← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 276

Sashe 169

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miliyar biyar ya tura mata bai gaya mini ba amma yana tura mata da kamar minti goma ta kira ni a ki'dime har da rawar murya "Amina don girman Allah ki kara yi mini godiya yanzu nan na ga sa'ko 5m na gode na gode na gode Allah Ya saka da alheri ga sabon gida an ce za a ba ni."
Dariya ta kama ni na ce." Sahura yanzu don Allah ina rantse-rantsen da ki ka dinga yi, Idiris fa aure zai ka'ra ko kin manta."
Ta ja tsaki tana fad'in." Wallahi tallahi Amina saboda Yallabai ya saka ba ki a maganar nan zan koma zaman aure da Idiris amma wallahi ba don haka ba sai dai ya aiko mini da takardata."
Ta kashe wayar ba tare da ta jira ta ji abinda zan ce ba."
Ya dube ni yana fad'in." Ba ki kyauta ba Amina." Ina dariya sosai na ce." Don ba ka ji rantsuwar da ta dinga yi ba shine abinda ya ba ni dariya da mamaki."
Ya gyad'a kansa Shima da d'an murmushi a saman fuskarsa ya ce." Ai tace saboda na sanya ba ki zata koma.

Kuma wallahi na ji dad'i sosai tuntuni na fahimci cewa ai tana da kirki da saukin hali."
A tak'aice na ce." Hakane kam Sahura mutum ce har da rabin mutum mun gode sosai ta ce na sake godiya ina yi akan kaina da ita Ubangiji Allah Ya sa kafi haka."
Ya amsa da Amin suma Amin yana kallona.

Na dan sauke ajiyar zuciya kafin na ce." Sai mu yi maganar Hauwa tunda mun sasanta wannan auran."
Ya bata rai yana fad'in." Za ki bata mini rai kenan ko?"
Na ce." B'acin rai kamar yaya?"
Cikin 'kosawa ya ce." Maganar Hauwa ta ishe ni a gidan nan Amina, ya kamata ke ma ki bar ta kamar yadda na bar ta ba na son abinda zai rikita mini gida dama can itace husumiya yanzu da bata nan ba gashi kuna zaune kalau da Maryam ba."
Haka kawai sai na ji rashin jin dadin maganarsa.

A ganina kamar Hauwa bata cancanci haka daga wurinsa ba duk da bai gaya mini abinda ya faru ba a wajan sulhunsu amma na lura haushinta da yake ji ya sake ninkuwa.

Zaman da na yi da ita na fahimci macace mai taurin kai da girman kai har shi eanda ya ajiyeta yi masa take kuma a cikin ayyukan da ta dinga yi a gidan nan da gadara da iko take gudanar da komai dalili tana ganin kamar ta fi kowa dangantaka mai karfi bayan ta aure duka na fahimceta.

To amma ni wannan baya damuna tunda nasan matsayina a zuciyar mijina ko bai fito ya fad'a ba.

Ba na sha'awar a ce sun rabu gabad'aya ga zuria a tsakaninsu mai k'arfi kamata ya yi a ce sun sulhunta junansu sun yi hakuri sun cigaba da zama.

Ganin yadda ya had'e rai da nuna baya buk'atar sake maganar Hauwa sai na shigo da maganar zuwa maiduguri tunda shi ya yi mini alkawari ya ce za mu je a karshen wata amma daga mun dawo za mu tafi legos tunda Alhmdullhi jikin matar tasa ya yi sau'ki.

Abinda ya faru kenan kamar yadda ya yi mini al'kawari cikin karamci da kara da kulawa muka je maiduguri tare.

Ya bi dangin Mamana da alheri mai yawa.

Baban Saude bayan gari a lokacin da muke je garin.

Da yawa wad'anda ba su ta'ba ganinsa a zahiri ba suka yi tozali da shi tare da alherinsa.

Ni kuma na sayawa Fadila sabuwar freezer 'katuwa da kenan d'inki domin yin sana'ar sayar da ruwa da 'kan'kara.

Kwananmu biyu kacal a maiduguri muka yi sallama da su.

A ranar da muka dawo a gidan Momi ya kwana washe gari ya shigo mini a hargitse yana gaya mini jikinta ne ya sake tashi jiya ba su yi wani baccin kirki ba suma ta yi sai gefan asubahi ta dawo.

Ya ba ni tausayi sosai itama haka domin da gaske ne duk mai zuciyar imani idan ya ga halin da take ciki zuciyarsa sai ta motsa.

Dole shiryin tafiyarmu Legos ya rushe yadda hankalinsa ya tashi da ciwon komai nasa tsayawa ya yi
Kwana biyu a tsakani ya sake kwasarta suka sake koma can kasar hindu din asibitin da suka kula da ita a wancan karon domin sake duba lafiyarta.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book complete 2k akan telegram normal What'sapp group 1k via 0542382124...binta Umar gtbank*
07084653262
Tun bayan tafiyarsu sau biyu muka yi magana dashi kamar dai wancan lokacin da suka tafi muna had'uwa ne ta What'sapp mu yi vidiyo call abinda ya kasance kenan amma wannan karon babu nisha'di da annashuwa a tare da shi muka yi magana.

Idan na tambaye shi yanayin jikin nata sai ya ce mini da sauki.

A wancan lokacin yi yayi kamar sabon angon da yake watayawa da amaryarsa ya yi fresh dashi don har na dinga tsokanarsa wannan karon kuwa akwai firgici da damuwa a tare da shi ko bai fad'a ba yanayinsa ya gama nunawa.

Na kasance cikin yanayi na tunani da zullumi domin yau tafiyarsu kwana goma sha daya kenan kuma a cikin kwanakin sau biyu kacal ya ta'bo ni, tun daga ranar ma ban sake ganinsa a WhatsApp din ba.

Idan na kira waya ta yanke ko na ji busy.

Gaskiya na damu sosai hakan ya sanya mini rashin nutsuwa domin sai zuciyata take ta yi mini sa'ke-sa'ken mugun abu bayan mafarkin da nake yi wai gani ina da dariya da ita mara lafiyar muna hira muna ta k'yalkyala dariya.

Masana mafarki kuwa suna fad'in yin dariya a mafarki ba alheri ba ne.

Gaza ha'kuri na yi na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa lafiya ina amsawa da Amin.

Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba.

Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo.

Hoton Momin ya turo mini cikin mawuyancin hali gabad'aya duk ta 'kare ta yi fiyat da ita tana kwance a tsakure a gado hancinta da abin taimakawa numfashi.

Na tsorata ainun da ganinta duk da ba a zahiri ba ne hoto ne sai da na ji wani irin tashin hankali ya rintsa da ni a lokacin zuciyata ta karya na kasa jimirin jure danne hawayen da suke danno mini.

Suka fara sauka a kumatuna.

Wannan ciwon ya gama cinye matar nan manya cutuka sun zagaye rayuwarta.

Vidiyo call ya kira ni ina goge hawaye na danna da ya ga ina kuka ya fara tambayar menene.

Na ce." Ni dai daka sani ba ka turo mini hoton nan nata ba hankalina ya tashi wallahi."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Tana jin jiki sosai Amina ku taya ta da addu'a gabad'aya bata gane wanda yake kanta numfashi kuwa sai da taimako."
Na goge hawayen da yake tsiyaya ina fad'in." Allah Ya saukaka mata.

Kai kuma Allah Ya baka lada."
Ya furta da "Amin." A tak'aice kafin ya cigaba da cewa." Kwana biyu mun d'an yi rashin service a garin.

Sai jiya da daddare ya daidaita ban kuma samu sukunin ta'bo ki ba sai yanzu ina fatan kuna kafiya."
Na ce." Wallahi lafiya lau, ni ma ina nan hankalina a tashe gabad'aya na kasa nutsuwa ina ta tunanin halin da kuke ciki."
Ya d'an yi murmushi kafin ya kanne mini ido ya ce.'' Ni kuma mafarkin ki na dinga yi kullum na kwanta sai kin zo mini har na yi wanka da asuba."
D'an harararsa na yi na ce." Kai kam ka daina haka don Allah."
A sakarce ya ce." To ya za a yi ne Amina da gaske nake wallahi kin san kuwa ba zan yi miki rantsuwa akan son rai ba.
Chapter 169 · 0% Book details