← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 276

Sashe 14

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ba za ki yi don Allah ba ki yanke adadin kudi ko kadarar da kike buk'ata daga wurina ni zan mallaka miki."
Hanci na ja tare da cewa ." Ni bana buk'atar dukiyarka kawai Ina tsoron yarana su zama marayu gaba da baya.

Na yi bincike sosai a kanka an ce aljanna ce ta aureka, kuma ba zata bari ka zauna da mace ba, shiyasa duk macen daka aura sai ta mutu.

Bayan haka kuma ni babu tsarin auran namiji d'an duniya a rayuwata."
Cikin b'acin rai ya ce." To ni kuma muddin mahaifiyata tana raye a duniyar nan ba zan yi jayayya da ita ba.

Ni kaina ba sonki nake yi ba, saboda ni mutum ne mai tsantsami.

Kin yi tarayya da maza biyu har kin haihu kafin ni.

Mai zai sanya na takale ki kai tsaye na gaya miki babu wata mu'amular aure da zata ratsa tsakaninmu.

Mutuwa kuma ko kin aure ni ko ba ki aure ni ba za ki mutu.

Wannan itace maganata dake ta karshe.

Zan kuma kira mahaifinki na sanar da shi, duk da shi d'in ma na lura kin fi 'karfinsa.

Amma dai shine ya haifeku wata'kila zai iya gaya miki ki ji.

Idan na zo ba na son bata lokaci ki zauna cikin shiri."
bai jira na ce wani abuba ya kashe wayarsa....
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim Opey bank
"Ta ce addu'a kam koyaushe cikin yin ta nake babu dare babu rana, duk wani abu na gaya maka akan yarinyar nan a daran jiya ba wayo da dubararka ba ne Allah ne ya baka ita, amana ce a wurinka.

Ka kula da ita da kyau ko bayan raina ban yarda ka munana mata ba.

Wannan shine adduata a gareka Allah Ya yi wa auranku albarka.

Ya amsa da "Amin Amin." Ni kam kasa daurewa na yi dalilin abubuwan da suka cunkushe mini a kirji.

Ita wannan matar ban santa ba, wata mu'amula bata ta'ba hadani da ita ba amma tana jifana da mugawayen kalamai.

Na rarrafa har kusa da ita na kama hannunta hawaye na kasa tsere a kumatuna na ce.

"Hajja ban san da irin kalamin da zan yi godiya a gare ki ba.

Hakika kin nuna mini k'auna ba tare da kin san asali da nasabata ba.

Kin so ni a lokacin da dama jama'a ke munana zato a kaina.

Hakika Ina yaba kyautayi da kawaici da k'aunar da kike nuna mini.

Wannan shine ya tilasta mini kar'bar muradinki ba tare dana shirya yin hakan ba.

Yadda ki ka zame mini uwa haka za ki same ni mai biyayya ga umarnin ki Hajja ni 'yar halak ce, kuma ina girmama duk wanda ya kaunace ni tsakani da Allah.

In sha Allah zan yi kokarin ganin na yi wa umarninki biyayya, na gode sosai da wannan karamcin naki."
Ta ri'ke hannuna katamau! tana kuka take ce wa." Ni ma ai kin taimake ni Amina, ina ga da ba dan ke ba wata'kila da tattake ni za a yi a wurin nan, ke kika fito da ni har na shaki iska.

Sannan na ji ro'ko da magiyar da kike wa Allah akan bukatunki.

A lokacin Ubangiji ya kimsa mini kasancewarki mata ga Tajo zai zama alheri.

Na san an fi karfin ki ne, amma ki kyautata ha'kuri in sha Allah nan gaba kad'an za ki yi farinciki Ubangiji Allah Ya yi muku albarka.

Kuma kamar yadda na fad'a miki zan dinga kawo miki ziyara sa'i da lokaci, Allah Ya ba ku zuria masu albarka."
Ban iya amsawa ba sakamakon kukan da ya ci karfina.

Na yunkura na tashi da kyar Hajiya Saratu ta kama hannuna muka kama hanyar fita dama shi Yallabai tuntuni ya fice shi da Yusi.

Koda na shiga motar ban iya dubansa ba. yana zaune Yusi a kusa dashi ya bashi wayarsa yana dannawa.

Sai ya zamana mun sa yaron a tsakiya.

Hajiya ta Saratu ya zagaya gefan da yake zaune suna magana.

Ban ji abinda suke cewa ba saboda ba na cikin nutsuwata.

Sai bayan da motar ta tashi tukkuna ta zagayo tana fad'in Amina a sauka lafiya sai mun zo in sha Allahu.

Na daure a hankali na ce." In sha Allahu na gode Mamana.

Sai da muka hau titi sosai na juya a hankali na dubi Yusi da yake ta fama yi masa jagwalgwalo a waya na mika hannu na kar'ba ba tare dana dube shi ba na mik'a masa..." Ka kar'bi wayarka kada ya shigar maka wani wurin."
"Ni na bashi ai." Ya fad'a a takaice! ban ce komai ba, na ajiye wayar saman cinyata.

Na juyar da kaina gefe.

Yaron ya zuro hannu zai d'auka na juyo da sauri tare da buge hannunsa.

Da ido na gargade shi.

Lokaci guda ya shiga hankalinsa.

Ya dube ni a tsanake yana cewa." Wayar nan tawa ce ai, kuma ni na bashi ina ruwanki idan ya lalata humm?

Na lura kina da saurin hannu, da hantara yaro ba abinda ya yi miki kin buge shi, ba ni wayata."
Na mi'ka masa abarsa kamar yadda ya buk'ata.

Sai ya kara mikawa yaron.

Shi kuma ya'ki kar'ba yana satar kallona.

Ya dube ni ransa a 'bace." Kin nuna masa akwai wata manufa ko?"
Kallonsa na yi da sauri domin ban yi tsammanin fassarar da zai yi mini kenan ba.

Ni na yi hakan ne a ko'karin cigaba da kula da tarbiyar yarona.

Don ba zan yi sakaci ta samu tangarda ba dalilin na lura shi din kamar ba mai tsawatarwa ba ne.....

Jikina ya mutu sosai ganin yadda ransa ya 'baci, amma kuma girman kaina ya hana na bashi ha'kuri ko na nuna masa nufina ba haka ba ne.

Kafin mu isa filin jirgin yana ta amsa waya tunda na lura wayoyin nasa kusan uku ne manya biyu da karama daya kuma wadda ya bawa Yusin itace bata da wani amfanin sauran.

Har muka isa Legos babu wata muhimmiyar magana a tsakaninmu.

Yusi tuni ya langabe a jikina bacci yake sosai.

Muna sauka escort dinshi suka tare mu su uku ne, daya ya d'auki Yusi yasa a kafada sauran kuma suka d'ibi kayanmu zuwa mota.

Na 'dan jima ni kadai a mota kafin ya shigo.

Domin muna sauka daga jirgi jama'a suka fara taruwa domin gaisawa dashi.

Na dinga hangen yadda yake sakewa da mutane da wasa da dariya har da tafawa idan ta kama.

Nan na sake fahimtar cewa shi din mutum ne mai sau'kin sha'ani.

Kuma dukiyarsa ba ta sanya masa girman kai da d'agawa ba.

Yana rayuwarsa ne daidai da kowa.

Ba zan iya fasalta muku haduwar gidanshi ba.

Na san dai ni kaina Allah ya gama yi mini gamnakatar na jin dad'in duniya muddin na samu kwanciyar hankali a cikin wannan gidan Allah ya sallame ni anan duniya sai dai na nemi lahirata.

Wallahi tallahi a mafarki ban ta'ba tunanin yin irin wannan auren ba balle na hasaso mini shiga irin wad'annan gidajen da muke ganinsu a kasashen waje.

Sai dai Allah yana zartar da buwayarsa ne a duk lokacin da ya ga dama.

Gidan cike da ma'aikata kowa kuma da aikinsa.

Tun a haraba suke ta zuwa gaisuwa sai da muka shiga ciki tukkuna sannan na dan samu nutsuwa.

Na yi kokarin daidaita nutsuwata domin ina tsoron ya fahimci rud'un dana shiga.

Na nemi kujera na zauna kafafuna na dan karkarwa.
Chapter 14 · 0% Book details