← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 276

Sashe 200

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na gyad'a kaina in banda rashin mutuncin Hauwa matar da ta rungumi d'anki da ki ka dangwarar ki ka tafi take yi masa wahala itace abar zagi da aibatawa.

Lallai da gaskiyar Hajja Hauwa ba ta da kunya yau na sake gasgazatawa tunda ita duk girma da shekarun mutum furfurasa ba ta hana ta yi masa diban albarka.

Da kyar na iya had'a fruit-salad din ina yi ina basu baki Hauwa ba su kadai ta ci mutunci ba har da ni da maigidan gabad'aya ta tsinka.

Na had'a masa abinci tsaf tunda lokacin su ma sun kammala na kai samansa na jere inda yake zama.

Na yi wanka da sallar magriba na shirya na zauna kaina ya kulle gabad'aya na rasa ta yadda za a yi na fara yi masa bayanin abin nan da yake faruwa wanda na tabbatar da cewar wani sabon tashin hankalin ne zai sake faruwa a tsakaninsu tunda haushinta yake ji dama.

Ya kira ni a waya na tashi na je na same shi ya sake sosai ya daina gabar yana ba ni labarin Bashir kanin marigayiya cewa an yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na shekara goma sha biyar tare da horo mai tsanani babu kuma biyan tare tunda dama tsohon mai lefi ne nemansa ake yi ruwa a jallo dilan wiwi da 'kwaya ne ga 'yan sace-sace yana ta'bawa.

Jin sa kawai nake yi hankalina baya kansa amma dai na yi kokarin aro jarumta ban bari ya fahimci cewa akwai rikici ba.

Da asuba yana fita salla na sauka kasa.

Kai tsaye d'akin yaran na leka tare suke da Mairo dama har ta yi musu wanka tana shiryasu da kayan makaranta.

Khalil da yake ya girma shi da kansa yake shiryawa.

Muka gaisa da su na wuce wajansu Baba Tabawa na same su suna dambarwa Taburni ta had'a kan kayanta ta 'kulle a d'ankwali tamau wai tafiya za ta yi rarrashinta ya hana Baba Tabawa shiga kicin kamar dai koyaushe.

Ganin da gaske take ya sanya hankalina ya tashi ba ni son rabuwa da matar gabad'aya ita kuma yadda ta yi fushi koda an bar ta tafi garin nasu ba lallai ta dawo ba.

Gabad'aya muka fito fallo na yi na yi da ita ta yi hakuri ta'ki Mairo da yaran gabad'aya duka suka fito aka yi cirko-cirko.

Minal ganin Taburnin tana kuka sai itama ta fashe da kuka da kar'fi don da alama hayaniyar da ake yi da kukan da suke yi su biyu ya tsorata kukan ta ya yi daidai da lokacin da ya shigo ya fara fadin." Lafiya a d'an ki'dime yana kallona domin neman karin bayani."
A tak'aice na ce." Taburni ce za ta tafi." Ya sunkuya ya d'auki Minal din yana rarrashinta da yanayi na damuwa ya furta.'' Taburni ke da na ce miki muna buk'atar zama tare dake yara sun yi sabo daku yanzu ki duba ki ga yadda Minal ke kuka ganin kina yi, ki yi hakuri ki zauna tare da mu duk abinda ya kamata na kulawa za a yi miki daidai gwargwado."
Ta sa gefan mayafinta tana fad'in." Dole ce ta sanya ni tafiya Alhji amma ni ma ina son zama daku."
Ya ce." To shikkenan ki gaya mini me aka yi nasan lallai ruwa baya tsami banza."
Shiru falon ya d'auka babu wanda ya yi magana.

Sai da ya sake maimaita maganarsa tukkuna a sanyaye ta furta." Amaryaka da ta dawo ita ce bata buk'atar zamana a gidan."
A dan daburce ya ce." wace amaryar tawa kuma Taburni?"
Ta yi shiru tana jan hanci.

Can kuma da ya gane Hauwa take nufi sai ya ja tsaki bai ce komai ba ya nufi dakinta da d'an karfi ya buga kofar d'akin ta yi magana ya ce." Bud'e malama."
Minti biyu ta bud'e ta fito da yanayi na bacci a idonta wato duk wannan dambarwar da take faruwa a gidan ita baccinta ma take yi.

Na tausaya mata k'warai da aniya yadda ya fara yi mata tijara da kausasan kalamai wanda ke nu ni da cewa ya fi buk'atar zaman Taburni a gidan a kan zamanta idan ba za ta iya zama ba hanya a bud'e take ta 'kara gaba.

Ta muzanta ainun domin ya yi bala'in tsinkata ya kuma nuna mata cewa masu aikinsa sun fiye masa ita tsit! falon ya d'auka na yi 'kasa da kaina ina jajanta mata ina kuma jin wani iri a raina yanzu me ya fi wannan takaici.

Babu abinda ya fi zaman lafiya dad'i a gidan aure Hauwa da za ta d'auki shawara sam tashin hankali bai kar'be ta ba bata ta cin riba ko kad'an sai fad'uwa a gigice da borin kunya ta nufi dakinta tana kuka mai cin rai......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK 1K ON TALGRAM VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK.*
*07084653262*
*V-VIP AREWAPEN*
*135*
Ya wuce mu ya hau samansa da tsananin 'bacin rai a fuskarsa wannan ya sake nuna mini cewa dama kiris yake jira da ita a gidan don dai haka siddan ba zai yi mata rashin mutunci ba ne sai da dalili amma yanzu da ya samu mafaka ya yi da hujja! ita aka yi wa amma ni nake jin kunya da nauyi wai hausawa suka ce sandar da ta daki uwargida da ita ake dukan amarya.

A ranar kuwa yini ya yi yana 'kuncin rai tabbacin ta gama 'kona masa rai da kuma damuwoyin mas'aloli masu yawa a tare da shi
har ni da nake ta ko'karin sasanta al'amarin haushina yake ji.

Hakan ya sanya ni rabuwa da shi na sauko na yi kwanciyata a d'akina gidan ya kasance shiru tunda ranar makaranta ce yara tun safe idan sun tafi sai yamma likis za su dawo.

Da k'yar dai muka rarrashi Taburni ta janye k'udirinta ta ha'kura da tafiyar har suka shiga kicin da Baba Tabawa a tare.

Sai da daddare tukkuna wajan sha d'aya na yi shirin kwanciya na sake komawa saman.

Na same shi zaune kan dadduma yana ta karatun al'kurani abincin da na jere masa bana tsammanin ya ci.

Sai da ya kammala tukkuna ya juyo yana kallona muka had'a Ido.

Ya d'auke kansa yana fad'in." Zuba mini abinci kad'an amma."
Ban ce komai ba na tashi na isa wurin abincin kamar yadda ya buk'ata shinkafa ce da taliya da miyar kifi masu girma.

Ya zo ya zauna da babbar wayarsa a hannu ya d'auki flat din abincin ya tallafe a hannunsa kamar yadda yake yi wasu lukutan ya fara da Bismillah sai da ya kusa cinyewa ya ajiye flat din ban ce komai na sanya a hannu cikin abincin na fara gyara masa kifin da bai ci ba duk da manya ne marasa k'aya amma dai ba a rasata ko yaya ne.

Ya ci kifin sosai don da alama ya fi bukatarsa a kan nama idan shine ba zai yi masa irin wannan cin ba.

Na tsinci maganarsa yana fad'in.'' Amina Hauwa tana ganin tana da wani matsayi mai girma a gidan nan ko?'
Na yi shiru ban ce komai ba domin ni gabad'aya ma al'amarinsu ya ishe ni.

Ya cigaba da cewa." Yara da suka ratsa tsakani na da ita ne kadai suke ri'ke da ita amma wallahi zan fad'a miki gaskiya ba ni son na bud'e idona na ganta cikin gidan nan nawa sai dole akan wad'an nan dabi'un da ta fara za ta sake fita domin ba ni had'a kowa da masu aikin nan mussaman Mairo da Taburni ina ganin 'kima da mutuncinsu duk wanda zai tsaya tsayin daka akan abinka ai masoyi ne."
Na ce." K'warai kuwa amma ita Baba Tabawa saboda ni na kawo ta bata da muhimmanci da zamanta da babu a gidan duk daya ne a wajenka ko."
Ya dube ni yana fad'in." Ban ce ba Amina ai ban ware ba har da ita na ke nufi."
Ya mutsa fuskata na yi ban ce komai ba.

Ya gama cikin kifin na tattara kayan abincin na sauka da su k'asa na wanko hannuna tsaf na sake komawa saman na same shi zaune a wajen bai tashi ba.

Na dube shi sosai ina fad'in" Yau bacci ne a idona sosai za a shafa maganin yanzu ko sai na kwanta."
Ya lumshe idonsa tare da bud'e su a kaina yana fad'in.'' E, amma mu dan yi wani abu kafin wannan ."
Na gane abinda yake nufi na dan 'bata fuskata kadan ban shirya kwanan tashin hankali da damuwa da kewa ba domin dai tsakani da Allah duk yadda yake ko'karin ganin ya samar mini da nutsuwa ba ta gamsar da ni ha'kuri nake yi kawai sai nake ganin idan bai ta'ba ni ya tsokano ni ba hankalina zai fi kwanciya.

Cikin rarrashi da kwantar da kai har sai da ya ba ni tausayi ya samu ya hillace ni a daran muka yi soyayya sosai ya samu biyan buk'atarta kwarai daga nawa bangaran kuwa abin sai a hankali har sai da na yi kukan b'akinciki a toilet anya rayuwa za ta tafi a haka kuwa gashi maganin da malamin nan ya bayar ya kusa k'arewa saura na kwana biyu kacal babu wani canji.

Sai da na yi kwana uku ban sanya Hauwa a idona ba tana d'aki a kwance na fi tunanin sai ta ji sahu ya d'auke take fitowa ta yi abinda za ta yi a kicin din ta dibi abinda take so ta koma.

Ai dole kunya ma yanzu ta fara har in dai ba za ta daidaita tunaninta ba ta zauna lafiya da kowa.

Kuma har yanzu duk ranar girkinta wajena yake kwana idan na shafa masa magani sai ya yi kwanciyarsa idan ina yi masa nasiha da rarrashi kamar da kurma nake magana sai ya juya mini baya kawai sai na zubawa sarautar Allah ido.

Tunda duk abinda ya kamata na yi na yi wannan shine alkawarin dana daukawarwa mahaifiyarsa.

Yau ne zai je bunkure kamar yadda muka gama maganar jiya magungunansa sun kare malamin ya ce ya je ya same shi gobe Kuma Hajiya Maryam za ta cika kwana arba'in da rasuwa mun yi waya da Nusaiba kan cewa tana so ta zo gidan su yi aikin funkaso da fanke duk na gaya masa bai ce kada ta zo ba.
Chapter 200 · 0% Book details