← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 276

Sashe 176

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tsanake na gaisheta ba tare da tashi ba ta amsa mini tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya ta furta." Gobe da wuri zan kama hanya Amina, jiya da daddare Babansu Fadila ya kira yake gaya mini mijinta ya zo ya ga masa bata da lafiya har da su k'arin ruwa."
'Yar dariya na yi kafin na ce." Anti Yagana ta kusa goya jika kenan."
Harara ta mako mini tana tabe bakinta."
Na ce." E, mana anti ai idan ki ka ji an fara da haka to k'aruwa ce."
Ta girgiza kanta tana fad'in.

" Yaran yanzu ba sa saurarawa 'ya'yan mutane daka an kai maka yarinya wata d'aya biyu zuwa uku ka had'ata da lalura wasu fa ko shekara ba sa yi suke haihuwa."
Da murmushi a saman fuskarta na ce." Hakane anti Yagana ai gwara matasan su yi auran da wuri ya fi alheri akan su dinga zinace-zinace kuma bari na gaya miki wani abu ba fa samarin ne kadai suke da wannan 'kawazucin ba har da 'yan matan wallahi dukkaninsu son auran suke yi."
Ta yi shiru tana ta'be bakinta.

Na ce." Kawai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su lafiya, domin tunda ki ka ji an fara da haka to an gamu."
Ta ce." To Allah Ya raba su lafiya." Na amsa da "Amin ko ke fa."
Muka dan yi shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." Wallahi ina tausayawa jama'ar da suke k'arkashin matar nan, da yawa akwai wad'anda suke d'aukar dawainiya mai yawa ta iyali iyaye da yan'uwa duka a 'karkashinta yau gashi ta fad'i ta mutu dole za su shiga wani yanayi wanda ba zai yi musu dadi ba.

Su kadai nake tausayawa sosai dalili yaranku da suke ri'ke a hannunta ai jajensu k'alilan ne tunda kuna raye sai ku cigaba da kula da yaranku Amma jama'ar da suke ci da sha a 'kasanta Allah ne kad'ai ya san su."
"Hakane anti Yagana to ya za a yi ne?

Lokacin ta ya yi cikinmu gabad'aya babu wanda ya isa ya dakatar da komawarta ga wanda ya halliceta hakika ya fi mu sonta shiyasa ya kira ta zuwa gare shi."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Ubangiji Allah Ya sa mu dace amma mutuwa kadai wa'azi idan har za mu hankalta."
Haka muka kasance a d'akin muna tattauna batutuwa da yawa har garin ya yi haske sosai
Gidan Hajiya Maryam marigayiya.

Yabi ta dube shi yana tsaye a jikin bango ya rungume hannuwansa a k'irji.

Bashir ne k'aninsu namiji da ya rage musu a maza tunda d'ayan ya rasu sai shi kad'an yanzu yana can yawon barkinsa ya ji rasuwar.

Dukkaninsu sun fi shekara
Takawas rabon da su gan shi, amma dai suna jin labarinsa cewa yana can Legos agege yana harkar sayar da tabar wiwi da sauran kayan gusar da tunani.

Jiya cikin dare ya sauka yau da safe suka wayi gari da tashin hankali domin ya ritsa su a d'aki gabad'aya har da yaran marigayiyar wai sai an raba gado an ba shi rabonsa ya koma bakin sana'arsa.

Kana jin irin zantukan da yake yi za ka gane mugun d'an kwaya ne ga wani shegen aski a kansa wandon dake jikinsa duk ya zazzago da iyayen sark'oki rakwacam a wuyansa da tafka-tafkan zobuna a tsayun hannunsa.

Su kansu don dai jininsu ne amma bai yi kama da musulunci ba.

Anti Yabi ita ce take bin Maryam shiyasa girman ya koma hannunta gabad'aya yanzu ta dube shi tana fad'in.

Malam yaushe aka yi mutuwar da zaka zo ka daga mana hankali, yaushe rabonmu da kai shekara kusan takwas fa babu wanda kake nema kana can kana yawon iskancinka, ko an gaya maka kowa ma mahaukaci ne irin ka."
Rukky wadda take sakuwarsa ta ce." Anti Yabi rabu dan kutumar......Ba ta k
rasa ba kuwa ya kai mata duka a bakinta yana fad'in." Ni ne dai Bashir ban canza ba zan iya kashe ki anan dan babanki."
Anti Saliha ta ce." Ka kasheta Bashir."
Da sauri ya furta." E, dan babanta ta k'ara sa mini baki ina magana sai na cire mata ma'kogwaro wallahi."
Nabila ta ce." Kai ka shiga hankalinka fa wallahi idan har ka ce za ka daga mana hankali zan sanya a rufe mini kai, haba ina dalili kuma ke anti Yabi da kuke maganar gado uban wanene ya ce muna da gadonta tana fa da miji da yara maza biyu a ciki a iya sanina ba mu da abinda za mu samu a dukiyar anti Maryam."
Rukky ta ce." Ai dama dole ki fad'i haka mana tunda ke kin san kina tare da ita duk wasu muhimmai abubuwanta suna hannunki kin fi kowa sanin sirrinta da dukiyarta dole ne ki fad'i haka."
Yabi ta ce." Wannan zancen banza kike yi Nabila kada ma ki kuskura ki zo da wannan maganar domin kuwa kin fi kowa sanin sirrin Maryam ko mun gaje ta ko ba mu gaje ta ba ba zamu tashi daga zaman makokin nan a banza ba.

Nusaiba ta fashe da kuka! da sauri duka suka juya suna kallonta don wata'kila sun manta da cewa yaran suna wurin.

Ta tashi da sauri ta fita tana goge hawaye Salim da Adam suka bi bayanta cikin damuwa mai yawan gaske.

Suna fitowa suka ganta a tsaye a tsakiyar falo tana kuka tuk'uru.

Salim ya ja hannunta da sauri suka nufi d'akinsu domin da akwai sauran bak'in da suka kwana a gidan dangin Babansu kakarsu ma Hajiya Ayya tana nan da wasu daga cikin 'yan uwanta.

Tana kuka ta ce." Allah Ya sa duka katikan Momi na banki suna hannuna.

Mukullin dirowar nan ne ban san inda yake ba.

Amma tun ranar da za su koma asibiti na kwashe katikan bakinta."
Salim ya ce." Yanzu ya za mu yi anti Nusaiba mu gayawa Hajiya Ayya ko Baba Tajo."
Adam da tunda suka fara maganar bai ce komai sai yanzu ya ce." A a ba yanzu ba tukkuna tunda ko sadakar uku da ba a yi ba, mu bari mutane su watse sai mu sanar da Baba.

Anti Nusaiba duk rintsi kada ki gaya musu cewa." Katin bankunan da take ajiya suna hannunki."
Ta gyad'a kanta tare sanya hannu tana goge hawayen da ta kasa tsayar dashi cikin damuwa ta furta." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wayyo Allah Momi!"
Adam ya je ya rungumeta sosai suka zauna gefan gado yana rarrashinta Salim din shima ya zauna gefenta jikinsa a mutukar sanyaye......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop Kuma 1k via 0542382124....

Binta Umar gtbank.*
*07084653262*
*120*
Yusi Ya fito daga toilet ya same su a zaune shiru.

Ganin Nusaiba a d'akin ya sanya shi d'an sakin fuska ya gaisheta cikin girmamawa ta amsa da yanayi na damuwar da take ciki ta tashi ta fita.

Adam ya mike babu kuzari ya shiga toilet din domin yin wanka.

Shi kuma Salim ya tashi ya fita daga d'akin.

Daga lokacin ya fahimci cewa bayan damuwar da suke ciki ta rashin mahaifiyarsu akwai wadda ta k'aru duk da bai ji komai ba ya san abinda suke tattaunawa a kai ba mai dad'i ba ne.

Yana nan zaune cikin zullumi da nazarin yadda rayuwar 'ya'ya take sauyawa idan suka rasa wani jigo Adam din ya fito a gurguje ya shirya suka fito falon tare wanda ya yi daidai da lokacin da Mairo ta fito tare kaf da yaran kowanne cikin tsafta.

Suka nufi masaukin Hajiya Ayya mahaifiyar Alhaji Amadu kenan wadda take tare da jama'arta.

Bayan sun gaisa anan wajenta yaran suka zauna twins da Minal tunda Mairo tana can suna hidimar d'orawa da saukewa kamar yadda al'ada ta zama a gidan mutuwa.

Yusi ya ri'ke hannun Khalil suka fita tare domin duk zaman da ake yi na makoki da yaron suke zaune gabad'aya gaban babansu suna kar'bar gaisuwar tare.
Chapter 176 · 0% Book details