Sashe 156
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na gyada kaina a sanyaye na furta." Labarin abinda ya faru da ita ya ta'ba mini zuciyata."
Sai ya ce." Ta ba ki labarin Alhaji Amadu ya ta'ba nemanta ne?"
Na ce."E, wallahi, amma yadda aka kusa sabauta mata rayuwa shine abinda ya rikita ni, kai Allah dai ya yafe mana."
Cike da rashin gane inda na dosa ya ce." Shikkenan kuma saboda Allah bai kaddara an aureta ba sai a sabauta mata rayuwa komai yin Allah ne fa, tabbas na ji labarinta wurin alh Amadu lokacin jim kad'an da rasuwar matata ta biyu Ayush ba na gari ma yake gaya mini yana neman auran kanwar Aziza matar Alhaji Sulaiman daga baya kuma ya ce mini ya janye saboda wasu dalilai."
Na ce." Bai gaya maka gaskiya ba matarsa ce ta jefe ta ta d'ora mata muguwar jinyya mai razanarwa."
Ya gyad'a kansa kafin ya furta." Abinda ta gaya miki kenan?"
Na ce." Kwarai kuwa, Kuma gaskiya akwai 'kamshin gaskiya a maganarta domin wallahi zan gaya maka a sammace kake Maryam ta gama da kai."
Dariya ya fara yi yana kallona kafin ya furta." Ai ni kafin ki ga mace ta gama da ni wallahi sai ta yi da gaske Amina."
Na ce." Au haba?''
"K'warai kuwa, yanzu dai mu bar wannan maganar mu yi ibada domin mu samu lada."
Na ce." Magana fa ba za a bar ta ba, saboda kasan gaskiya Hajiya Aziza ta fada shiyasa kake bagarar da maganar wallahi ko ka 'ki ko ka so Maryam mashirika ce."
Da sauri ya ce." Subahanallahi!"
Na juyar da kaina gefe na ji yana fad'in." Ki daina ba ni so ranar lahira Ubangiji ya tsayar mini dake domin ki bada sheda shin kin ta'ba ganinta tana shirka da Idonki."
Na girgiza kaina a hankali kafin na ce." Ban ta'ba gani ba ayyukanta ne suka nuna haka a zahiri."
Jim ya yi yana nazari kafin ya ce." Kin ga wad'annan maganganun Amina na jima ina jin su akanta tun kafin ma na aureta da yawa an kawo mini suka akanta na rintse idona domin cika wasiyyar da abokina ya bari na kuma yi imani da cewa babu wani kulunboto da za ta yi yayi tasiri a kaina don haka kada ki gazgata kema tunda ba ki ta'ba gani da idonki ba, ki dubi alherinta kawai idan ma tana yi wannan tsakaninta ne da Allah."
Shiru
na yi na wani lokaci kafin na ce." Allah Ya kyauta amma tsakani da Allah wasiyyar nan da aka bar maka ba ta yi mana rana ba shi kuma duk cikinku ya rasa wanda zai bar wa wasiyyar auran matarsa sai kai, anya babu lauje cikin nad'i kuwa."
Ya 'bata ransa sosai Yana fad'in." Amina ba ni son abinda zai daga mini hankali a yanzu, na gaya miki maganar nan tun farkon fari wallahi tallahi babu wani dalili da zai sanya na ci amanar abokina wai da ransa na kwadaitu da matarsa kuma shi ya rubuta wasiyyar nan da hannunsa ni kuma na yi kokari cika ta domin na gaya miki ko ni na fadi na mutu zan yi farinciki ace shi ya maye gurbina a wurin iyalina dalilin aminci da sha'kuwar da take tsakaninmu."
Na ce." To na ji amma ai tun kafin ya rasu kake yabonta tare da fad'in kyawawan halayenta har cewa kake yi ta iya soyayya."
Ya dafe kansa kafin ya ce." Na fadi hakane saboda ki yi koyi da ita domin ni mutum ne mai son a kula da ni a kuma tarairayeni da soyayya.
Zan gaya miki gaskiya wannan ma yana daya daga cikin dalilan da suka sanya nake yabonta saboda ba ta tsallake umarnina kuma duk abinda na nuna masa soyayya tana yin fiye da yadda na yi idan kara na ajiye bata tsallakewa ke kanki da ta fahimci ina sonki ta taya ni sonki domin ban ta'ba ganin kishinki a tare da ita ba."
Murmushi na yi na takaici na yi shiru ban ce komai.
Idan ki ka karanta ba ki biya ni hakkina ba ina bin ki bashi.
Ya rike hannuna yana fad'in." Maganar nan don Allah kada a sake tashinta matar nan tana cikin halin rai da rayuwa ni dake da duk wani makusanci a gare ta adduarmu take buk'ata, kada ki yadda zantukan mutane su rusa miki tunani da Imani, ita kuma Hajiya Aziza na raina wayonta wallahi ai Maryam sanin da nayi 'kawarta ce sosai Aminiya abokin b'arawo ai b'arawo ne Amina mai zai sanya daga zuwa kawai ta gaya miki abinda ya jima..
Ubangiji ya hana fallasa asirin bawansa mussaman idan bawan nan ya yi tabbatacccen tuba."
Da mamaki na ce." Har yanzu dai ba zaka daina take gaskiya ka fifita karya ba ko, kai tsaye ka ki ka aminta da zantukan da suke yawo a gari akan matar nan, kai ma da bakinka ka fad'a cewa an gaya maka amma sai kame-kame kake yi kana kare ta Hajiya Aziza ai ba ta yi lefi ba tunda komai dalili yake yi.".
Ya ce." Ba wai kare ta nake yi ba Amina na ce miki Allah ne ya yi hani da cewa idan daya daga cikinku ya aikata kuskure ku yi shela a duniya mussaman idan bawan nan ya tuba babu wanda yake shiga tsakanin mahallici da bawansa."
"Ka tabbatar da cewar ta tuba?"
Da tsawa ya ce." Ke Amina maganar nan ta isa haka na ce miki wai ke wace irin yarinya ce ne, idan har ba ki nemi fitina ba ba kya jin dadi a rayuwarki ke ba za ki ta'ba ba ni nutsuwa da kwanciyar hankali ba."
Cikin dauriya na ce." Babban abinda ya daga mini hankali yadda har ka iya rufe Idonka ka gaya mata cewa Kamalu ya ta'ba yin fitina irin ta 'kuruciya a baya, sannan ka fitar da rikicin da ya faru a gidan nan har jama'a suna yamadidi da mu cewa mun had'e mata kai ni da Hauwa ba ma yin mu'amula da ita."
Ido ya tsira mini a rikice ya ce." Yanzu wanene ya kawo maganar Kamalu anan?"
Na ce." Ni ce na kawota domin na yi iyakacin bakin kokarina akan na ga na danne maganar a zuciyata na kasa abinda ya sanya ni sake gazgata cewa kai ka gaya mata a ina mutane za su samu labarin zaman da muke yi har su zage mu akan mun ware matarka tuntuni ka nuna hadin kan dake tsakanina da Hauwa baka so saboda ba mu sanya matarka a cikinmu ba har ka gaza ha'kuri ka fitar da maganar duniya."
Ya jima yana kallona cikin tashin hankali kafin ya ce." Ni ko Hajja ban ta'ba gayawa sirrin gidana ba mahaifiyata kenan.
Baban Saude shine mutumin da nake ganin zan gayawa matsalar da ta shafe ni ya ba ni shawarwari saboda na yarda da nutsuwa da adalcinsa kuma ki ji tsoron Allah Amina
Idan har za ki yi mini adalci ki fadi gaskiya akaina kada neman fitina ya sanya ki haddasa mini ciwo, ki fadi gaskiyar abinda ki ka sani a kaina na daga da'bia na tabbatar da cewa tsayin zamana dake zaki gane abinda zan aikata da kuma wanda ba zan aikata ba mai zai sanya kawai na zaunar da Maryam na gaya mata abinda ya faru a baya me yasa zan yi haka?
Uhm me yasa zan aibata Kamalu a wurin Maryam saboda soyayya ta yi mini dadi."
Ya kai karshen maganar cikin yanayi na damuwa da alhini."
Na ji hawaye sun zubo kumatuna ban goge ba na ce." To a ina ta samu labari idan ba kai ka gaya mata ba, ita kuma ta gayawa yaranta."
Ya yi d'an jim kafin ya furta." A lokacin da abin ya faru ke kan ki fa kin yi dogon rubutu a social media wato fecebook rubutun da ya zagaye kowace kafa ta sadarwa wanda bai san akan wane dalili ki ka yi rubutun akaina ba zai je ya bibiyi ba'asi kin manta da haka? kin manta cewa Salim zai iya cin karo da labarin ke ma fa kin bada gudummuwa wurin 'kara rura wutar lamarin domin dai kin san matsayina rubutunki kuma ya janyo cecekuce da yawa, me yasa za ki d'ora mini lefi?''
Shiru na yi ina kuka domin bakin cikin abinda ya faru ne gabad'aya ya taso mini.
Ya tashi tsaye yana fad'in." Ke duk yadda mutum ya so da ya zauna lafiya dake ba za ki ba shi damar hakan ba, ba ki iya rarrashi da tarairaya ba sai neman fitina."
Ya tafi ya je ya kwanta saman gadona tare da rufe k'afafunsa da bargo.
Kuka na ci na koshi yana kallona bai ce mini komai ba.
Na shiga bandaki na yi wanka na fito duk idonsa biyu na shirya jikina da kayan bacci.
Abinci na zauna na ci kad'an kafin na kwashe kayan na kai kicin na dawo d'akin yana dai kwance amma bai yi baccin ba.
Gefansa na zauna ina d'an kallonsa gabad'aya ya yi sanyi yanayin damuwa ya bayyana a fuskarsa.
Ban ce komai ba na ra'ba daga gefansa na kwanta ina jin bai fi sau uku ba ya ta'ba kwana a d'akina ba.
Ya mik'a hannu ya kashe fitilar gefan gado kafin ya janyo ni jikinsa sosai ya matse ni a kirjinsa muka sauka ajiyar zuciya kusan a tare jikinsa na dan rawa na ji maganarsa a hankali cikin taushi da rarrashi Yana fad'in." Da zan iya ha'kuri dake Amina da tuni na yi, Allah Ya jarrabe ni da sonki kada ki ga haka ki nemi halaka ni don girman Allah."
Shiru na yi ban ce masa uffan ba ina jin dai yadda hannunsa keta zarya a sassan jikina. yana mika bakinsa wuyana yana sumbata cikin sar'kewar murya yake fad'in." Mu yi soyayya irin wadda na Annabi s.a.w ya koyar Amina kada mu cutar da wani sashe na jikinmu ina buk'atar kulawa a yau ta mussaman kada ki yi mini 'kwange ki marabce ni da zuciya da gangar jikinki."
Na dai yi masa shiru ban tanka ba zuwa lokacin ma na fara bin layinsa.
Ya dago fuskata yasa bakinsa yana ta sumbatar kumatuna kafin ya fara ko'karin had'a bakinmu wuri d'aya.