← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 276

Sashe 88

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka had'a baki da ita Hajiya Alili suka saci wani almajiri suka mika shi ga kungiyar kamar yadda suka buk'ata da da farko cewa suka yi da ita sai ta bada d'anta na cikinta ta ce musu ai bata taba haihuwa ba shine suka buk'ace ta cikin kwanaki biyu kacal ta kawo musu matashin yaro wanda bai balaga ba.

Matsanancin tashin hankali muka shiga gabad'ayanmu domin lamarin da ya faru sai yake nema ya shafi zuri'armu gabad'aya mutane suna ta ririta maganar tare da 'kir'kiro k'arya da gaskiya har da masu cewa dama sun jima suna zargin alhalinmu ko maita ko karuwanci ashe 'yan mafiya ne, wasu kuma na cewa gidan namu dama ai ya yi 'kaurin suna yara tun suna k'ananu suke sace sace......

Mun shiga book3 anan har mun yi rabi fa, ina ga ya kamata ku shi mini albarka don ban ta'ba kawo muku wani uzuri ba kullum sau biyu kuke samun update sannu sannu bata hana zuwa
Na gode muku sosai.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*60*
Hadiza ta zama kamar zautacciya domin kuwa ita da mahaukaciya marabarsu kalilan ne zafin addu'a da irin saukar karatun al'kur'ani da ake yi akan 'batan yaron ya sanya da bakinta ta fad'i ta yi kisan kai domin kuwa yaron tuntuni an shanye jininsa hakkin rai da rashin sabo ya sanya nutsuwa ta yi kaura daga jikinta.

Yadda bincike ya nuna ita Hajiya Alili tunda ta ji maganar ta fasu a gari ta yi 'batan dabo aka nemata a ka rasa a garin.

'Yan unguwa suka cinnawa gidanta wuta ita kuma Hadiza muna ji muna gani mota guda da 'yansanda suka tafi da ita.

Tashin hankalin da ya assasawa Babanmu fad'uwa kenan ranga ranga rai a hannun Allah muka kai shi asibitin nuna koke-koke don wallahi ni tsananin damuwa da fargaba ya sanya na manta halin da nake ciki duk wasu lalure laluran da nake yi a tsaitsaye nemansu na yi na rasa saboda tsananin tashin hankali da fargaba don sai na ce na jima ban ga abinda ya daga mini hankali kamar wannan lamari ba.

Da yake tunda ta bar gidana ban sake ganinta ba sai da wannan abin ya faru gabad'aya kammaninta sun canza ta zama kamar wata tsohuwar kilaki hujin hanci biyu kowanne da barima a sak'ale har da sarkar kafa a kafarta ta hagu.

Hankalina ya sake tashi a fakaice na dinga share hawayen tausayi da nadamar duniya domin dai Hadiza ta gama tona mana asiri ta 'bata mana nasabar gidanmu, ta ci mutuncin Babanmu yanzu da muna da sauran 'yan uwa mata da wahala su auru da wuri dalilin wannan abin kunyar da ta janyo mana.

Anti Yagana tana da juriya sosai ban ga kwalla a idonta ba amma a gigice take mussaman da Babanmu ya fadi.

Ita kam Fati dama tana da iskokai domin tun tana yarinya sun taba nunawa zaman bori tayi a tsakiyar tsakargida suka dinga haurowa kanta suna ifece-iface anti sakina ita ce taje ta gurfana a gabanta tana yi mata addu'a.

Muka dinga zurga da kai kawo daga gidanmu zuwa asibiti zuwa ofishin 'yansanda.

Ni da anti Yagana mune manya kuma mune masu rufin asiri a ciki.

Itama Ummansu Hadiza sun ri'ke dukiya a da can domin mahafinsu tsohon mai kudi to amma yanzu babu domin duk rabinsu sun karye dalilin fafar da suka dinga yi da kudin gadon, kuma dama kaf gidansu babu wani fitacce wanda ya samu ilimin addini sun taso da jin dadi da gata irin na mahaifi wanda shi din aka shede shi mutumin kirki ne, kuma dukiyar da ya tara musu ta halak ce domin ko da can ma baya had'a hanya da riba.

To babu
abin yanzu da yawa wasu daga cikin danginta ma sukan rasa abinda za su sarrafa a cikinsu su bawa iyalinau.

Ga masifar da take ciki bata fita ba wata ta kara kutsowa Alajiji d'anta na fari da ta haifa a wani gidan ya je ya damfari wani makudan kudi asirinsa ya tuno yana hannun hukuma suna bincike akansa domin dama tsohon mai lefi ne ya jima yana harkar yahoo 419 shine kiran da ta yi Alhaji Tajo a kwanakin baya ta ke gaya masa ya taimaka musu.

Son zuciya
acinta kuma duk wanda ya sayi rariya tabbas ya san sai ta zubda ruwa idan da godiyar Allah iya jarin da Alhaji Tajo ya bata ya isheta ta juya ta kuma ri'ke kanta har ta kula da wasu to amma ta sanya son zuciya da son dole sai ta yi kudi ta kowace hanya ga abinda ya janyo mata nan.

Anti Yagana a gidana ta sauka wannan dalilin ya sanya muke zurga zurgar tare domin ba zan ta'ba bari ta yi ita kadai ba.

Hankalinmu bai kwanta ba har sai da muka ga jikin Babanmu ya dawo yadda yake tukkuna muka samu nutsuwar tattauna yadda za a kamo bakin zaran matsalar da Hadiza ta rikitowa kanta.

Lamari ne gagarimi wanda duk wanda ya ji abinda ta aikata ya jajanta mata don gaskiya da wahala idan hukuncin kisa bai rataya a wuyanta ba gashi an yi an yi da ita ta fad'i wurin da mutanan da suka sanyata suke ta'ki fad'a duk kuwa da azabar wahalar da take sha a hannun hukuma.

Ranar da muka je da dubata alfarma kawai suka yi mana dalilin ina auran Babban mutum amma da babu wani uzuri da zai sanya su bar mu shiga wajenta.

Kuka wiwi na dinga yi ganinta a jigace ta dimauce jikinta duk shacin duka abinka da farar fatar da aka had'a mata da man bilitin ta ki'dime sosai tana ta zantuka marasa tushe anti Yagana ce mai dauriya bata koka ba amma idonta kadai ya tabbatar mini da cewa kukan zucci take yi.

Fati kam fad'uwa ta yi a wurin aljanu suka bugeta a karon da ba zai lissafu ba domin tunda aka kama Hadiza take iskokai
Hassana da Usaina suka fita da ita can waje domin wurin da muke babu iska.

Da muka fito anti Yagana ta gargadi su Hassana akan kada wadda ta kuskura ta gayawa Ummansu halin da muka tsinci Hadiza su nemi hanyar da zasu kwantar mata da hankali koda kuwa ta 'karya ce don za ta iya shiga mummunan yanayi muddin ta ji halin da Hadizan take ciki.

A daran aka sallami Babanmu daga asibiti a waya na kira Ayuba sabon direba na ce dashi ya zo ya d'auke mu a mota gabad'aya domin a galabaice nake kwarai da gaske gajiya da jiri da ciwon mara da kafafu ban kuma kawo komai a raina face wahala da fargaba tare da kai da kawon da na yi.

Muna komawa gida ni da anti Yagana na zube a tsakiyar d'akina domin wani mashahurin ciwon mara ne ya turnike na dinga murkususu ina ri'ke cikina anti Yagana hankalinta ya tashi sosai ta kira Baba Tabawa tana cewa mu je asibiti na girgiza mata cikin halin da nake ciki na fara yun'kurin amai amma bai fito ba kakari na ke yi ban amayar da komai ba sai can na ji kamar an fasa ruwan pure water a zanina jini mai yawa ya fara gudana har ya fara naso a kafet din daidai inda anti Yagana ta ajiye kafarta.

Cikin fitar hayyaci na furta." Anti Yagana 'bari zan yi jini ne yake zuba."
A ki'dime ta tsuguna gabana ta daga cinyata jini sharkaf ya jika mini zani sai ta fashe da kuka tana fad'in." Ciki ne dake dama Amina Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Ta k'walawa Yusura kira tare da ce mata ta gayawa Ayuba ya fito da mota za mu je asibiti. dishi dishi na fara gani domin kuwa kafin faruwar hakan na yi masifar tsorata da irin mahaukacin jinin da nake zubarwa wannan shine ya assasa d'aukewar ji da ganina na wucin gadi.

To cikin dai ya zube a lokacin da ban yi tsammanin fitarsa ba.

Wahala kuma na ci ba 'yar karama ba domin kuwa biyu ne ashe na farkon ya fita ba mu jima da zuwa asibitin ba.

Na biyu sai da aka kai ga yin wankin ciki tukkuna aka yo waje dashi.

Jini kam na zubar ba kad'an ba aka dibi na anti Yagana aka sanya mini aka nemo leda daya a waje a kara.

Tun a daran anti Yagana suka yi waya da maigidan ta sanar dashi halin da ake ciki.

Ina jinshi lokacin da yake gaya mata ai ban ta'ba sanar dashi ina da juna biyu ba har wata uku da sati uku.

Ya ce mata in sha Allahu gobe mu tsammaci zuwansa.

Da safe Baba Tabawa da Yusura suka tafi gida domin yin abinci.

Anti Yagana tana tare da ni a asibitin motsi kad'an sai ta dube ni ta share kwalla.

Jikina ya yi sanyi na fara zargin ko likitan da yake tsaye a kaina ya yi mata bayanin wani abu ne.

Ni babbar fargabata ma zuwansa asibitin nan domin kuwa gabad'aya na yi sanyi da lamarin dalili na riga na san likitocin asibitin Malam Aminu suna da gogewa ta fannin aikinsu dole zasu yi binciken abinda ya asassa fitar cikin nawa.

Jiki babu wani kuzari na yi wanka da ruwan da ta had'a mini a bandakin dake cikin d'akin da nake kwance da yake waje na mussaman suka ajiye ni a asibitin dalili tun shigowarmu security suka shaida fuskata duk kuwa da yanayin da nake ciki na ciwo.

Littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na shirya cikin doguwar riga na kintsa jikina sosai cikin rashin kuzari da k'warin gwiwa gabad'aya rashin walwala da sukuninta ya fi damuna sosai akan fitar cikin daga jikina.

Likitan da yake duba ni ya sake shigowa muka gaisa ya yi mini tambayoyi na ce masa jiri ne ya fi damuna sai rashin jin dadin jikina.
Chapter 88 · 0% Book details