← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 216 OF 276

Sashe 216

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na zuba masa ido har ya zo ya zauna a gefan kafafuna yana fad'in." Kin mayar da ni sakarai mara mutunci ko Amina Ina yi miki magana kin yi banza wulakancin nan ya isa haka wai me ki ka taka ne?"
Shiru na yi ban tanka masa ba ya cigaba da cewa." Hauwa duk ta d'auki matakan gyara kuskuranta kamar yadda ni ma na d'auki matakin gyara akan zamantakewar da muke gudanarwa a gidan nan zan yi kokarin kwatanta adalci."
Na ce." To wannan kuma damuwarka ce idan ba ka yi adalci ba duka za ka ci a lahira."
Bai mayar mini da martani ba saboda ya saba jin irin wad'annan maganganun na fitowa daga bakina sai ya d'ora akan maganarsa yana cewa." A wannan lamarin da yake faruwa kece matsala domin kin d'auki wata hanya ta daban wadda na kasa gane inda ki ka dosa na gaya miki ba ni da ra'ayin raba gidana nafiso yarana su tashi tare domin su shaku."
Na tashi zaune ina kallonsa na ce." To sai ka rabu da matsala mana dole ne kana da da yadda za ka yi a kaina tunda na zame muku matsala ka yakice ta ka huta, ba zan zauna da Hauwa a gida daya ba wannan shine abinda zuciyata ta yanke mini.

Ya furta." Ni kuma ba zan raba gidana ba Amina ni dake shege ka fasa."
Na koma na kwanta tare da cewa." Duk yadda kake jin kanka baka fi karfin hukuma ba idan ba za ka raba gida ba to sai ka ba ni da takardata."
Ya furta." Wannan zoben da na sanya miki a yatsa shi yake nuna cewa ni dake mutuwa ce za ta raba auran zobe muke yi."
Na ciro zoben na ajiye masa shi saman cinya ina fad'in.'' Ai ban san manufarka ba kenan ga abinka nan."
Ya d'auka da mugun haushi da takaici a tare da shi ya dinga jujjuya zoben yana kallona har ya so ya d'an ba ni tausayi na d'auke kaina daga kansa.

Ya ce." Na gode." Ya mayar da shi hannunsa kafin ya sake kallona a karon da bashi da adadi ya ce." Gobe ki ka ce za ki je maiduguri ko?"
"Umm!" Na furta can kasan zuciyata.

Ya tashi tsaye yana cewa" Sukairaju zai kai ki a mota za kuma ki ga sa'ko cikin acct d'inki sai da safe."
Ya kama hanyar fita na ce." Da yara zan tafi domin ina so su ga dangina."
Ya juyo da saurin gaske yana cewa." Wannan ne kuma ba ki isa ba babu inda za ki je mini da yara.

Ke dai ki je Allah Ya ba da sa'a."
Na tashi zaune ina cewa.'' Mai kake nufi yaran nan na ta'ba nuna maka wani iko a kansu tunda na haife su baka da hujja domin ba naka ba ne kai kadai dangina zan kai su domin kowa ya gan su."
Ya ce." Ba za su je ba na fad'a ke dai tunda kin zama isashshiya ga hanya nan ki tafi, yaran ma da ba wani damuwa ki ka yi da su ba yanzu za ki ce za ki je da su wani waje su zauna a gidan ubansu kawai."
Raina a b'ace na ce." Maidugurin ne wani waje kada ka manta fa asalina ne."
Ya ce." Wani waje ne mana ko akwai wani nawa a garin duk danginki ne ke ce ta maiduguri 'yan biyu kuma na kano ne garin Dambatta."
Ya fita da sauri tare da jan kofar da k'arfi.

Bacci rabi da rabi na yi da sassafe duk na gama shirye-shiryena kaya set goma na sanya a akwati na ce Khalil ya kira mini Masa'udu ya shigo ya tsaya bakin kofa muka gaisa na ce ya d'auki akwati ya kai mota.

Na koma na sanyo hijabi dina har kasa lokacin yaran sun gama shirin makaranta amma ga dukkanin alamun Khalil ya gaya musu tafiya zan yi tunda shi ya fita da akwatina.

Suka fito Minal ta rushe da kukan gaske sauran sun yi cirko cirko Usai da yatsa a baki tana tsotsa na cire hannun ina fad'in ke ba za ki daina tsotsar hannu ba sai tasa kuka tabbacin a kusa take dama.

Taburni da Baba Tabawa suka fito Mairo ta fito suka tsaitsaya yaran suna ta kuka har da Khalil ina kallonsa ya tsuguna bayan kujera.

Na ji giwata ta yi sanyi ainun dama kamar kiris suke jira domin koda na tsiri zaman d'aki haka suke shigo mini d'aya bayan d'aya idan sun taso daga makaranta.

Shi da Hauwa suka sauko yayin da nake gayawa Baba Tabawa Fadila ce ta haihu zan je ba wani abu ba ne.

Hauwa fuskarta a sake ganin abinda yake faruwa ko tana zargin yaji na yi oho a gabanta dai jiya na yi masa maganar tafiya maidugurin amma ban san abinda ya assasa mata sakin fuska ba duk dambarwar da uban yake yi da Minal akan ta sake ni ta'ki sai ihu take yi Hauwan ta zo tana jan hannunta da yake yarinyar a zababbiya ce idan tana kuka sai ta gartsa mata cizo a hannu.

Aikuwa ba shiri ta sake ta matsa gefe.

Babu halin na ciccibeta na rarrasheta kamar lukutan baya idan tana kuka d'aukarta nake yi yanzu kuma jikina ya yi nauyi cikin da nake d'auke dashi wata shida ni kaina nauyi yake mini bana iya sunkuyon kirki.

Na ja hannuna duka yaran suka biyo ni dakina.

Na zaune gefan gado su uku duk sun tsaya a gabana 'yan biyu da ita Minal din ta uku Khalil ne bai biyo ni ba.

Tausayinsu ne ya kama ni ta kar'fi da yaji Hassana da Husaina sun koyi ha'kuri don yadda suke shakkata ba sa shakkar ubansu wasu lukutan idan suna kiriniya da ido na yi musu gargadi suke shiga hayyacinsu shiyasa ba sa yin iya shegankatar da Minal din take yi dalilin uban yana lelenta ba kuma fin sauran ta yi a zuciyarsa ba kawai yana fad'in sunana ne da ita wai yana yi mini kara..

Kawai na ji hawaye ya silalo mini duk wannan k'aunar da shakurar da take tsakanina da yarinyar nan dole na bar wa Hauwa 'yarta domin yaran da na haifa kawai zan hada kan kayana mu tattara a waje daya bana tsammanin barinsu a gidan idan Hauwa tana ciki za mu tafi tare da yarana da mai aikina baba Tabawa kenan su Taburni da Mairo idan suna da ra'ayin cigaba da zama da Hauwa su zauna.

Ya shigo dakin sai na yi gaggawar goge kumatuna.

Minal na ta fad'in." Mama zan bi ki unguwa, Mama zan biki unguwa."
Ya tsaya a gefe yana fad'in." In banda neman fitina Amina ai sai ki bari su tafi makaranta tukkuna ki fito ki tafi tunda kin san lallai ne za a iya samun wannan matsalar.

Na yi shiru dai ban ce masa komai ba.

Ya zo ya ja hannun yarinyar da ta d'ora saman cinyata Yana fad'in." Yi shiru za ku je unguwa ko?"
Ta daga kanta.

Ya dubi 'yan biyu da suke tsaye a kusa da ni sai ya girgiza kansa cike da jin haushi ya kamo hannayensu yana cewa." Zan kai ku da kaina ku je karatu ku dawo da daddare da kaina zan fita da ku yawo kuna so ko?"
Suka daga kai babu wani karkashi a tattare da su.

Jim kad'an da fitarsu ya dawo d'akin ina zaune ban motsa ba tsabar yadda jikina ya mutu.

Kawai ya mayar da kofa ya rufe ya tsaya yana kallona sai da na gaji tukkuna na dube shi na dan wani lokaci.

Ya yi kwafa yana cewa." Wato da tafiya za ki yi ban isa ki yi mini sallama ba ko?"
Shiru na yi uffan ban ce ba.

Ya cigaba da cewa.'' Yaushe za ki dawo kwana nawa ki ka yanke?"
Na ce." Sati biyu."
Ya girgiza kansa yana cewa." A a ban amince ba a yi sati daya dai Hajiya sati biyun da ki ka d'iba a cikinsa nake tsammanin daurin aurena da yarinyar nan Hajara."
Na ce." To ni ina ruwana ni ka aurowa ita da sai lallai ina nan ko iyayenta ni suka bawa."
Ya ce." Kada ki gaya mini maganar banza da wofi Amina kina d'aga mini murya fa ya ina yi miki magana cikin lumana domin mu fahimci juna kina so ki zage ni wallahil-azimin na gaji da wannan rashin mutuncin da ki ke yi mini a gidana."
Can kasa na ce." Sai ka d'auki mataki ai."
Ya yi shiru yana kallona nasan ya ji abinda na ce kawai ya rasa yadda zai yi da ni ne."
Ya ce ki duba jiya da daddare na sa miki miliyan bakwai ki yi guziri ga 'yan'uwa na can garin naku.

Biyar kuma sayi kayan kwalliya na danne kirji kamar yadda al'ada ta nuna Hauwa ma na bata."
Na dubi tsabar idonsa ina fad'in." Ba ka isa ka saye ni da kudi ba wallahi bari ka ji da can ba ni kudin dannar kirjin kake yi mata biyu ka auro kafin wannan cikinsu kwabonka baka ta'ba ba ni ba don haka ban ga dalilin da zai sanya wannan karon munafurci zai sanya ka ba ni kudinka ba."
Jikinsa ya yi sanyi ya furta." To shikkenan na ji zan ciko miki 10m sai ya zama sha biyar ba biya ki shikkenan ko?"
Na ce." Ba ka ji mai na ce ba kenan ba ka isa ka saye ni da kudi ba wanda ka tura mini ma yanzu zan dawo maka da abinka Allah Ya rufa mini asiri."
Sai ya yi shiru hankalinsa a tashe na ji yana fad'in." Allahuma ajirni fi musibati Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ya bud'e kofar d'akin ya fita cikin gaggawa.

Ni ma na tashi da sauri na fito na hange shi yana hawa sama falon babu kowa na fice daga gidan.

Sukairaju na tsaye jikin mota da alama fitowata yake jira tunda tun dare maigidan ya sanar masa da tafiyar ya shirya tsaf.
Chapter 216 · 0% Book details