← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 276

Sashe 188

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye d'akin malamin suka nufa da shi gidan ya rud'e sosai da hayaniya duk kowa a tsaye na bi su ina kuka na fitar hankali.

Babar yarinyar nan Hajara ta zo ta ri'ke ni ta baya ina cire hannunta tana sake ri'ke ni fadi take yi "Yi hakuri ki yi masa addu'a kin ji, Allah ya ba shi lafiya."
Na dube ta ina cewa." Ya mutu ko?"
Sai ta girgiza kanta cikin ko'karin kwantar mini da hankali ta ce." Bai mutu ba ke waye ya gaya miki."
Hawaye ya sake tsinke mini na ce." Kansa na ga ya karye ko'ina na jikinsa ya shika.

Kin ga ai lafiya lau ya fito har muka yi muku sallama ko?''
Ta daga kanta cikin alhini ta ce." E, kwarai kuwa amma hakan ba shi yake nuna cewar bashi da rai ba zai tashi in sha Allahu."
Na ri'ke hannunta tamau ina fad'in.'' Ta cutar da ni, ta cutar da yaranmu ta zalince shi, ya yi mata alheri ta saka masa da sharri.

Ta gigita mini rayuwata."
Kawai sai itama ta fara kuka ta rungume ni a jikinta tana cewa." Ki yi hakuri ki samu nutsuwa mu je can wajenmu ki zauna ki nutsu kin ji ko, ki yi wa mijinki addu'a."
Hajja ta fad'o mini a rai.

Na sake fashewa da kuka mai gunji!

Ta kama ni sosai muka nufi d'an wajenmu a hankali take ta fad'in." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.

Na kama ni ma idan ta ajiye na d'auka.

Ta zaunar da ni saman tabarma tana cewa Hajara ta d'auko mata mafici.

Ta kar'ba ta fara fifita mini har yanzu ba ta cika ni ba domin ni kaina nasan ba a hayyacina nake ba gabana duf-duf kawai yake yi mini daga zarar na yun'kura zan tashi sai ta riko ni.

Gabad'aya yaransu da manya sun yi cirko cirko a gaba.

Da wani irin sauti na ce." Wayyo Allah anti Yagana kina ina?" Na silale saman tabarmar na kwanta hawaye suka dinga biyo gefan idona.

Na riga fa nasan mutumin nan ya mutu kawai a fito a gaya mini ne ba za a yi ba.

Na riko hannunta ina sake tambayarta a karo na biyu ta girkiza kanta tana cewa." Na gaya miki fa bai mutu ba Hajiya yana da rai in sha Allahu."
Na zuba mata Idona kafin na ce." Wuyansa ya karye ana gane alamun rashin rai a jikin dan adam tana nan fa kada ku yaudare ni."
Ta ri'ke ni da kyau a hannunta sai ta dubi yaran tana fad'in." Ku tafi ku yi alwala kowa ya d'auko al'kur'aninsa a yi karatu.

Jin haka ya sanya ni k'ara gazgata abinda zuciyata take gaya mini me yasa ba su yi karatun tun d'azu ba sai yanzu k'wa:kwalwata ta dinga gaya mini cewa a gidan mutuwa ne kad'ai ake yin karatun al'kurani.

Jakata na d'auka da take ajiye a gefena na d'auko wayata a karo na shida number Hajja na kira ta yi ringing sau biyu a na ukun ta d'aga.

Tana magana na yi shiru hannuna yana ta rawa kiran sunana take yi Amina, Amina, bakina ya yi nauyin gaske hawaye ya ziraro daga idona cikin 'karamin sauti na ce." Ya mutu Hajja ta kashe mana Babanmu Hajiya Maryam ta cuce ni......
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: *Gudun aure paid book complete 2k k akan telegram normal What'sapp group kuma 1k via 0542382124....

Binta Umar Opey bank*
*127*
Da tsananin damuwa nake jin ta tana kiran sunana na ajiye wayar ba tare da na kashe ba jikina na rawa sosai na 'kunshe bakina da hannu jin yadda wani mahaukacin kuka ke ko'karin kufce mini.

Mahaifiyar Hajara da na ji suna kiranta da Inno ta d'auki wayar tana fad'in.

Hajiya halima ce.

Daga daya bangaran ita hajjan tana ta fad'in." Ko Baba Sulen ya rasu Amina domin shekaran jiya Kamalu ya ce mini ya je ya duba shi a can asibitin Murtala an kwantar da shi.

Amina, Amina kina ji na."
Ta ce." Ni ce Inno uwargidan Malam D'aha nan Bunkure."
Hajja ta ce." Inno me yake faruwa ne, wanene ya rasu ina Amina take?"
Duka ta jero mata wad'an nan tambayoyin.

Cikin sigar kwantar da hankali ta ce." Babu wanda ya rasu Hajiya Halima gigitace dai kawai ta sanya har ta gaya miki haka."
Ta ce." Inno ki gaya mini gaskiya kin san dai ni ba yarinya ba ce?"
Sai ta dabarbarce ta kasa gaya mata komai.

Zuciyata ta sake karyewa tabbas bata da abinda za ta fad'a kuma da bakinta take cewa bai mutu ba gashi yanzu an tambayeta ta yi shiru.

Ina jin Hajjan tana ta magana Inno ki gaya mini menene, ki bawa Amina wayar mu yi magana na ji ta a kusa dake tana kuka."
Ta miko mini wayar jikinta a sanyaye.

Na kar'ba nasa a kunnena na ji tana fad'in." Yi shiru ki kwantar da hankalinki Amina ki gaya mini abinda yake faruwa kin ji ko, ki gaya mini ko menene ina sauraranki."
Da kyar na daidaita kaina na ce." Muna nan Bunkure ni da Baba amma ban san halin da yake ciki ba yanzu Hajja ki zo don Allah."
Ta ce." Yi shiru zamu zo in sha Allahu, yanzu dare ya yi amma da asuba zamu d'auko hanya dukkan tsanani yana tare da sauki."
Ban iya cewa komai ba sai jan hanci na ji ta kashe wayar sai ni ma na ajiye tawa na matsa jikin bango na takure can 'kasan zuciyata ina ta ambaton Allah akan ya kawo mana d'auki.

Dare ya tsala sosai muna zaune a tsakargidan ni da Inno mu biyu kacal ta yi ta yi da ni na shiga na kwanta na ce mata ta barni ko na kwanta din ba bacci zan yi ba gabad'aya hankalina na sashen malamin shiru ya hana kowa shiga Sukairaju da yan uwansu su Dahuru tunda suka shiga dashi ban sake ganin gilmawarsu a hanyar ba Rabi'u ne ya shiga sau d'aya kafin ya fito ya nufi bangaransa dake cikin gidan bai sake fitowa ba.

Muna zaune har aka kira sallar asubahi.

Kowa ya fito ya yi alwala yara da manya na yi na shiga d'akin da suka sauke ni a tun farkon zuwanmu gidan na yi sallah ina kuka sosai ina yi wa rayuwarmu addu'a.

Karatun al'kurani tun daga almajiransa na waje da cikin gidan iyaye da yaransu.

Na kar'bi al'kur'ani wurin Hajara na bude nima ina karantawa a hankali a hankali na ji zuciyata tana sanyi.

Gari ya fara haske Hajja suka shigo gidan ita da Hajiya Saratu da kanin mahaifinsa alh Sa'idu.
jin maganarsu ya sanya na rufe al'kur'anin da sauri na fito tsakargidan.

Inno ta sauke su tare da shimfida musu tabarma suka zauna yanayinsu ya nuna tsantsar tashin hankali a haka suka dinga gaisawa da jama'a.

Ba su wani jima da zama ba.

Rabi'u ya fito daga wurinsa suka gaisa a gurguje ya nufi sashen malamin minti biyar a tsakani ya fito tare da fad'in." Hajja Malam yana magana."
Kusan a tare muka tashi gabad'aya ya shige mana gaba kowanne mu zuciyarsa na dokawa.

Yana zaune saman buzu da al'kur'ani warshu mai falle-falle a hannunsa d'akin tsaf Y
yana ta k'amshin turaran wuta.

Can muka hange shi kan wata katifa madaidaiciya da shimfidar bargo a samanta.

Yana kwance sambal sun cire masa rigar jikinsa daga shi sai singileti da dogon wandon rigar da suka cire hannayensa nade a k'irji ido a rufe.

Kafafuna suka fara kyarma Hajja kuwa kuka ta sanya tana fad'in." Me ya faru Malam ma'kiyane suka jefe shi ko, Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ta nufe shi tana kuka sosai ta tsaya a kansa tana fad'in." Ni kuwa me ka yi wa jama'a ne Tajo daidai gwargwado kana alheri da kyauta da yawa wasu na ta ganin wautarka akan dukiyar da Allah Ya baka.

Ka yi kyautar hajji ka yi ta umara, ka yi kyautar kud'i ka yi ta gida da mota da jari, duk hakan bai yi musu ba sai sun kwantar mini da kai."
Shiru d'akin ya yi tana kuka da sambatu Hajiya Saratu na kusa da ni tana goge hawaye ta ma kasa zuwa inda yake kwance.

Gabad'aya ta gigice sai kuka take yi na kasan zucciya.

Ni kam idona bushewa ya yi k'amas ban yi mamakin hakan ba wata'kila hawayen idona ne ya 'kare sai dai wani kutittiran abu da nake jin sa ya tokare mini a wuya.

Da na d'aga kaina na dubi wurin da yake kwance sai gabana ya yanke ya fadi.

Alhaji Sa'idu ya tashi a hankali ya je ya kamo hannun Hajja ya zaunar da ita a gaban malamin wanda tunda take koke-koken bai ce komai ba.

A nutse ya had'a al'kur'anin da yake hannunsa ya mayar da shi ma'adanarsa ya kalli Hajja da har yanzu ta kasa nutsuwa ya ce." Hajiya Halima kukan ya isa haka, mu godewa Allah da ya takaita lamarin kuma aka samu hanyar warware shi cikin sau'ki.

Littafin nan na kudi ne yar uwa kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Kamar yadda ki ka sani dai ni malamin zaure ne mai almajiran mai kuma hidima da al'kur'ani.

Na ji dad'i sosai da Allah ya tsawaita mini nisan kwana wannan al'amarin ya kasance ya kuma ba ni iko da damar warware shi.

Ba ni cutarwa ta hanyar sanin da Ubangiji ya ba ni kamar yadda wasu malaman suka d'auki wannan hanyar ta zalinci domin neman abinci da cutar da hallitar Allah.

Hakika a wani zuwa da Alhaji Tajo ya yi gare ni wattanin baya na karanci akwai rikici da makaru a tattare da shi.

Wannan dalilin ne ya sanya ni gaya masa cewar ya dage da addu'a akan shi da kuma yaransa idan ban manta ba na tambaye shi iyali da adadin yaransa ya sanar da ni.
Chapter 188 · 0% Book details