← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 276

Sashe 106

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan lamarin da yake faruwa ne ya tayar mata da hankali ya sanya take ti'kar kuka kamar yanzu aka yi mata mutuwar.

Kuka na dinga yi a hankali ina jan hanci.

Can kasa na ce." Baban Saude in sha Allahu babu abinda zai sake faruwa wannan al'kawari ne na yi maka zan yi iyakacin bakin kokarina akan abinda ka ce mini." Na yi shiru tare da sake jan majina na dubi wajan da yake zaune wanda kaf hankalinsa yana kanmu ni da Dada, da alama kukan da muke yi din ya fara sosa masa rai na ce." Don Allah ka yi hakuri in sha Allah ba zan sake aikatawa ba, sannan kuma ni ma don Allah ka yi mini adalci ka zauna da ni lafiya ka daina 'kullacina idan na yi maka wani abin yin hakan shi yake k'ara tunzura mini zuciyata, har na aikata abinda baka so."
A nutse ya furta." Kada ki damu magana ta shige in sha Allahu rabbi, za ki shirya tare za mu koma kamar yadda na yi wa Baban Saude bayani ai babu amfanin zaman tunda an sasanta mu ko?"
Baban Saude ya ce." 'Kwarai kuwa, ai ko ba ka furta hakan ba dama ni ma niyyata kenan na ce ka dauketa ku tafi, shine abinda ya dace."
Ya gyada kansa a tsanake ya sake duban Dada da take ta faman yi masa godiya sai ka ce wadda ya yi wa gagarimar kyauta, ita godiyarta yadda ya sakaye sirrin bai tona ba, har ma mahaifiyarsa bai gayawa ba.

Ashe godiyar da take yi zata sake ru'banyuwa domin kuwa kyautar kujarar umara ya yi musu ita da Baban Sauden.

Shi kuma Babansu Fadila ya yi masa alkawarin bashi zungureriya mota domin fad'ad'a harkokinsa na sufari.

Ashe kafin na shigo sun jima suna tattauna al'amura na rayuwa anan ya fahimci yana buk'atar tallafi domin cigaba da gudanar da sana'arsa.

Dama wajan kyautar ban girma ai ba daga nan ba, mugun kirki ne da shi tare da yin irin kyautar bazata wadda Allah yake so.

Shi kansa Baban Saude da yake abin ya zo masa a bazata kasa rufe bakinsa ya yi, ya yi masa godiya sosai tare da addu'oi masu yawa.

Na ji dad'i kwarai da alherin da ya yi musu hakan ya kara goge takaicinsa dake cikin zuciyata kuma ba ni damar yin jayayya dole na bi umarni kamar yadda suka buk'ata bayan isha'i na hada kayana tsaf Salmanu ya fita da akwatinana ni kuma na tsaya yi wa matan gidan sallama da godiya Sayyada tana fad'in in sha Allahu za ta zo mini ta yi mini kwanaki.

Muka rabu cikin kewar juna da kuma mutunta juna.

Ashe tare suke da Sukairaju yana jikin mota a tsaye yayin da shi Yallabai din da Baban Saude suke tsaye a bakin kofar gidan suna magana.

Babansu Fadila ya tafi ina tsammanin. na dan tsaya a hankali na ce." Baban Saude shikkenan za mu tafi na gode sosai Ubangiji Allah Ya kara girma, Allah Ya saka da alheri."
Ya ce." Amin suma Amin Amina, Allah Ya sauke ku lafiya, ki kula ki kuma ki kiyaye da kyau."
A hankali na furta." In sha Allahu rabbi.

Da sauri na yi gaba jin kuka na nema ya k'wace mini.

Kafin na k
rasa bakin motar Sukairaju da saurin gaske ya bude mini na shiga na zauna ina goge hawayen da suka fara zuba a kumatuna.

Kaina a kasa Sukairaju ya bude masa kofar motar ya shigo a tsanake yana tattare babbar rigar da take jikinsa.

Ya zauna sosai kusa da ni yayin da 'kamshin da yake fita daga jikinsa ya game motar gabad'aya Lumshe idona na yi a hankali na bude tare da sauke ajiyar zuciya a hankali da jin fargaba da fad'uwar gaba kad'an kad'an.

Wani iri yanayi na fara ji a tattare da ni, na tashin soyayya tare da kewa dalili kuwa shine dama tun fil'azal k'amshin da ya zauna a jikinsa yana daya daga cikin abinda yake saurin tayar mini da hankali.

Jikina na d'an janye hankali na had'u da jikin motar domin ina ganin kusancin da yake tsakaninmu shi ma yana taka muhimmiyar rawa.

Sukairaju ya d'an juyo a nutse ya ce." Sir za mu wuce hotel din da muka sauka ne?"
Ya gyad'a kansa a yayin da yake d'an gyara zamansa a gefana ya ce ." 'Kwarai kuwa ai tafiyarmu sai gobe tukkuna dole nan d'in za mu kwana."
Sai ya juya da sauri ya cigaba da jan motar cike da bin umarni.

Shiru ya ratsa tsakaninmu babu wanda ya dubi juna.

Kiran da ya shigo wayata shine ya ratsa shiru da ya ratsa.

Ya dube ni a hankali w
nda tun shigowarsa motar bai yi mini irinshi ba amma bai ce mini komai ba.

Na d'auki wayar dake saman cinyata tare da duba mai kiran anti Yagana ce.

Numfashi na sauke babu kuzari na sanya wayar a kunnane ban san kuma mai take tafe da shi ba, yanzu har fargaba nake yi naga kiranta.

" Kina ina yanzu?" Abinda ya fito daga bakinta kenan, ko amsa sallamata ba ta yi ba.

A takaice na ce." Ga ni a mota tare da Yallabai za mu tafi."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." Na so a ce kin zo nan domin akwai taimakon da na sanya a ka yi miki rubutu ne da tofi."
Shiru na yi tare da d'an satar kallonsa sai na ga hankalinsa yana kan wayarsa Allah Ya sa ma ban bud'e handsfree ba amma dai duk da haka ina fargaba saboda yana da kaifin ji, itama anti Yagana tana da matsala wallahi.

Na ji tana fad'in." Kun jima da tafiya ne, amma dai ba yanzu da daddaran nan za ku d'auki hanyar abuja ba ko." A takaice na ce." Sai gobe haka na ji yana cewa yanzu za mu nufi masauki."
Ta ce." To shikkenan zan kira ki da safe za mu yi magana in sha Allahu rabbi.

Wannan littafin na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

"To, kawai na iya ce mata na kashe wayar tare da d'ora ta a saman cinyata.

Anti Yagana rigima kenan yanzu da ta tabbatar da cewa an sasanta zan koma ta daina hantarata.

Shiru ya cigaba da wanzuwa a motar shi Sukairaju yana can yana abinda yake gabansa.

Ni da shi kuma kowa girman kai ya hana ya yi wa d'an uwansa magana.

Lokacin da aka kira wayarshi ban kalleshi ba amma gabad'aya hankalina yana kan saurarar maganar da yake yi a waya.

Matarsa ce Hajiya Maryam ta kira shi.

Na yi shiru mamaki da tsoro yana shigata.

Yadda yake kashe murya da tausasa harshe wajan mayar mata da amsa shine abinda ya fi d'aukar hankalina.

Jikina ya shika k'warai da aniya domin abinda yake yi ko saurayi dan shekara ashirin da biyar albarka.

Idan ni na zama towon tushe ai ya ji nauyi da kunyar Sukairaju domin yaronsa ne a ganina bai kamaci ya saki baki yana fad'in wasu manyan kalmomi na soyayya da turanci ba.

Duk yadda na yi wajan ganin na ji a hakan ba komai ba ne a cikin zuciyata kasawa na yi don sai nake ganin kamar ma da gayya da cin fuska yake yi mini hakan.

Da ta kira shi sai ya gaya mata yana uzuri a ganina bai kamata ya biye mata ba tunda dai ta san muna tare sai dai idan bai gaya mata cewa bikona ya zo ba, tunda duk yawancinsu munafukai ne ba su ta'ba yarda su fito da ainihin abinda yake kasan zuciyarsu.

Ban san lokacin da na ja tsaki mai tsayi ba na dan gyara zamana tare da cire gefan rigarsa da ya had'u da mayafin da yake jikina.

Had'e fuska na yi sosai a karo na biyu na sake yin wurgi da gefan babbar rigarsa da ya sake sauka a cinyata a dalilin gyara zamansa da ya yi.

Sai ya juyo yana kallona still da wayar a kunnansa bai katse ba.

Ban yarda na hada ido dashi ba amma yanayina kad'ai shi ya nuna a kusa nake wata'kila kiris nake jira na fashe.

Kuma haka din ne don abinda nake ji a can kasan zuciyata ni kaina ya shallake tunanina.

Ya kashe wayar tare da ajiyeta a saman cinyarsa kamar dai yadda na ajiye tawa.

Sai ya d'auki gefan babban rigarsa ya d'ora a cinyata yana d'an murmushi amma bai ce komai ba.

Zumbura baki na yi tare da kawar da kaina nasa hannu na cire rigar daga jikina.

Sai ya sake mayarwa yana sake matsowa jikina.

A hankali murya can kasa ya furta." 'kyan'kyamina ki ke yi Amina."
Shiru na yi ban tanka masa ba, kuma ban kalleshi shi ba.

Sai ya d'auki hannuna da yake ajiye a saman cinyata ya had'e yatsunmu waje daya ya rintse can kasa da karamin sautin da ni kadai zan iya ji ya furta." Mu 'kulla alkawari." Hucin numfashin maganarsa ya sauka a gefan fuskata.

Ya sake matse yatsun da k'arfi yana sauke ajiyar a zuciya ya furta." Kin ji Hajiyata."
Cikin wani irin yanayi na dube shi.

Duk da idanuwansa rufe suke da gilashi hakan bai hana ni fahimtar halin da yake ciki ba.

Ban iya ce masa komai ba na janye idona daga kallonsa zuciyata na d'an yi mini zafi kad'an domin sai nake ganin kamar akwai raini a lamarinsa ai ya kamata a ce yanzu ba shi da lokacin kowa sai nawa tunda mun jima ba ma tare a ganina bai kamata ya tsaya wata mace ta kira shi koda matarsa ce din ya biye mata da zantukan soyayya ba.

Ya sake furta." Mun yi al'kawari ko Amina."
Da 'kyar na ce." Ai mun yi tun a gaban Baban Saude."
"Wani nake so mu sake yi ni dake kawai, kin ji rabin rayuwata." Na dube shi da sauri jin abinda ya furta wai rabin rayuwarsa.

Lallai ban yarda ba idan har ni din rabin rayuwarsa ce ai ba zai dinga yin nesa da ni ba duk tsaurin lefin da na yi masa.
Chapter 106 · 0% Book details