Sashe 102
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*67*
Wajejen sha biyu na rana Sahura ta kira ni a waya a nutse na d'auka muka gaisa amma babu cikakkiyar walwala a tare da ita fara da cewa." Yanzu sis ashe dai sai da ki ka sanya kafa ki ka shure shawarata ko? jiya na dawo daga aiki na tarar da Yusra a gida da yamma Baba Tabawa ta shigo tana gaya mini kin yi tafiya zuwa maiduguri gaskiya ba zan boye miki ba ban ji dad'in abinda ki ka yi ba domin kuwa yanzu nan muka gama waya da anti Yagana
tana tambayata wai ko nasan wani abu da yake faruwa game dake."
Ta nisa kafin ta cigaba da cewa." Na ce mata kin gaya mini amma kin ce sirri ne, shine ta ce to na bar shi ba sai na gaya mata ba tunda amana na kar'ba a wurinki.
Sai kawai ta kashe wayar a sanyaye Ni kuma gaskiya na ji rashin dadin hakan mai yasa ki ka boye mata abinda yake faruwa da rayuwarki Amina bai kamata ace har sai ta fito duniya tana neman dalili ba."
Murmushi na yi mara armashi na ce." Sahura hakan da na yi shine kwanciyar hankalina da kuma samun nutsuwata don Allah kada ki ka ga lefina kada ki 'kullace ni, addu'a kawai nake so ki taya ni da ita, sannan maganar anti Yagana kuma ni na fi kowa sanin halinta kwata-kwata ba ta kar'bar uzurina in dai akan mutumin nan ne to bata ta'ba fahimtata kamar yadda ke ma ba kya gane nufina.
Wannan dalilin ya sanya ban gaya mata ba domin lefinsa za ta take da k'afarta ta rufe gabad'aya ta d'auka ta d'ora a kaina, to shiyasa ko da na yanke shawara ban nufe ta ba kai tsaye na yi tafiyata a gidan Baban Saude."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce." To ke yanzu me ki ka yanke a zuciyarki rabuwar ki ke ganin itace mafita a gare ki ko kuwa, tunda kina ganin kin fi karfin ki d'auki shawarata Amina to ni menene sai kin gaya mini ba'kar magana a fakaice.
Kowa rai ya yi dad'i ai barin mai shine.
Ni dai tun tasowarmu ban ta'ba saninki da wannan mugun taurin kan ba, sai da Allah ya rufa miki asiri ki ka ji kina kama 'yan-canji tukkuna ki ke ganin karanki ya kai tsaikon da za ki iya cin mutuncin kowa.
Tuntuni na sha gaya miki aure ibada ne shiyasa iyayenmu koyaushe suke jaddada mana mu kyautata ha'kuri domin kuwa shine kaso mafi rinjaye a zamantakewa irin ta aure.
Na gani da idona na ji labari a bakin da ba zai kirkiri 'karya ba oga yana sonki irin son da yake da wahalar samu.
Yana ta tataki yana yi miki duk abinda ki ke so.
Kin zubar masa da ciki saboda tsabar son zuciya kin tafi yawon kai shi k'ara gari ya gari har maiduguri kamar wannan mutumin Amina anya kina da hankali kuwa.....
Ba tara k
rasa ba na katseta da saurin gaske domin kuwa zuciyata ba zata iya jure hatsaniyar da take yi mini ba.
Sahura bata ta'ba ba ni haushi ba irin yau.
A fusace na furta." Na kai shi k'arar Sahura shi din wanene Annabi ne ko kuma walliyin Allah da har ake gudun 'bata masa rai.
Ina ruwana da dukiyarsa mutum ne fa kamar ni mai tarin zunubai mai kashi da fitsari, mai yasa zan tsaya jin tsoro da shakka a kansa tunda yana tsuguno a masai kamar yadda nake yi.
Ai da yana da bambamci da sauran hallita ne sai na saurara masa.
Na gane dake da anti Yagana so kuke na zauna 'bakincikinsa ya kasheni to akan wane dalili.
Shi kadai ne namiji a duniya da har zan jira yana b'ata mini rai, bai fi karfin na kai shi 'kara ba wallahi tunda ni dai abin hannunsa bai bude mini ido ba.
Yarana suna buk'atata to ban ga dalilin da zai sanya na zauna wata hallita tana kuntuka mini ba." Na kare magana ina nishi saboda tsananin b'acin ran ganin yadda mutumin nan yake nema ya shiga tsakanina da makusantana.
Itama da tsananin b'acin rai ta furta." Ni ina nema a wurinsa kuma ina ci da sha a karkashinsa na gode miki da ba'kaken maganganu da kuma gori, ki cigaba da yin fito na fito da umarnin Allah da kafarki za ki taka siradi tunda mutumin nan kin zalince shi kin kuma sa'bawa Ubangijin da ya hallicceki."
Jin muryarta tana rawa ya sanya na sassauto a hankali na ce.'" Sahura don girman Allah kada ki juya mini bayana, ki tuna irin gwagwarmayar da muka yi a baya, kada ki yadda mutumin nan ya raba zumuncin da yake tsakaninmu don Allah ki fahimceni wallahi yana zalintata.
Na yi lefi na bada ha'kuri, na tuba ga Allah to a yafe mini mana menene za a dinga yi mini gashin 'kuma a fakaice idan dama mutum bai taki wani abin ba.
Ta yi shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." To shikkenan na ji, yanzu me ki ka yanke akan abinda ki ka yi?"
"Ban yanke komai ba Sahura sai abinda Allah Ya zaba mini, idan har rabuwar itace alheri ina farinciki da hakan, idan kuma akwai sauran zama a tsakaninmu to gaskiya ba zan koma ba lallai sai ya fahimci cewa abin fa da yake aikatawa kuskure ne, sai ya dauki matakin gyara da alkawari tare da sharad'in hakan ba zata sake faruwa ba.
Murmushi ta yi irin na takaici kafin ta ce." Amina wani lokacin ina mamakin tsaurin idonki wallahi to wai Baban Sauden ki ka wakilita da ya kira Yallabai din ya titsiye shi akan kuskuran da mafi rinye ke ce mai shi.
Idan fa an bi ta 'barawo to a bi ta mabi sawu na gaya miki tun ranar da na zo gidanki wallahi ke ce mai lefi mai yasa za ki zubar masa da ciki saboda wani banzan dalili da bashi da tushe.
Son zuciya ne fa wannan tsagwaronsa ki ka nuna masa a zahiri saboda ke ai kina da yaran shi kuwa fa.
Ki bari ki haihu mana ki ga abinda za ki haifa da lafiya ko babu kawai sai ki yankewa Allah hukunci, ba zan gaji da gaya miki ba, baki da gaskiya."
Cike da tsantsar takaicin kasa fahimtata da ta yi har yanzu
Na ce." Ban kyauta ba din Sahura duk abinda za ku yi ku yi din, haba na gaji da magana daya wai ana aure dole ne ko kuma tilas aka ce sai na zauna da mutumin nan da za ku bi ku tsangwameni. uwata ce ke da za ki kira ni a waya kina gaya mini maganar da ranki ya so, ko kuma ke ce ki ke zaune da mutumin nan ne, kwata-kwata kun kasa fahimatata, na yi kuskure na nemi afuwar Allah amma gabad'aya kuna juya mini magana saboda kawai wani dalili naku.
Ina kara jadadda muku shi ai ba sahabi ba kuma ba Annabi ba ne da ba za a 'bata masa rai ba.
Ko annabawan Allah suna kuskure balle wani bawa kuma Allah Ya yafe musu saboda haka a yanzu daga ke har anti Yaganar ba na buk'atar ku fahimce ni, duk abinda za ku yi akan lamarin kun jima ba ku yi ba." Ina gama maganata na kashe wayar raina a mafisar b'ace.
Tunda muke da Sahura ba mu ta'ba musayar yawu mai zafi irin wannan ba.
Haba na gaji da jan magana d'aya muddin ba za su gane hujjata ba to sai mu yi ta tafiya a haka ba zan sake yarda wata ta kira ni a waya ta 'bata mini rai ba.
Wannan littafin na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Da takaicin abinda y
faru tsakanina da Sahura na yini duk yadda na kai ga ko'karin ganin sun fahimceni ita da anti Yagana abin ya gagara har sai da sa'bani ya gifta a tsakanimu, to kuwa ta yaya za a yi kuwa na manta da mutumin nan tunda ta dalilinsa anti Yagana take furta maganar da ban ta'ba tsammanin fitowarta daga bakinta ba, wai za ta rabu da ni har abada saboda shi yau ga Sahura tana gaggaya mini ba'kaken maganganu.
Ban ta'ba nadamar saninsa ba a rayuwata sai a wannan lokacin.
Da daddare muna zaune a babban tsakar gidan gabad'aya har da maigidan Baban Saude an shimfida masa dadduma mu kuma muna zaune a 'katuwar tabarma ana ta hira cikin nisha'di cikin raina ina ta mamakin hakan wato duk wanda zai k'alubalanci Baban Saude akan wani lamari tabbas ba zai zauna dashi ba ne, sannan kuma bai gama karantar hali da d'abi'arsa ba.
Dada da Anti Yagana suka yi sallama a lokaci daya suka shigo gidan.
Ganinsu a tare ya sanyayar mini da jiki domin kuwa na tabbatar da cewa anti Yagana ce ta je ta gaya mata abinda yake faruwa.
Suka zauna akan tabarma ana gaisawa Baban Saude yana cewa da Dada ba ta gaya masa za ta zo ba a d'azu da safe da ya je can gidanta domin su gaisa.