Sashe 55
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na daure zuciyata na ce." Dama zan gaya maka ne jiya anti Yagana take gaya mini ana biki a can garinsu mamanmu maiduguri shine aka ce a gaya mini, to ina so zan shirya gobe ko jini sai na wuce."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba, kamar ma bai ji abinda na gaya masa ba.
A da kufule na ce." Ka ji."
Bai dube ni ba ya furta." Ban bari ba."
Sai na ji wani 'kullutun abu ya tokare mini a wuya, duk irin suburbudar da ya yi mini jiya da abinda zai saka mini kenan, ai tsayin shekara da wani abu ban ta'ba tambayarsa zuwa wani wuri ba, ban yi tsammanin zai hana ni ba.
Zuciyata na yi mini zafi na ce." Dada ce fa ta ce a sanar mini, 'yan uwa duk za a had'u kowa zai je, to ni me yasa zaka hana ni, tun fa da na zo garin nan shekara har da doriya ban je wani wajan ba."
"Ni dai na ce ban bari ba." Ya fad'a hankalinsa a kwance.
Kawai sai na ji hawaye sun fara gudana a kumatuna.
Ina jin dai d'an tahalikin nan ciwo yake so ya haddasa mini.
Ya dago kai yana kallona lokacin da kukana ya yi karfi.
Sai ya mayar da kansa ya rufe laptop ya rufe ya dan gyara zamansa yana dubana amma bai ce komai ba.
Naja hanci a shake na ce." Wannan zalincin ya yi yawa, kwata-kwata ka hana zuciyata nutsuwa kullum sai ka gumama mini b'akinciki, ban san me na yi maka a rayuwa ba a rayuwa."
Ya ce." Me na yi na zalinci, ba yunwa ba ishirwa haka zalika ba tauye hakki a shimfida, don kawai na hana zuwa unguwa shine zalinci."
Na ce." Zalinci ne mana, kana fita ka yi walwala ka hadu da 'yan uwanka ku gaisa, ni ma na gaya maka Ina so na ga dangina domin Ina kewarsu ina so kuma zuciyata ta samu sasaauci."
"Ko da ke, ko babu ke, za su yi bikinsu, ba ni so iyalina su yi nisa da dai kusa ne sai na barki amma gaskiya maiduguri ya yi nisa, kuma kin ga sai kin yi kwanaki kafin ki ce zaki dawo."
Jin ya fadi haka ya sanya na ce." Ai kai zaka fad'i kwanakin da zan yi."
Ya yi shiru yana lumshe ido kamar me shirin bacci.
Na dawo kusa dashi na zauna na ri'ke hannunsa a hankali na ce." Ka ji my love."
Ya bude idonsa da suka dan canza yana kallona ya ce ." Yaushe rabon da na ji wannan sunan abakinki, yanzu ai kina bukatar zuwa biki ko?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Ya girgiza kansa tare da sake rufe idonsa.
Jikinsa na sake matsawa sosai a hankali na ce." Ka ji sweet love." Bai tare da ya bud'e idonsa ba ya ce." Matsa kada ki sanya na yi abinda ban yi niyya ba."
Ban matsa ba, sai ma hannuna dana sa Ina d'an jan gemunsa a hankali.
Ya bude Ido muka tsirawa juna ido.
Hauwa ta turo kofar d'akin ta shigo hannunta ri'ke da wani kwando cike da kayan abinci.
Janye idonta ta yi ta wuce can wajan da yake zama domin cin abinci ta fara shirya wurin.
A hankali na dan matsa daga kusa dashi ina fad'in." Ka amince ko?"'
"Zan yi shawara tukkun zuwa yamma zan gaya miki abinda na yanke."
Don kada ya tsinka ni a gabanta ya sa na tashi daga kusa dashi ba tare da na ce komai ba na kama hanya fita.
Na ji ta ce." Amina tsaya kawai a yi ta ta kare, ba zan bari a ginu a haka ba domin dukkaninmu musulmai ne, ba maguzawa ba, idan shi mijinki yana jin tsoronki, ni gaskiya ba a haifi wata mace da zan ji tsoro ba, kuma ba zan yarda na yi zaman boranci ba, ba kuma zan yarda a tauye mini hakki ba."
Na ce." Akan me kike wannan zantukan."
Da mamaki da takaici ta ce.'' Au tambayata ki ke yi akan me nake yin magana."
Na ce." 'Kwarai kuwa."
Yana zaune yana jin mu bai ce komai ba.
Ta ce." Jiya girkin waye?"
Na ce." Oho!"
Ta zo iya wuya kawai sai ji na yi ta lallayo ashar ta jefo mini tana huci." Ni za ki mayar sakarai, kina abu kamar mai tabin kwakwalwa, na rantse miki da Allah ba za mu wanye lafiya dake ba, tunda ni ban shiga huriminki ba, ba zai yiwu ranar girkina ki dinga yi mini kutse ba."
Na dube shi shima yana cike da mamakin zagin da ta yi don sai hararta yake.
Na ce." Ka ji tana zagina ko?"
Ya ce." Je ki kawai, ki kyale ni da ita."
Ta kara fusata tana cewa." A dake ni a hana ni kuka, kuma a ce ba zan yi magana ba, sai ta fashe da kuka mai karfi
Ya ce." Idan zagi ne ni zaki ga domin ni na kwana da Amina a ranar girkinki, amma ita bata da lefi, Hauwa wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe kada ki kuskura na kara jin zagi a gidana, kin nuna mini rashin tarbiya da kuma rashin aiki da ilimi.
Ni ba namijin da mace take d'agawa hankali ba ne, ni na yi miki ba daidai ba, a wurina zaki nemi hakkinki, ita Amina ai bata da lefi.
Ta sake fusata tana cewa." Haka zaka ce ko?
Ni me yasa ba ka nemana a ranar girkinta duk da bata zuwa dakinka ai baka taba zuwar mini da bukata ba."
Ya ce." Ai shiyasa na ce miki a wajena za ki nemi hakkinki, domin itama dole na yi mata."
Ina tsaye ina jinsu duk abinda ta fad'a a kaina sai ya tare maganar yaki bari sunana ya fito.
Cikin raina na ce idan don na ji dad'i ne ban ji ba, domin kuwa wataran ni ma zai iya kware mini baya a gabanta, na bude d'akin ba fita na barsu suna ta turzawa, amma na yi mamakin sosai, domin ni a tunanina tunda ba na zuwa dakinsa ranar girkina ita da shi suna kwanciyar aure, ashe zargin hakan kawai nake, ashe shine dalilin da ya sanya jiya ya famshe kwanakinsa.
Yini na yi cikin zullumi da tunanin zai barni ko ba zai barni ba.
Har na yi shirin kwanciya sai gashi ya shigo shi ma da shirin kwanciyar na zuba masa ido har ya k'araso ya zauna a gefana, yadda nake kallonsa shima haka yake kallona.
Na daure na ce." Da ka sani ka ce na fito falo sai mu yi magana, kada ta zargi wani abu."
Ya ce." Ina jin tsoronta kenan?"
Girgiza kaina na yi a hankali na ce." Ba haka nake nufi ba, kai zaka nemi zaman lafiya a gidanka."
"Kada ku zauna lafiya don Allah kin ji ko."
Jan bakina na yi na shiru na rabu dashi abinda dai na kudire a raina shine idan za ta ce zata yi mini hayaniya ko ta zage ni kaniyarta zan ci, tunda ga wanda ya yi mata nan
Ya dube ni a tsanake kafin ya ce." Na kira Anti Yagana a waya kan maganarmu dake ta d'azu."
Yanayin yadda ya yi maganar ya sanya ni jin sanyi a cikin raina, har ga Allah ina jin dadin yadda yake mutunta anti Yagana har ya sakaya sunanta.
Na nutsu Ina kallonsa.
Ya cigaba da cewa." Na amince za ki je amma da sharad'in kwana uku kacal za ku tafi a jirgi ke da Yusi da Sukairaju nasa a yi muku shirin hakan, kada ki sa'ba umarnina."
Da sauri na ce." In sha Allahu na gode sosai Allah Ya kara girma." Ya amsa da "Amin." Kafin ya cigaba da cewa." Ni ma yana da kyau na bada gudumawa ko."
Murmushi na yi ban ce komai ba.
Ya ce." Nawa ki ke ganin zan basu."
Na dube shi sai na dan ji tausayinsa, shi dai abin sa bai rufe masa ido ba.
Na ce." Ko nawa ka basu sun gode."
Ya ce." Ai shawara na tambayeki sai ki ce mini ka basu abu kaza."
Na ce." Wallahi ban san abinda zan ce maka ba.
Shiru ya yi yana lalube a wayarsa.
Shigowar sa'ko na ji a wayata dake gefana na d'auka ina dubawa miliyan goma ne.
Na dube shi cikin mamaki mai tsanani.
A nutse ya ce." Ki cire miliyan biyar ki basu gudumawace ni dake.
Miliyan biyar din kuma kudin yaranki ne wanda na yi muku alkawarin satikan da suka wuce ba ke kadai na bawa kuna da yawa.
Na ce." To ai ni ban ce ina neman hakki ba."
"Idan ba ki ce ba yaran fa?" Ya fad'a yana kallona.
Na ce." Ni dai gaskiya dawo maka dasu zan yi wallahi.
Ya mike yana fad'in." Ki dawo mini dasu sai ki ga 'bacin rai, ki ajiyewa yaran zasu amfana anan gaba in sha Allahu, kuma koda jita jita zata sake tashi a gari ba zasu zarge ni ba.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
https://chat.whatsapp.com/K944WIHnBaKHDrZS6snUky
*TALLAH!*
*Albishirinku mata
walisa matan da suka amsa sunansu mata, wa
anda suka san sirri da fa'idar gyaran jiki domin ta da koma
ar sha'awarsu.