← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 233 OF 276

Sashe 233

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa ce masa komai na yi na kama hanyar d'akina yaran suka nufi wajen da yake zaune babu wani kuzarin kirki a tattare da su gabad'aya.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*156*
Cikin nauyin jiki na cire hijab din jikina na zauna gefan gado har yanzu zuciyata bata samu nutsuwa ba dalili nasan lallai ne akwai abinda zai biyo bayan abinda ya faru.

Zamana da minti goma ya shigo shi kadai d'akin.

Muka dubi juna kafin ya furta." Da gaske ne abinda yaran nan suka fad'i."
Na gyad'a kaina tare da cewa." E, da gaske ne." Domin fad'in gaskiya shine abinda ya kamace ni." Ya yi shiru yana yi mini wani irin kallo na cigaba da cewa suna tare duk a wuri d'aya ta zame ta fita ba tare da kowa ya ankara ba.''
Ya tare ni da sauri ta hanyar fad'in." Ke kina ina har hakan ta faru?" Na ce." Ina d'aki a zaune tare da matan gidan su kuma suna tsakargida suna wasa."
Ya ce." Babu wani abu anan face sakaci da rashin kula Amina me yasa kin san cewa ba su ta'ba zuwa waje ba ki yi nesa da su.

Har sai da ta 'bace ta yi nisa tukkuna duka za ku ankara da cewa ba ta gidan saboda kun shagalta gabad'aya."
Na danne haushin da ya ba ni na ce." Duk yanayin kular da zan yi a kansu idan Allah ya aiko tsautsayi babu yadda za mu yi kuma kada ka ga lefina fa yarinyar nan ban yi niyyar zuwa ko'ina da ita ba ka d'aukota ka kawo mini cikin mota.

Me yasa don tsautsayi ya faru a kanta a ce ba za a yi mini uzuri ba."
Ya fusata sosai yana fad'in." Ba ki yarda da cewar rashin kula ba ne kenan.

Ya za a yi ki je da yara wajan da ba su saba ba ki sake su ke kina wani waje a zaune kuma ki ce a yi miki uzuri akan wane dalili ke ba za ki yi lefi a nuna miki kuskuranki ba kenan."
Na ce." Ba zan fasa fad'in tsautsayi ne ba.

Kuma na iya kasancewa akan kowa amma abinda nake so na gaya maka akan yarinyar cewa tana da rawar kai fiye da 'yan uwanta me ya kai ta fita ta bar su tunda tare suke duka a zaune a waje daya suna wasa.

Lefin ai ba nawa ba ne gabad'aya."
Ya gyada kansa yana cewa." Tunda kin ce haka wallahi babu inda za ki kara zuwa da yaran nan."
Na tare shi da sauri ina fad'in." Aikuwa ba ka isa ba kaffara ta hau kan ka."
Bai ce komai ba ya juya ya fita cike da b'acin rai.

Na ja tsaki ni ma cikin b'acin ran na tashi domin cire kayan jikina sun yi mini nauyi yamma ta yi sosai don daf ake da kiran sallar magriba.

Na sanya doguwar riga cotton mara nauyi da hula na fito falon shiru ban ji motsinsu ba na yi tunanin ko suna sama tare da shi.

Kicin na shiga na dora farar taliya haka kawai nake sha'awar cin ta da manja da yaji da kifi.

Na kammala na fito still ban ji wani motsi ba d'akina na shiga na yi sallah ban sake fitowa falon ba sai da na yi Isha'i na fito babu motsinsu.

Kai tsaye saman na hau na bud'e d'akin nasa babu kowa shiru.

A lokacin ne na gazgata abinda zuciyata take raya mini ya kwashe yaran ya yi gaba da su kenan.

Ga abinci na dafa har da su.

Na dibi daidai yadda cikina zai d'auka na kira Ayuba na juye musu shi da masu gadi
Abincina na ci na k'oshi na samu yar nutsuwa na kira anti Yagana na gaya mata shawarwarin da na yanke ta sake
bada goyon bayanta sosai amma ba lallai ne ta samu damar zuwa bikin ba tunda tana tare da maijego ba ta yi arba'in ba.

Mun jima tare da Babanmu a waya muna magana har yana yi mini jajen 'batan Minal duk abinda na yanke na gaya masa ya yi ta sanya mini albarka har muryarsa tana rawa.

Bana tsammanin zan kira shi domin na tambayi dalili.

Mu tafi a haka kawai domin neman dalilin ma zai kara masa kwarin gwiwa ne.

Hamusu na wakilita kamar yadda na gayawa Babanmu a washe garin ranar aka fara aikin gidan domin sabunta wasu abubuwan.

Aikin gidan Usaini ma an cigaba da gyara bangaran amarya kamar yadda na yi masa alkawari duk dai a washe garin ranar da nake gidan namu.

Da yamma sai ga Fati ta zo mini da yaranta su biyar yadda na gan su a lalace ita da yaran gabad'aya sai da tsigar jikina ta tashi Fati mai garin jiki da san girma duk ta tsiyaye yaran babu suttura ta arziki duk sun kod'e sun d'angale yaduka masu arha wanda take goyo uku da wata riga irin ta gwanjo hannun da wuyan ya yi masa yawa da wando wanda aka rage gefansa da zare da allura.

Tana sauko shi daga bayanta zarni ya cika mini hanci domin dai ba ta sanya masa pampers ba ya kuma yi mata fitsari a jiki da zanin goyon gabad'aya.

Na zura mata musu ido jikina a sanyaye wai shin wace irin rayuwa muke ciki ne a yanzu ki ga mace da 'yan shakaru kad'an ta tsofe ta lalace saboda rashin kula da wahalar gidan aure.

Suka dinga bi daya bayan d'aya suna gaishe ni ina amsawa tausayinsu na tsirga mini wannan rayuwa Allah Ya saukaka mana ita sai na tuna lokacin da ubansu ya fito auran Fati Ummansu ta dinga murna tunda a lokacin yana tashen samun kudi sai dai babu arabi babu boko haka ta tsige mata makaranta duka ajinta biyu a sakandire ta ce karatun ai babu dole ta yi mata aure lokacin Babanmu sai yadda ta yi da shi.

Tana ta washe bakinta take cewa.

" Daga gidanmu nake Umma ta ce ai kin zo garin ga ma abin alherin da ya faru na ce bari na kawo miki yara ku gaisa."
Cike da kulawa na ce." Kin kyauta sosai Fati na ji dad'i kuma ina fatan duka kuna lafiya ." Na tambayeta hakan kamar yadda al'ada ta gada amma a zahiri ai duk wanda zai ga Fati ya san ba ta cikin nutsuwa.

Ta yi d'an murmushi tana fad'in." Lafiya lau anti Amina."
Na dafa kafadarta ina cewa." Ki gaya mini idan da wata matsalar Fati ba ki jin dadin auran nan ko."
Ta kuwa fashe da kuka har jikinta na rawa na rugumeta sosai a jikina idona ya ciko da ruwan hawaye yaran suka yi tsuru suna kallonmu na kyaleta ta ci kukanta ta k'oshi kafin ta dago ta goge fuskarta.

Na ce." Gaya mini ko da akwai taimakon da zan iya yi miki."
Ta ja hanci tana fad'in." Babansu ya karye a kasuwa tuntuni anti ga yara a tsakaninmu ba na ma tunanin rabuwa da shi tunda lokacin da yake da shi ya yi mini kuma idan na ce zan kashe auran ban san wanda zan aura anan gaba ba kuma zan yi ta tunanin yarana zuciyata ba zata nutsu ba.amma wallahi anti Amina yunwa tana damun mu ni da yara sannan sai matsalar gidan haya wani abokinsa ya bashi shawara ya sayar da gidansa suka saro kaya karshe kudi ya narke masa duka suka lalace Bai tsira da komai ba. muna gidan haya muna shan tsangwama da gori.

Anti Amina ba zan rufe miki ba yunwa ta assasawa Faruku d'auke-d'auke tun bai kai shakarun haka ba ko idan ma'kota sun aike shi ya rage kud'i ya boye.

Ba ki ga yaran da yake bi ba yanzu sai na kwana uku biyar har sati ban sanya shi a idona ba.

Har shaye-shaye yake yi fa anti Amina."
Ta rushe da kuka tana riruke hannuna.

Faruku shine babban yaronta ya zama saurayi yanzu domin ya girmi ma Kamalu tunda duka sun riga ni aure da haihuwa haihuwarta bakwai da biyar ta zo mini.

Na zura mata ido ina tuna abubuwan da suka shud'e a shakarun baya.

Lallai Fati tana cikin jarrabawa.

Ban yarda na yi magana ba sai da na daidaita kaina tukkuna na mayar da hawayen da ya ciko mini a kwarmin ido domin kara mata kwarin gwiwa na fara yi mata misali a kaina da sake jadadda mata cewa babu abinda bashi da karshe kuma dukkan tsanani yana tare da sauki.

Yanzu dai babban tashin hankali matsalar yunwa domin itace musabbabin dole kuma a magance ta idan ba haka ba d'aya bayan d'aya yaran za su d'auki hanyar da yayansu ya d'auka
Duk matsaltsalunta da ta gaya mini na gazgata domin ita dama halinta daban da na Hadiza sannan ba kasafai take biyewa Ummansu idan tana wani abin ba abinda dai ta dinga yi mini a lokacin kuruciya na rashin kunya wannan dama d'abia ce ta yaran da suke da uwa a gida mussaman idan an nuna musu su kad'ai ne 'ya'ya masu 'yanci ba kuma su samu tarbiya ba ko a wancan lokacin dama ni su Hassana ne da Usaina ne mutane na mun fi shiri da su haka duka muka dinga rayuwar a gidan to yanzu ga yadda rayuwa ta juyawa kowa.

A dai yadda take a yanzu ko bata bud'e baki ta fad'i damuwarta ba duk mai hankali zai gane cewa tana buk'atar taimako kuma ni ta burge ni sosai da ba ta yi tunanin watsar da yaranta ba.

Ta yi hankali sosai saboda idan ta fito shi kansa zawarcin wata babbar jarabawa ce sannan wanene zai kula mata da wannan yaran.

Na ba su abinci suka ci suka koshi ina sake kwantar mata da hankali da bata tabbacin zan yi mata iyakacin bakin kokarina idan har ta yanke shawarar sana'ar da za ta yi zan taimaka mata da jari.

Da za ta tafi na bata dubu goma sannan na sanya Ayuba ya d'auketa a mota domin ya kaita gidanta na kuma tabbatar mata cewa idan hidimar bikin nan da za mu ta kammala zan yi mata Aiken kayan abinci.
Chapter 233 · 0% Book details