi sororo da tawa a hannu Ina mamakin al'amarin.

Gaskiya Idiris bai kyauta mana ba wallahi.

Ina binki bashi domin littafin nan na kudi ne.

"Wallahi jiri ne ya d'ebe ta ta fad'i, Allah ma yasa ina d'akin da ban san abinda zai faru ba." Nabila ce take yin wannan maganar yayin da take zaune kusa da 'yar uwarta dake kwance a sambal a gado sai kace matacciya.

Ya ce." Dama ai kamata ya yi ki kasance tare da ita a koyaushe saboda jikin nata babu kwari har yanzu, sai kin kula sosai." Ya kai karshen maganar yana duban dirowar da take gefan gadon da Momin take kwance wata madaidaiciyar jarka ce cike da rubutu da kofin gilas a ajiye.

Ya dubi Nabilan yana fad'in." Ta ci abinci?" Ta ce." Yanzu dai zan kawo mata?" Ta mike da sauri tare da kama hanyar fita.

Ya zauna kusa da ita a hankali ya kira sunanta "Maryam." Ta bude idonta tana ko'karin tashi zaune ya sanya hannu ya dago kafadunta ta tashi." Me yake damunki yanzu?"
"Ba ni jin komai sai jirin fa, daga zarar na mike zan ji hajijiya baya ga haka kuwa sai dai nace alhamdulillahi."
Ya gyad'a kansa cikin kulawa ya furta." Za ki daina ji in sha Allahu daga zarar kin ci abinci kin sha magani yanzu, amma menene a wannan a gefanki."
Ta dubi wurin da yake kallo a hankali ta ce." Sanyawa na yi aka rubuce mini al'kur'ani mai girma.

Ya d'an jima yana dubanta kafin ya ce." Hakan yana da kyau, kina ji ko dole fa sai kin rage yawan tunani da damuwa, ba ke kad'ai ce ke d'auke da wannan cutar ba kuna da yawa ko a asibitin ma ai kin ga wad'anda suka fi ki jin jiki, cuta ba mutuwa ba ce za ki samu sau'ki in sha Allahu, ki dinga sanya hakan a ranki."
Sai ta sanya kuka tana fad'in.

Anya kuwa, ga ni nake yi mutuwa zan yi wallahi, ba fa na jin dad'in duniyar gabad'aya, ciwon nan shi zai kai ni."
Ya ce." A a, mutane nawa ne suka yi jinyya mai tsanani kuma suka tashi ki daina sanya damuwar hakan a ranki za ki ji sau'ki in sha Allahu."
Ta dinga share hawaye tana girgiza kanta har Nabila ta shigo da plate din abinci madaidaici ya kar'ba ita kuma ta juya ta fita.

Kusa da ita ya matsa sosai da kansa ya bata abincin da maganganunta ta sha.

Ya sanyata a jikinsa sosai yana rarrashinta cikin tausasawa kamar yadda ake yi wa mai ciwo.

Kusan sha d'aya da arba'in sha biyu saura kenan ta yi bacci ya fito Nabila na falon tana kallo ya ce ta shiga su kwana tare.

Sallama ya yi mata a gurguje ya fita.

Cikin baccin da ya kwashe ni na ji motsin shigowarsa d'akina.

Na bude ido ina kallonsa yana zama gefana kamshin turare biyu ya gauraye hancina k'amshinsa daban ne kuma ya zauna a jikinsa tuntuni duka kayansa k'amshin suke yi yanzu hancina na shako mini wani kamshin na daban.

Na tashi zaune ina d'an dubansa na dubi agogo sha biyu saura minti goma sha biyar ya samu kimanin awa uku babu wani abu a can.

Na ce." Ashe za ka dawo?" Ya gyad'a kansa yana fad'in." E, me zai sanya ni na kwana bayan ga amaryata tana jira ko ba ki yi kewa ta ba?"
Ya fad'a yana d'an matsowa kusa da ni.

Sai na ji kawai haushinsa ya kama ni, na tsani munafurci wallahi ko bai fad'a mini ba ya rungume matar nan a jikinsa tunda ga k'amshin turaranta nan a jikinsa.

Na ce." Aikuwa da ka sani ka kwanta a can kawai dubi agogo fa ga gani."
Ya rike hannuna yana murzawa ya ce." Kada mu yi wata hatsaniya dake a wannan daran Amina, ki ba ni hadin kai da k'warin gwiwa don Allah kada kishi ya sanya ki zobe lada da albarkar da nake ta shi miki tunda na dawo kike faranta mini rai, ina ta murna Allah ya amshi addu'ata a kanki, ki ru'banya ladanki kafin gari ya waye."
Baki na zum'bura na ce." Me ka ji na fada yanzu, cewa na yi fa da ka sani ka yi kwanciyarka a can shine ya zama lefi bata fa da lafiya."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Ba ni da wani dalili da zan kwana a can, ai ta ji sau'ki kuma kwana na nawa a tare da ita, ai kina da hakki a kaina ni ma ina dashi a kanki kamata ya yi mu raya wannan daran ya zama ma mussaman a gare mu har ya fi na ranar amarcinmu daraja."
Shiru na yi ban ce komai ba ya d'an shafa dokin wuyana yana fad'in." D'azu dana shigo na gan ki rungume da yaron nan a kafadarki sai dana na ro'ki Allah subahanahu-wata'ala da ya ba ni namijin ko'karin samar da makamacinsa a daran yau, za ki ba ni hadin kai ko?"
Ya fad'a hucin numfashinsa na sauka a jikina.

Na kalle shi na ga ya wani saki gabad'aya kansa a langa'be ido daya a kanne.

Cikin zuciyata na ce." Yaudara da iya kalamai sai ka ce goggagen d'an bariki.

Ya had'e hannunmu waje daya yana sakin ajiyar zuciya tare da d'an sake shigowa jikina.

Ya kamo daya hannun na yana duba lallan yasa bakinsa ya sumbuta yana fad'in." Ko wannan da ki ka yi mini na ji dad'i har na ce Allah Ya shi albarka abinda za a ru'banya miki lada ne.
Chapter 161 · 0% Book details