Sashe 121
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ka cigaba da yi masa magana kada ka biye masa ni kuma zan yi magana da Baban nasan dai haka kawai ai ba zaka kirkiri karya don jin dadi ka gaya mini ba ko?''
"Wallahi Mama babu karya cikin maganata gaskiyar abinda yake faruwa na gaya miki, menene ribata idan na yi k'aryar kuma me ya yi mini da zan 'bata shi."
Na ce." To kada nunawa Momi damuwarka a fuska ka daure ka ji ko."
Ya ce." In sha Allah Mama.
Daga haka sai muka bar maganar muka shiga wata ina d'an jansa da wasa duk domin ganin ya manta abinda yake damunsa.
Amma zahiri ni a can 'kasan zuciyata cike nake da fargabar yadda zan tunkari maigidan da maganar.
Wala'ala ya fahimceni, wala'ala kuma ya juya mini manufa, amma dai tun yanzu ya kamata a ce ayi wa tufkar hanci kafin lamarin ya yi tsamari rayuka su zo suna 'baci.
Daf da magriba ya tashi ya fita da zummar shirin shiga massalaci.
Bayan kwana biyu ina cikin nazari domin har yanzu na kasa tsayar da abinda nake ganin shine daidai.
Ba na so na yi magana ne a ce na goyi da bayan yarona wata'kila shi kansa zai iya ganin haka shiyasa hankalina bai kwanta ba har yanzu sai dai na gaza daurewa na sanar da Baba Tabawa abinda yake faruwa domin kuwa macace mai tsinkaye da nisan tunani.
Ta jima tana jimantawa kafin ta ce." Ai shurun ba shine mafita ba, gwara ki gaya masa tunda shine jagoran kowa a gidan ya yi wa tufkar hanci kada lamari ya yi k'wari hatsaniya ta tashi ya ce mai yasa ba a gaya masa ba.
Ina ganin duk wanda zai ce kin so kanki da zummar kawo gyara to ya zalinceki domin kuwa abinda ki ka yi shine daidai, ai ba ki za'bi Kamalu kin fifita akan Salim ba, duka naki ne kamar yadda itama Momin take nunawa, to ya kamata a ce wannan 'barakar da take ko'karin kunnowa an yi maganinta.
Ajiyar zuciya na sauke bayan duk na gama sauraran maganganunta.
Na ce." Shikkenan Baba, in sha Allah zan sanar da shi halin da ake ciki duk kuma yadda muka yi aki ji."
Ta ce." To shikkenan, Allah Ya maganta."
To daddare ina d'aki a kwance misalin takwas da rabi ya shigo mini cikin tsananin b'acin rai.
Na tashi zaune da sauri gabana na fad'uwa.
Ya zauna samar kujerar madubi na ce." Kai lafiya Kamalu."
"Mama barka da dare." Da abinda ya fara kenan.
Na amsa a takaice na ce." Menene?"
Duk dauriyarsa sai da muryarsa ta yi rawa ya ce." Mama ba zan iya ba, ba zan iya jurewa ba, zan tafi kano gobe domin kuwa Salim baya neman zaman lafiya da ni."
"Mai ya yi maka kuma?" Na tambayeshi jikina sanyi kalau domin kuwa wani yanayi na shiga na tsananin tausayin yaron ba komai ne ya janyo masa hakan ba sai maraici da rashi domin kuwa duk abinda Salim yake yi yana yi ne domin ya ga a cikin rigar arziki su yake.
"Salim tare da abokansa suke yi mini dariya har na ji daya daga cikinsu yana kirana da 'kolo, dayan kuma yana cewa mini criminal." Sai hawaye suka fara kasa tsare a kumatunansa.....
Chapter 29 Bata kai kalma 2k yanzu na cika she muku a wannan chapter din.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*81*
Zuba masa ido na yi ina kallo a yayin da hawayen ke ta zarya a dakalin fuskarsa bai goge ba, ni ma kuma ban ce masa ya yi shiru ba sanin da na yi cewar kukan shine zai sassauta masa takaicin abinda aka yi masa.
Lallai gagarimin abu ne ke sanya fitar hawaye a idon Kamalu tun yana yaronsa balle yanzu da shekarun samartaka suka fara kama shi dole an yi gwagwarmayar rayuwa a samu zuciya ta sake 'ke'kashewa.
Idan an kira shi da 'kolo (almajiri) ai ba damuwa ba ne, ni na ji dad'i ma da ya zama 'kolon mahaddaci kuma marubucin al'kur'ani.
Kalmar criminal din ce ta hargitsa dukkanin lissafina, Salim abin har ya kai haka.
Abinda ya faru shekaru kusan shida zuwa bakwai yaro ya samu nutsuwa ya zama mutum shine yanzu za a taya
r masa da hankali.
Cikin jan ajiyar zuciya ya ce." Mama Salim na b'akinciki da yadda Allah ya yi mini jama'a a area nan, sannan yana kishi sosai ya ga na bude massalaci manya mutane na bina sallah suna gaisawa da ni.
Wannan na ji da kunnena yana fad'in duk wanda ya bi b'arawo sallah shi ma bashi da maraba da 'barawo, kuma sannan bashi da sallah.
Mama yaushe wannan sunan zai goge a tarihin rayuwata"
Na ji kwalla ta ciko mini ido.
Na daure ban yadda ta zuba ba, na ce." To share hawayenka ka daina kuka ka ajiye abinda yake faruwa a matsayin cigaba, domin kuwa haka siddin ba zaka cimma wata nasara ba tare da kalubale ba.
Ita hassadar ai itace matakin komai.
Kada ma ka damu, kuma ina mai tabbatar maka da cewa watarana Salim zai bi ka salla, zai kuma nemi fatawa a wurinka, wannan ni ce na gaya maka, domin kuwa ina nan ina roka maka d'aukaka da shura ta fanninin addini anan gidan duniya, Kamalu idan Allah Ya yarda duniya da mutanan dake cikinta za su amfana da kai."
Hannu yasa ya goge hawayen dake zuba a kumatunsa.
Na ce." Ka kyale mini komai a hannuna, ka ji ko ka cigaba da hakuri, ni kaina a wannan ga'bar ba zan ha'kura ba dole a yi wani abu kai, amma kada ka nunawa Momi komai, ka bar abin a zuciyarka."
A sanyaye ya ce." Shikkenan Mama, zan yi yadda ki ka ce din, amma ni ina so na koma can kano zan fi samu nutsuwa cigaba da gudanar da neman ilimina."
Na ce." Idan har hakan shine alheri za ka koma Kamalu, ka cigaba da addu'a ka kuma bar maganar tsakanina da kai."
To a daran na nemi maigidan a waya duk da nasan ba sosai yake amsa waya da daddare ba amma yadda nake jin zuciyata ba zan iya bari sai gari ya waye ba.
Wayar ta katse bai daga ba sai na yi masa text na cewa ina son magana dashi a duk lokacin da ya ga sakona.
Wajan goma da rabi kuwa ya kira ni da kansa.
Na daga muka gaisa a nutse.
Na ce." Baba ina son magana da kai amma kada ka fahimce ni girman Allah da Annabi ka dubeta ta fuskar hankali da maslaha."
A nutse ya ce." To ina jinki ai ni mai hankali ne ba mahaukaci ba, kada dai ki ce mini kin yi 'bari domin kwana biyun nan mafarkai nake yi marasa kan gado, Ina ganin ma farkon watan nan za mu zo."
Na ce." Ban yi 'bari ba, amma ka sani cewa ni da kai ba mu da ikon komai akan abinda Allah Ya zartar.
Idan har kaddara ta gifta cikin ya samu matsala ba za ka d'auki kaddara ba kenan?"
Ya ce." Zan d'auka mana, ai mafarkan da nake yi ne ya sanya ki ka ji na yi miki wannan maganar.
Na tuba ga Allah duk yadda ya yi daidai ne."
Shiru na yi ina sauraransa har ya gama maganganunsa.
Na ce dalili ne mai karfi ya sanya ni kiranka a daran nan, kuma ni kaina zan ji dadin zuwanka domin ka gyara abinda yake faruwa Kamalu ne da Salim.......
Duk abinda yake faruwa na zayyane masa.
Ya jima yana nanata maganar da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Yaushe Salim ya lalace haka, kuma abu ya faru tunda kuruciya saboda rashin hankali ka tara abokai kana gaya musu criminal?" Ya sake maimaita kalmar tabbacin hakan ya bashi tsoro da mamaki.
Na ce." Kamalu ya ce zai koma kano da zama can wurin Hamusu."
Gyaran murya ya yi tare da cewa." Wannan kuma abinda yake cikin ranki ne shekara da shekaru shine ki ka samu mafaka dalilin wannan matsalar.
Na gaya miki Amina idan har Kamalu zamansa zai koma kano to Yusi ma zai bi shi.
Nusaiba da Salim Adam amana ne a hannuna.
Haka zalika tunda ina auranki yaranki ma amana ne a hannuna koda ubansu yana raye to balle kuma baya raye.
Idan har kina ganin za ki yi iko da abinki ni ban iya ba sai na ce Allah Ya taimaka."
Na ce." To yanzu ya kake so a yi?
Kasan dai cigaba da zaman Kamalu a gidan Momi akwai matsala watarana za su iya yin abinda bai da ce ba."
"Babu abinda zai faru, ki kyaleni da yaran dukkaninsu tunda kin gaya mini kin gama aikinki."
Jiki babu karsashi na ce." Shikkenan sai da safe." Sai kawai na kashe wayar domin kuwa jikina yana ba ni kamar ba zai d'auki tsatstsauran mataki ba.
Da lamarin na kwana na kuma wayi gari dashi dalilin da sanya kenan na kasa barin abin iyakacinmu.
Na kira anti Yagana na gaya mata halin da ake ciki.
Sosai kuwa ranta ya 'baci ta dinga fad'a tana cewa babu lallai babu dole muddin da cin zarafi da cin mutuncin da kuma tozarci Kamalu dole ya bar gidan.
Arziki ai ba hauka ba ne.
Na ce." Anti Yagana tun farko fa ni dama abinda na guda kenan, shiyasa da matar nan ta bukaci zaman Kamalu a wurinta na dinga gocewa.
Karin abin kuma maigidan ya'ki ya fahimceni, wai muddin Kamalu zai bar gidan sai dai su tafi da Yusi wanda na tabbatar da cewar hakan matsala ce babba.
Da ya zauna mun yi magana da fahimta tuntuni da tun farko wannan matsalar bata kunno kai ba.