Sashe 99
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har goman safe tana daki, bata zata ba se ji tayi ana murnar dawowar Abbansu da ya tafi Umarar Mauludi, dafe kanta tayi dan yanzu kam bata da dama dole ta fita tayi masa sannu da zuwa amma ba zataje yanzu ba seda daddare. Wayarta ta dauka ta sake gwada kiran number Khausar amma har sannan a kashe ake gaya mata dan tun jiya bayan ta dawo daga gidan su Hadiza take kiran layin amma a kashe.
Kiran Rufaida ne ya shigo mata taja tsaki kafin ta latsa wayar ta shiga silent dan a yanzu haushin kowa takeji, idan ba ta rama abinda Yayan Hadiza ya mata ba kuma ta ci uban Hadizan bazata samu sauqin abinda takeji a zuciyarta ba kuma ba zata tunkari Khalil yanzu ba se bayan ta gama da qaramar yar iskar tukunna zata koma kansa shima taci masa uwa, qilan karuwar tasa ta gaya masa abinda ya faru shiyasa tun tsahon jiya zuwa yau be nemeta ba amma zasu hadu ne, seya gane ita ya ciwa Amana.
WhatsApp ta shiga tana budewa kuwa sega saqon Khausar harda sauke ajiyar zuciyavta bude ta tarar da Voice note data turo mata bata bata lokaci ba ta kunna ta fara ji
"Jiya naji labarin abinda ya faru, yanzu kika yarda ace ga mari ga tsinka jaka?
Ta bi miki miji kuma kinje bin ba'asi yayanta ya dokeki wallahi karki yarda idan ba haka ba kina nan zaune ganin idonki zata aure miki miji kuma daga nan sunanki sorry, dan haka idan kin shirya inada qarin hujjoji da idan kika same su ko a qafa aka daurawa Mijinki na tabbatar da seya kwance ta ya gudu. Kafin nan dai kiyi qoqari ki kwaci yancinki ki rama abinda akayi miki idan kuma kinyarda kin karbi faduwa shikenan".
Cikin sauri ta fara typing bayan da ta gama Jin voice din se kuma ta goge ta mayar mata itama da Voice tace
"Idan na gama da ita ina nan kan juyowa kanki tsohuwar Annamimiya dan na tabbata bakinku daya dake da ita tare kuka hada duk wata qulla qullar datake bin mijina Allah kadai yasan dalilin da ya saka yanzu kika zame kika dawo kina bani bayanai a kanta, toh ni ba mahaukaciya bace da kike zaton zan yarda dake, idan ma kin angizani ne saboda a cutar dani toh ta Allah ba taki ba gani nan garas babu abinda ya sameni kuma zan dawo da shirin cin kutumar ubanku gaba daya keda su, kin gama mun aiki tunda har kika kaini gidansu, ki jirayeni idan na gama da ita kanki zan juyo" tana turawa ta dannawa lambar block dan zuciyarta ta gama bata bakinsu daya da Hadizan, qila ma wani shiri ne sukeyi na su fitar da ita daga gidanta dan su samu damar samun Khalil ita kadai toh kuwa uban da ya haifi uwarsu ma yayi kadan kuma daidai take da qugun kowaccen su.
Wuraren uku na rana saqo ya shigo wayarta.
"Naji saqonki kuma naga kinyi blocking numberta, toh ki duba na tura miki saqo da wata sabuwar number. Ni me qaunarki kuma bana nufin cutar dake sema kareki daga cuta da ha'incin da ake miki a bayan idonki amam zaki gane ba yanzu ba".
Tsaki ta buga duk yanda bata so amma zuciyarta seda ta tilastata ta bude saqon da tace ta tura mata a waya ta kirata, kai tsaye tace idan zata samu dama zata tura mata,
Hoton Hadiza da Khalil ne idan batayi kuskurena Ranar da ya tafi SA ne, babban abinda ya daga mata hankali hoton a cikin jirgi akayi shi, a zuciyarta ta ayyana 'kenan tare suka tafi' kamar kuwa Khausar tasan tunanin da takeyi kenan ta turo mata da cewar
"Tare suka tafi, a cikin satin daya wuce ta dawo kuma tace zata sake komawa dan daqyar ya barta ta taho".
Wani abu taji ya danne zuciyarta yana neman katse mata numfashi se kawai ta sulale a qasa wasu hawaye masu zafin gask suka shiga kwararo mata. Kwakwalwarta tamkar an liqeta ta kasa kawo mata kowanne tunani illah na Khalil da Hadiza ya tafi, kenan shi yasa sam baya wani nuna kewarta lallai Khalil.
Anty da shirun Umaiman ya dameta ce ta ga Abba ya dawo har su Maman Asad sunzo tace bari dai ta leqa ko lafiya Mama dai ko a jikinta sabgarta takeyi. Yanda Antyn ta tarar da ita ya bata tsoro, ta dagota tana tambayarta lafiya meya samu fuskarta ta kasa cewa komai se kuka kawai. Qirjinta zafi yake zuciyarta kamar zata fashe wai Khalil ya raba musu kansa ita da wata Karuwa a waje wallahi ko duniya zata tashi bazata yarda ba, seta daidaita yarinyar nan idan ma bata halakata ba.
Kuka kashirban ta dasa sanda Anty ta yayibo mutanen gidan akan suzo su ga yanda take, Mama dai bata zo ba tunda taji kan zancen jiya ta barwa ranta duk ma inda taje da abinda tayi z fito ne a bakin su taji wai tace musu zamewa tayi a bandaki Hankulansu suka sake daguwa Maman Asad na ta tashi su tafi Asibiti tace babu komai lafiya lau take jinta dukda haka bata haqura ba seda ta kira wata qawarta ta hadata da Umaiman tayi mata tambayoyi kafin tace mata babu komai in taji wani abu ba daidai ba taje Asibiti sannan suka haqura. Mama dai dariya tayi daman tana dakin Abba daya kwanta baccin gajiya Anty take mata bayanin tace Allah ya rufa asiri daga haka bata tanka ba.
Umaimah bata samu fita zuwa inda Khausar ta kirata ba, kwana tayi idonta biyu tana saqa da warwarar matakin da zata dauka akan Hadiza da Khalil. Qarfe daya da rabi na dare ta gaji da juyi a gado ga shi ta rasa mafita akan abinda ya kamatu tayi bata daddara ba ta sake dannan kiran layin Khausar cikin Sa'a ya shiga ringing biyu ta daga muryarta da alamar bacci take tambayar wanene
"Umaimah ce, dan Allah kiyi haquri da maganar dana gaya miki dazu raina ne ya baci baki san irin halin dana tsinci kaina a ciki ba tunda kika bayyanamun abinda yake faruwa tsakanin Mijina da Qawarki, yanzu abinda yasa na kiraki akan taimakon da kika ce zaki yimun ne shi nake so naji wane shiri kike dashi akan ta da kika ce zai taimaka mun? Sannan ke din wacece, meye alaqarki da ita sannan me tayi miki da har kika zabi ki bayyanamun alaqarta da Mijina akan ki rufa mata Asiri a matsayinta na qawarki?" Umaimah ta fada murya a dashe saboda kukan da ta sha.
Shiru Khausar tayi dan har Umaimah ta cire tsammanin tana tareda ita sannan taji tace
"Tabbas qawatace Hadiza koma nace miki Aminiyatace amma tayi mun abinda har duniya ta nade bazan manta ba kuma na kasa yafe mata, kamar yanda take qoqarin shiga tsakaninki da Mijinki haka ta ringayi mun, duk saurayin dana hadu dashi a rayuwa baya zuwa biyu gurina in gar sun hadu ze koma yace ita yake so, ta rabani da duk wasu namemana kuma itama ba auransu takeyi ba, zata cucesu ne ta karbi abinda zata karba agurinsu kafin ta barsu kinga daga ni har ita munyi Asara kenan.
Sannan bayan wannan da akwai babban sirrinta wanda qalilan mutane ne suka sanshi, Hadiza mata take nema yan uwanta abinda har yasa nake sakewa ina nunawa Samarina ita kenan dukda tafini kyau da haduwa a zatona babu abinda zatayi dasu tunda ba layinta bane amma kuma sedaga baya na fuskanci ba haka bane, qazamar rayuwa takeyi tana hada mata da Maza duka tana mu'amala dasu abin mamaki kuma Mijinki ya sani a hakan kuma yake tareda ita dukda ina zargin abin nata harda Asiri a ciki, a cewarsa idan ya aureta yayi jihadi zata dena duk abinda takeyi
Wani dum Umaimah taji akanta, yanzu a ce duk matan duniya Khalil ya rasa wadda ze nema se yar Lesbian kuma har yana fadin wai Jihadi zaiyi, sam kwakwalwarta bata nemi hango gaskiya ko qaryar abinda Khausar ta gaya mata ba ta hau kai daram ta zauna,
"Kika ce Khalil ya sani?" Ta tambayeta cikin wani irin sauti, Khausar ta juya ta kalli Shema data rubuta mata duk abinda zata gayawa Umaiman ta bata hannu suka tafa kafinta jinjina kai kamar tana gabanta tace
"Na tabbata, na sanar Miki da cewar Aminiyata ce idan kinada tantama ki tambayi Mijinki wacece Khausar qawar Hadiza" duka Shema ta kai mata a baki ita kanta bata san sanda ta bige bakin nata ba ta zaro idanu, kallon bakida hankali Sheman tayi mata se tayi saurin gyaran murya tace
"Karima qawar Hadiza zaki ce masa idan kika fadi haka duk wata maganada ze ji a bakinki baze taba qaryata wa ba danyasan nasan komai akansa da ita Hadizan kuma yanzu zan tura miki da evidence din da nace dan ki sake tabbatarwa da kanki".
Umaimah bata iya magana ba, a maganganun kaf iya abinda ta gane yar Lesbian Khalil yake shirin dauko mata a matsayin kishiya se kuma sunan Khausar da ya samu guri a kwakwalwarta dan ita bata ma ji wani rudewa da tayi akan subul da bakan na balle canza sunan da tayi, Khausar din kawai ta riqe kuma tana katse kiran tayi saving number da sunan sannan ta koma WhatsApp tayi unblocking nata sega hotuna kuwa sun fara shigowa harda videos.