← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 276

Sashe 8

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan shekaru hud'u da rasuwar Samira bai kara sha'awar yin wani auran ba, ya cigaba da bunkusa kasuwancinsa duniya na kara suturtashi da taguwar arziki Allah kuma yana kara sahale masa.

Hajja ta zaunar dashi kan batun iyali dalili girma ya fara cimmasa shekara arba'in da hud'u ya kamata ace ya tara yara a halin yanzu.

Bai yi jayayya da umarninta ba yace ta nemo masa yarinya mai nagarta sai ayi auran.

Haka kuwa akayi Hajja ta sake binkito masa a dangi amma wannan karon family din Babansu ne Alhaji Ibrahimu.

Ayusha yar yayan mahafinsa ce kusan ma itace yar autar gidansu a mata.

Ya amince duk da bata kwanta masa a rai ba, zai yi ne domin farincikin ta.

Aka gudanar da komai baya kasar yana can India harkokin kasuwancinsa.

Amarya ta tare a dankareran gidanta ba ango.

Kwana goma da d'aurin auran ya dawo.

Wata ijaba da hukunci na Allah dawowarsa da kwana daya don ba wani Abu da ya shiga tsakaninsu dalilin gajiyar da ya kwaso bai tunkareta da wata buk'ata ba.

Ayusha ta tashi da matsanancin zazzabi wanda ya dinga sumar da ita tana farfadowa.

Babu jinkiri bare bata lokaci aka nufi babban asibiti da ita.

Ashe tana da zazzabi typhoid dama yakan tayar mata sa'i da lokaci sai dai wannan karon ya zo da 'karar kwana satinta daya a asibiti rai yayi halinsa.

Babu wanda bai tsorata da wanna lamari ba.

Kafin kice kwabo kowa ya fara juya al'amarin ana dangatashi da makaru
ko dai shafar aljanu da sauransu.

Da yake ya riga ya yi suna a duniya duk yadda akayi ga boye sha'aninsa baya boyuwa sai duniya ta ji.

Nan take jaridu da kafafan sadarwa suka samu abin yi.

Kowace majiya da irin 'karyar da zata girba.

Akwai masu cewa ma aljanar da ta aure shi ta gindaya masa sharad'in bashi ba aure.

Wasu kuma suna cewa asharadin dukiya da shahararsa babu aure.

Shiyasa duk matar da ya aura zata mutu.

Zantuka masu kyau da muni suka dinga dawowa kunnansa.

Uffan bai ta'ba cewa ba, har kura ta lafa jama'a suka mance da al'amarin, don ma a lokacin harkokin media basu yi karfi ba wata'kila da har yanzu maganar Bata mutu ba.

Hajja ta ki hakura duk da shi din ya sare da lamarin auran.

Ta samu inna Uwani kanwarta ce uwarsu daya ubansu kuma itace mahaifiyar Samira ta je mata da buk'atar a yi masa madadi da Hauwa kanwar Samira ce don itace ma take bin ta a shekaru.

Inna Uwani ta dinga zille-zille tana kaucewa, yau ta ce wannan gobe ta ce wancan.

Duk lokacin da Hajja za ta tuntubeta da maganar sai ta kawo uzuri.

Daga karshe ma sai ta dinga Jin wasu zantuka na tashi a cikin dangi inna Uwani da ita Hauwan suna fad'in haka kawai suna ganin kashi da rana ba za su taka ba.

Tunda sun rasa Samira sun bar wa Allah, amma ba zai yiwu ba sai dai ya je can wani wuri ya nema.

Hajja ranta ya yi mummunan baci har sai da ta zubar da hawaye akan kyamar da 'yar uwarta ta nunawa jininta.

Daga karshe sai kawai ta ha'kura ta barwa Allah sai dai koyaushe cikin tsananta addu'a take yi a kansa akan Allah Ya magance masa matsalarsa.

Shi ma tun daga lokacin sha'awar aure ta fice masa daga rai domin shima ya tsorata ainun har ya fara zargin kansa yana hasashen kada dai maganar da jama'a suke yi ta zama gaskiya.

Dalilin ciwon mahaifiyarsa kenan Hajja hawan jini mai k'arfi ya kamata.

Ashe da sugar a kwance sai shima ya tashi duk a lokacin aka dinga dau'ki ba dadi da ita ana neman rai 'kasa-'kasa har dai Allah Ya sassauta mata aka dawo da ita.

Sai dai sa'i da lokaci ciwon yana tashi mussaman idan ta shiga yanayi na b'acin rai da fargaba.

Amma da yake macace mai tawakkali bata ta'ba gazgata maganar mutane akan yaronta ba.

Ta amince Allah ne yake saukar da ikonsa a kansa, kuma duk wanda ya mutu lokacinsa ne yayi har yanzu bata yarda yaronta yana tare da makaru ko wata aljana ba.

Allah ne me yi kuma shi ta mikawa lamarin gabakidaya.

Wannan dalilin ne ya sanya take yawan zuwa kasa mai tsarki domin ta yi masa addu'a akan Allah ya kawo karshen matsalarsa.

Girma da manyan shekaru sun hau kanta tana so kafin rayuwarta ta kare taga yaransa.

Ganin Amina na ro'kon Allah akan miji nagari a take ta ji a ranta Allah ya kar'bi adduarsu bakidaya dalilin da ya sanya kenan ba ta yi shiru ba ta nemi alfarmar yarinyar wanda ta hangi dacewar auran nasu da samun albarka mai tarin yawa.

Wannan kenan...

Wani irin numfashi take fesarwa idanuwanta a rufe jikinta gabad'aya ya saki.

Gabad'ayanmu muka gigice!

Mussaman shi uban gayyar ya tararrayota jikinsa ya rungume yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ni kam Ina daga zaune amma kafafuwana sai karkarwa suke yi.

Sai na nemi kukan da nake yi na rasa tsabar tashin hankali da d'imuwa.

Ban san lokacin dana je na rungume kanta a kirjina ba ashe na hada da hannunsa.

Ya cire da saurin gaske.

Ya tashi da sauri d'akin da ya fito ya shiga Hajiya saratu ta zauna a wurin da ya tashi tana share hawaye.

Ganin yadda na d'uka kanta ina yi mata addu'a sai itama ta fara yi.

Tana tofa mata kamar yadda nake yi.

Hannuna a saman kirjinta ina dan shafawa a hankali a hankali numfashinta ya daidaita.

Jikin nata kuma ya daina karkarwa.

Babanmu na gefena a tsaye ya rasa yadda zai yi in banda kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un babu abinda yake yi.

Ya fito yana waya da harshen larabci kimanin minti uku ya gama wayar ya je kusa da 'yar'uwarsa ya tsaya ita dashi duk suka ba ni tausayi ganin yadda suka d'imauce.

Falon ya yi tsit! kowa da irin abinda yake sa'kawa a zuciyarsa.

Wannan littafin dai na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina na, duk kankantar hakki sunansa hakki mu kula sosai!

Kai na shiga rud'u ba k'arami ba.

Ni tsorona Allah da Annabi kada ta mutu na zama ina da hannu a ciki.

Har likitan ya zo ya gama abinda zai yi bana cikin hankalina.

Na dai tsinci kad'an daga cikin bayanin da yake yi akan tashin ciwon wani labari taji ya firgitata ko dai taga wani tashin hankalin har jinita ya haura ka'ida dole a kiyaye."
Baba ya ce ba zamu tafi ba har sai ta tashi daga bacci ya tabbatar mata da cewa aure kamar an yi shi an gama.

Ni ma ban bada goyan bayan tafiyar ba dalili na san hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba in ba gani nayi ta tashi ba.

Anan muka kwana sai gefin asuba tukkuna ta motsa.

Da yake ina kusa da ita da sauri na ri'ke hannunta ta fara yun'kurin tashi zaune Hajiya Saratu ta zo ta taimaka mini muka tayar da ita.

Ta zuba mini ido tana kallo.

Sai na rike hannunta da kyau na ce." Sannu Hajja ya jikin naki?"
Muryata rad'au ta furta." Na ji sauki ina Tajo?"
Da sauri na daga kaina yana can saman wani gado a kwance wata'kila bacci ne ya shammace shi.

Hajiya saratu ta ce ." Gashi can a kwance wata'kila bacci ne ya d'auke shi."
Sai ta girgiza kanta kawai ta tashi tana fad'in." Sallah zan yi." Muka kamata muka kaita bandaki ta kama ruwa ta dauro alwala.

Jikinta yayi kwari sosai a tsaye tayi sallarta cikin nutsuwa.

Hankalina ya kwanta sosai ganin yadda Allah ya rufa asiri ciwon bai tsananta ba.

Bayan duk mun gabatar da salla an gaisa da juna.

Babanmu ya dubeta yana fad'in." Hajiya maganar nan tana nan in sha Allahu za a daura auran Alhaji Tajo da Amina muddin Hakan shine kwanciyar hankalinki.

Yau Juma'a kamar yadda kika buk'ata sai a nemi albarkar ranar.

Duka ni da ita mun mikawa Allah lamarin shine yake da iko damu bakidaya."
"Ta d'an dube ni a hankali kafin ta ce." Amina na janye maganata, ba zan sanya ki kiyi abinda ranki baya so ba.

Kamar yadda ki ka fad'a kina da za'bi a rayuwarki.

Allah Ya za'ba muku abinda yafi alheri gabad'aya.

Za mu cigaba da zumunci daku in sha Allahu rabbi."
A lokacin da ta fad'i maganar rasa abin yi nayi duk sai na diririce!

Magana nake so na yi amma bakina ya yi nauyi.

Ban ta'ba ganin tsananin fushin Babanmu ba sai a lokacin.

Ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. yana cewa shi ya haife ni ba zai yi mini baki ba, ammafa da wahala na samu miji kamar wannan.

Hawaye masu zafi suka dinga gudana a kumatuna.

Duk yadda na so na fahimtar dashi halin da ake ciki ba zai gane ba, idonsa ya riga ya rufe da cewa babban mutum zai auri jininsa.

Babanmu a sanin da nayi masa bashi da kwadayin abin duniya amma yanzu tashi guda ya aminta da auran mutumin da bai tsananta bincike akan halayensa ba.

Kuka nake sosai na gaza cewa komai Ina dai jin hajjan tana ce masa ya bar maganar haka ai don ba a yi auran ba zumunci ba zai yanke ba.

Da kyar na furta." Hajja ku gafarce ni, akwai 'kudurori da manufofi da uzurirrikana da nake so na cika a rayuwata shine dalilin da ya sanya na k'yamaci aure a yanzu.

Ba wai ina 'kin jininki ba ne.

Ni ya kamata ku k'yamata amma baku yi ba, wallahi na amince ayi auran nan saboda farincikinki.

Yadda lokaci daya kika nuna mini k'auna ni kaina na san idan na nuna 'kyama ga alherin da kike nufina dashi ban yi miki adalci ba.

Na yarda na amince Koda hakan zai zama karshen numfashina kenan." Na rushe da wani irin kuka mai karfi.

Sai ta kamo ni ta rungume tsam a jikinta tana kuka take fad'in." In sha Allahu zaku zauna lafiya da juna kuma za a samu zuria mai albarka na gode sosai da wannan karamcin da kika yi mini Allah Ya yi niki albarka.

Na gode, na gode na gode sosai."
Abin mamaki da al'ajabi.
Chapter 8 · 0% Book details