← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 276

Sashe 34

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajja ta yi wa babyn wanka ta shiryata tsaf sannan aka sanar da maigidan halin da ake ciki.

Ban ta'ba ganin zahirin farincikinsa ba kamar wannan rana a lokacin da ya d'auki babyn sai da ya dan zubar da hawaye kafin ya danne zuciyarsa ya dinga godiya ga Allah bisa abinda yake yi masa.

Sai ya dubi Hajja ya dubi babyn ya ce" Ban taba riskar kaina a cikin farinciki ba kamar yau Hajja Ni ma na zama Baba."
Ita dai dariya kawai take yi tana fad'in." To ai babu abinda ya gagari Ubangiji Tajo.

A ranar ya yi mata hud'uba da Nana Aisha dalilin k'aunar mai sunan bisa irin gudumuwar da ta bawa Ma'aiki S.A.W.

Gari yana kara yin haske ya kira likitan da tunda na samu cikin take zuwa ta duba ni akan ta zo ta domin ta duba lafiyarmu ni da babyna kasancewa haihuwar gida ana samun matsala mabambamta."
Cikin ikon Allah ko da ta duba mu lafiya lau babu wata matsala, a lokacin Allah ya lullube mata abinda yake da kawai.

Dangi da 'yan'uwa daga bangarena bangaransa suna ta bugo waya domin addu'a da fatan alheri mussaman abokanansa sun taya shi murna sosai a yayin da yake ta shirye-shiryen kayatattaciyar walima.

Ni ma inata gayyatar mutane dan mun yi waya da Anti Yagana ta ce mini za su da yawansu daga maiduguri Sahura ma haka.

Shi ma Yusi Yana nan yana ta gangamin gayyatar abokanansa da ya hadu da su anan din.

Hajja kamar dama a bangaranta ba a cewa komai ba, dan idan naga yadda take zumudi har tausayi take ba ni, ta kasa zaune ta kasa tsaye.

Hadiza itace mai kira mata mutanenta a waya, a kira wannan a gayawa a kira wannan a gayawa.

Mutanan Bauchi ma su Inna Uwani suna kan hanyar zuwa.

A yau da ya kasance kwana biyar da haihuwa tun safe mai k'unshi ta zo ta yi mini ja da baki.

Da daddare kuma na ajiye a raina sai na je gyaran gashi.

Nana sunan da muke Kiran babyn kenan tunda ubanta ya riga ya yi mata huduba da sunan tana wurin Hajja tana bacci dalilin da ya sanya ma kenan na saki jikina da yawa domin yarinyar ba mai yawan kuka ba ce sa'banin wasu jariran da suke hana iyayensu bacci, tana da ha'kuri sosai idan ta koka to tabbas yunwa take ji, sai ta yini tana bacci a bayan Hajja ko Hadiza.

Tun kafin su k'araso wurin da nake na jin yadda take ta tsala kuka.

Idona akan Hadiza da take ko'karin kwantota daga bayanta tana cewa." Ki sake bata nonon tasha wata'kila
bata koshi ba, kin ganta nan, ta ki bayan Hajja sai tsala ihu take yi, ni ma shine na gwada goyata ko zata yi bacci, ta ce bata san wannan ba.

Hajja tace na kawo miki ita ki bata nono, amma dai naga ta dan bubbuga cikinta wai ko kumbura ya yi.

Na ce.

Hadiza kin ga duka hannuwana a daure da lalle don Allah zo ki taimaka mini fito da nonon asa mata a baki."
Na dan gyara ta sanya mini ita a jiki, amma fir taki kamawa.

A lokacin ne na ji jikinta zafi rad'au.

Na ce." Hadiza ba ki ji jikinta da zafi ba?"
Za ta yi magana kenan Hajja ta iso wajan tana fad'in." Ba ta daina kukan ba, ko cikin
ta ne yake ciwo ne.

Ta miko fidarta tana fad'in.

A bata ruwan d'umin nan ko cikin zai saki."
Na ce." Hajja ba na jin kumburin ciki ne zazzabi ne a jikina, Hadiza ri'ke ta na cire lallan nan."
Da sauri ta dauketa daga jikina, na cire lallan da ba'a jima da sanya shi ba, hankalina gabad'aya ya tashi.

A ki'dime ta ce." Kai Innalillahi!

Hajja kin ga abinda take yi."
Na dago kaina a sukwane! wanda ya yi daidai da lokacin da Hajjan ta 'karbeta daga hannun Hadiza tana jijjigata.

Ban san lokacin da nake k'unshin kafata ba.

Sai gani a tsaye ina ko'karin karbarta daga hannunta.

A lokacin idonta ya kakkafe sai sandarewa take yi a hannun Hajjan na fashe da kuka mai sauti a razane na shiga d'aki na d'auko wayata dake saman madubi hannuna na kyarma na nemi lambar maigidan domin sanar dashi.

Shi ma ya shiga rud'u sosai.

Yana tare da baki don tun wajan shida na safe ya fita, ya ce maza maza mu tafi babban asibitin yara.

Na kashe wayar tare da shiga toilet na wanke kafafuna na fito na zura hijab.

Lokacin Hajjan da Hadiza suna harabar gidan.

Yusi sai kuka yake yi.

Itama Hajjan tana yi.

'Kasimu daya daga cikin direbobinsa ya fito da mota da saurin gaske muka shiga dan Hadiza ko mayafi ma babu a jikinta sai da muka je asibitin tukkuna ta ankara.

Emagency muka nufa abinka da family din babban mutum motar da ta kai mu asibitin itace ta shaidawa ma'aikatan daga inda muke.

Kafin kiftawa da bismillah 'kwararrun likitoci sun rufu akanta..

To duk ko'karin da likitoci sukayi kan ceto rayuwar baby Nana hakansu bai cimma ruwa ba.

To ai dama kud'ira da hukuncin yana wurin buwayi gagara misali.

Allah Ya kaddara kwanaki biyar kacal za ta yi a doran duniya ta koma ga mahallicinta.

Hausawa sukan ce an nuna kama.

Duk na'urori da suka daura mata suka kwance a sa'ilin da suka tabbatar da mutuwartata bayan da jininta ya kone tas sakamakon cutar nan ta sikila wanda uwa da uban basu san cewa su As da As ba ne, sai da hakan da bayyana a tare da abinda suka samu ta hanyar aure.

To shi dai Yallabai din kamar ya yi dan karamin hauka don koda ya zo asibiti lokacin an nannad'e gawar yarinyar kuka ya sanya sosai a ofis din babban likitin da shi ya yi ruwa da tsaki akan ganin an ceto rayuwarta hakan bai samu ba.

Kamar ba babba ba, ko kuma wanda bai san mutuwa ba, ya dinga tsiyayar da hawaye wanda hakan ya kara karya lagon likitan ya dinga rarrashinsa tunda kowa ya san aikinsa ne yin hakan a matsayinsa na likita.

Sai da ya tabbatar nutsuwa ta dan shige shi sannan ya tambayeshi ya akayi hakan ta faru domin yanzu kai ya waye kafin ayi aure ana yin gwajin genotype domin gujewa wahala da haihuwar yara masu d'auke da wannan gagarimin ciwon da yake kashe su farat daya.

Kasa yi masa bayani komai ya yi.

Kawai ya kar'bi takardun sakamakon gwaje gwaje da akayi wa yarinyar ya zira a aljihu.

Da kyar ya iya furta." Idan na samu nutsuwa zan tuntubeka da shawara.

Rungume da ita ya fito a kirjinsa.

Yusi ya ki'dime ya ruga da gudu ya tare shi yana kuka.

Yayin da Hajja take gefe a zaune dan lokacin da aka fadi mutuwar kafarta kasa tsayuwa ta yi ta silale ta zauna a dandagaryar kasan wajan tana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ina kallon Hadiza ma tana share hawaye wani na zuba sai ri'ke hannuna take yi amma ta kasa ce mini komai, lallai ranar naka sai naka.

A lokacin ni kasa cewa komai na yi kukan ma ban iya ba can kasan zuciyata dai Ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! amma ina jin yadda wani kutittiran abu ya zo ya tokare mini a kirji.

Ban kara tsunkewa ba sai lokacin da ya fito da gawar rungume a kirjinsa.

Sai kawai wasu hawaye masu zafi suka fara silalowa suna sauka a kumatuna.

Muka tsirawa juna ido, domin kuwa mu kad'ai ne muka san irin artabun da aka sha kafin samuwar cikin.

Ya k'araso wurin da muke idonsa jawur hakan ya ba ni tabbacin da da cewa kuka ka yi.

Ban ga aibunsa domin duk yadda zan fasalata muku tsananin k'aunar da yake wa babyn ba zaku fahimta ba.

Ya tsuguna gaban Hajja dake tankwashe da kafa sai kace wadda take tsakar dakinta.

Ya dan bude fuskar babyn ina dan kallonsu ta gefan Ido domin gabana buguwa kawai yake yi don sai nake ganin kamar zai gayawa Hajja bata mutu ba.

Na ga hawaye ya silalo daga idonsa a sha'ke ya furta." Hajja ta rasu da gaske, ina cikin wani yanayi wanda ba zan iya tantancewa ba ki taya ni da addu'a."
Hajja ta sanya gefan hijabinta ta goge hawayen idonta.

A nutse ta sanya hannu taja tawol din ta rufe mata fuska tana cewa." Ka yi hakuri, haka Allah ya kaddara, ba mai nisan kwana ba ce, mu je gida kawai a suturta Allah Ya sa mai ceto ce."
Yasa hannu ya goge fuskars kafin ya lalabi gilashinsa dake cikin aljihu ya sakaye idonsa, sannan ya mike tsaye likitan da escorts d'insa tare da Yusi suka bi shi a baya.

To ni din na ma fi su karfin hali domin tunda a karin farko na ambaci Innalillahi wa'ina ilaihi! na ji kwarin guiwa don ban sare ba, na ajiye a raina cewa dama ba mai nisan kwana ba ce.

Ni na taimakawa Hajja ta tashi na gyara mata takalmanta ta sanya muka nufi bakin motar da jama'a suka yanyameta....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k ne akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.
Chapter 34 · 0% Book details