Sashe 94
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban tanka masa ba na kama hanyar fita sai ya taso da sauri ya biyo bayana da wayar a kunnansa da maigidansa yake waya saboda yadda yake yin kasa da murya cikin ladabi kamar yana kusa dashi.
"Ranki ya dad'e barka da asuba."
Muryarsa na ji a daf da ni, na juya ina dubansa yana biyo bayana da wayar a hannunsa..
A takaice na ce" Barka kadai Sukairaju ya kake?"
Ya ce." Alhamdulillahi, idan ba matsala Ina iya yi miki rakiya don yanzu muka gama magana da oga ya ce na biyo bayanki."
Cikin jin haushi na ce." Makauniyace ni, da za ka biyo bayana ko kuwa ban san gari ba."
Ya girgiza kai cikin ladabi ya ce." Ko daya kulawa ce da kuma bin umarnin maigida."
Na ce." To ka kira shi ka gaya masa na ce ba na son kulawar wannan wace irin masifa ce ne ."
Sai ya tsaya ya yi sararo.
Na ja tsaki na fara tsayar da abin hawa shi kuma ya fara laluban wayarsa da sauri ya kara a kunne yana cewa." E to ga mu nan ni da ita atare a bakin titi tana tsayar da mashing tana tare da k'aramar akwati."
Ina jin sautin muryarsa amma ban ji abinda yake cewa ba.
Daidai lokacin adaidaita sahun dana tsayar ta yi parking na yi saurin shiga.
Shi ma da sauri ya zagaya ya zauna kusa da direban shi kuwa ya ja babur din ya hau titi.
Takaici kamar ya kasheni, ni wulakata mutum ba dabi'ata ba ce, kuma ba na so na fara akan mutumin nan tunda na lura shi ma yana gyara hanyar abincinsa ne, kuma duk umarnin da aka bashi dole ya bi.
Ban ce masa komai ba har muka isa tasha na fito, shima ya fito da kudi ya biya direban ya zo yana ko'karin kar'bar akwatin hannuna.
Na ce." Kira mini ogan naka a wayarka."
Da sauri kuwa ya fito da wayar daga gaban aljihunsa ya kira shi ya miko mini wayar kafin ya daga na matsa can gefe wajan da babu hayaniya sosai duk da safiya ce amma tashar cike take da jama'a.
Yana d'agawa ya fara da cewa." Sukairaju ya aka yi, na gaya maka duk inda ta sanya kafarta ka ajiye taka anan ka kula sosai da ka ji ko?"
Na ce." Bashi ba ne ni ce Amina."
Ajiyar zuciya ya sauke ya furta a Ina ki ka ajiye wayarki ina kira baki daga ba." Lokacin da ya kira tana cikin handbag d'ina kuma na ji kiran ina sane ban daga ba.
Na ce." Tana hannuna wayar ba ni da lokacin d'agawa ne."
"Okey na ji, ina za ki je da sanyi safiya haka harda akwati kin san duk inda ki ka nufa ba ki tsira ba tunda da aurena a wuyanki."
"Shiyasa kenan ka bada tsarona saboda kada na gudu yawon bin maza ko."
Shiru ya yi bai tanka mini ba.
Na ce." Idan kana kan layi to don Allah ka umarci wannan gardin da yake bina a baya ya koma, ko kuma ya tattaro ya dawo karkashin aikinka dan banga amfanin zamansa a gidan mutane ba face dora musu nauyi da ya yi, domin ni na gaya maka ban mayu ba har abada zama ya kare a tsakaninmu."
Hankalinsa a kwance ya ce" mutan gidan ne suka ce miki sun gaji dashi saboda yana dora musu nauyi ko kuma sharri ki ka yi musu."
Da sauri na tari numfashinsa ." Sai sun fad'a sannan za a gane yanayin rayuwa ya za a yi baligin mutum kamar wannan ka zo ka ajiye shi a gidan mutane da sunan bada tsaro akwai wani tsaro ne wanda ya wuce wanda Allah yake ba ni tun kafin a haife ni."
"Zan kira anti Yaganar na ji shin cewa da yawunta ne ki ke fad'in hakan, na san halinta da karamci ba za ta ci zarafin bako ba."
Jin abinda ya ce sai jikina ya d'an yi sanyi nasan halinsa tsaf zai iya kiranta ya tambayeta.
Kashe wayar na yi ban tsaya saurarar abinda yake cewa ba.
Kafin na mikawa masa abarsa ya kara kira na daga wannan karon cikin tsare gira da kaurarriyar muryar da babu wasa ya furta." Ki gaya mini Ina ki ka nufa yanzu domin na ji hayaniya da karar ababan hawa hala kina cikin tasha ko?"
Na ce." Eh ina tasha zan nufi kano domin duba jikin Gwaggwo da izinin Allah, zan kuma biya na gaishe da Hajja."
Ya sassauta yana fad'in." Na amince dai ki je ki duba Gwaggwon amma ban amince miki zuwa wurin Hajja ba, ke kwata kwata ma ba na so asan kin shiga garin, ki zauna a gidanku kawai kwanaki biyu zan gama yi muku shiri sai ku biyo jirgi ku dawo gida ga'badaya."
Na ce." Gaskiya ba zan iya shiga garin kano ban je wajan Hajja ba sai da ka yi hakuri.'' Kai tsaye na fadi hakan domin a karon farko na fahimci akwai abinda yake b'oyewa dama na san duk abind
a yake faruwa ba ta sani ba."
Ya sake sassauta murya cikin sigar rarrashi ya ce." Na ji kije amma kada ki gaya mata duk abinda ya faru tsakaninmu sanin kan ki ne bata da lafiya."
Na ce." Ai ta inda aka hau ta nan ake sauka Yallabai, ai ba auran 'yar tsana muka yi ba sai da waliyyai da shedu suka shaida to me zai sanya kuma a boye musu saki yana da kyau ta sani yanzu saura igiya biyu."
Diriricewa ya yi ya fara fad'in." Ki saurare ni ki ji, na gaya miki wallahi muddin ki ka sanar da Hajja wani abu sai na sa'ba miki, kin ji na gay......Datse wayar na yi Ina jin wasai a cikin raina na tabbata ta wannan hanyar ma kadai zan hukunta abina.
Ya yi ta kiran wayata ban daga ba, da ya gaji sai ya kira ta yaron nasa, kimanin minti goma suna magana kafin su gama wanda ni lokacin ma na gama da wani direba inda na d'auki shatar mota guda na biya..
Ya k'araso yana tambayar direban yadda muka yi duk ya gaya masa ai na riga na biya ba tare da ya dube ni ba yake gayawa direban tare za mu tafi.
Na dubi direban ina fad'in.'' Ni da na biya ka kudin motar umarnina zaka bi ko nasa."
Cikin ladabi ya d'an risinar da kansa ya ce." Ranki ya dad'e umarninki zan bi, amma yana da kyau mu tafi tare dashi tunda yana tsoronki ne kin san fuskarki da ta maigidanki ba 'boyayyiya ba ce, ni na yi mamakin ma ganinki cikin tashar nan.
Jin haka ya sanya da sauri na bude motar na shiga domin sam ban yi wannan tunanin ba yanzu abin sai ya zama magana da yayatawa kafafen sadarwa.
Na dubi Sukairaju da yake ta ko'karin sanya akwati a bayan mota na dan leka ta tagar motar a nutse na ce." Ka je ka taho da Yusi ina nan ina jiranka."
Yadda ya amsa da sauri shi ya tabbatar mini da cewa bai kawo cewa dabara na shirya masa ba.
Ina ganin ya shiga adaidaita sahu.
Na dubi direban da yake jingine a jikin motarsa na ce." Ka shigo mu tafi na gama magana dashi ya koma gobe zai biyo bayana da yarona."
Ya d'an yi jim yana kallona kamar bai yarda ba, na 'bata rai tare da cewa." Ka ga idan ba za ka je zan fito na nemi wata motar menene hakane?"
Ya bude motar ya shiga ya zauna a mazauninsa jikinsa duk babu k'wari haka ya kunna motar wani abokinsa ya zo ya tsaya suka d'an yi magana kafin ya bar wajan shi kuma ya ja motar muka fita daga cikin tashar sai sannan hankalina ya kwanta.
Don girman Allah ki biyani hakkina kafin ki karanta mini littafi kada ki bar nauyin wani akanki.
Bayan mun d'auki hanya sosai na kira Hamusu domin jin a ina aka kwana nasan tunda mutumin nan ya yi ruwa da tsaki akan lamarin nan da wahala gwaggo bata kwana asibiti ba.
Illai kuwa muna gaisawa ya fara da cewa." Yanzu nan da na fito daga wanka nake shirin kiranki wallahi, jiya wajan goma da rabi na samu kira daga maigidanki ya ce mini mota tana zuwa daga asibitin Malam za ta d'auki Gwaggwo babban likita zai dubata sosai.
In takaice miki dai Gwaggo tana can an bata gwado kuma jiki da sauki alhamdulillahi na dawo gida domin na yi wanka, anti Amina ki kara yi mana godiya a wajansa lallai yana abinda ya dace da dukiyarsa wallahi anti Amina d'akin da aka kwantar da Gwaggo daban yake da sauran ita kadai ce ba hayaniya kuma tun jiya da daddaren likitoci suka ta zaryar shigowa dubata."
Jikina ya d'an shika kad'an jin yadda Hamusu yake yi mini bayani kamar ya fashe da kuka sai godiya yake yi.
Cikin raina na ce.' Haushinka yake ji Hamusu amma saboda iya taku da neman suna ya dabaibayeka da alherinsa ta inda da wahala ka hangi kuskuransa.
Na ce." Babu damuwa Hamusu ai Gwaggwo ta wuce komai, ni ma gani a kan hanya in sha Allahu daga zarar na sauka zan kira wayarka."
Babanmu na kira na gaya masa ina kan hanya.
Na kira Sahura itama na sanar da ita, daga nan sai na fara tunanin inda zan sauka, ba zan iya zuwa gidan Hajja ba gaskiya gidanmu kuma babu spece d'akin da na yi zawarci Ummansu Saminu tana kiwon kaji.
Kawai sai na yanke shawarar sauka a gidana na kuntau.
Yana kulle har yanzu shagon ne dai ake ta hada hada a cikinsa dama mun yi da Hamusu cewa idan auransa ya tashi zai zauna a ciki gidan to an samu tsaiko ne daga bangaran budurwar da yake nema babanta ya ce sai ta yi karatun likitanci shi kuma ya'ki ya canza wata ya dage sai ita yanzu dai an kai kudi an sa rana shakara uku mun ci shekara daya yanzu saura shekara biyu.
Sake kiransa na yi a karo na biyu na umarce da cewa ya sanya yara su wanke gidan su gyara shi sosai, shekara kusan biyu dole a samu datti.
Ya ba ni tabbacin cewa kafin na sauka za a kammala.