← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 267

Sashe 42

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kefa baki da kirki wallahi daga gaya miki abin arziqi zaki farayiwa mutum tsiya kuma karki sake cemun Usaini wallahi" Khalil din ya fada yana dariya.

"Aa zancen gaskiya mana toh bari zan gayawa Hajiyar tunda naga kunya kake ji, ina qanwar tawa mu gaisa?"

Kallon Umaimah data tunzura baki gaba yayi dan a speaker ya saka wayar tana jin duk abinda suke fada se yace
"Ta kwanta Kinsan likita yace ta ringa hutawa"

"To shikenan zuwa da safe zan kirata in Allah ya yarda amma fa ba wai kuma ance ta huta ka saka ta tayita kwanciya kamar ruwa bata motsa jikinta ba, Aa ana so a ringa motsawa aikin da ze jigata ta ne dai ba'a so kaima seka rage zalama ka bar yar mutane ta nutsu tunda kayi abinda kake so, Allah ya inganta ya bada lafiya" Jalilan ta fada daga nan sukayi sallama tana sake jaddada masa daya kula da Umaiman.

Umaimah kuwa hankalinta na kan Agogo, qarfe goma na bugawa ta tashi ta dakko wayarta dake jikin chaji ta koma kan kujera ta harde, shima bebi ta kanta ba ya chanza tasha zuwa Channels ya fara kallon labaran qarfe goma.

Tana hawa ta bude group din kuwa ita ake jira dan har an rufe group anyi mata Admin, shugabar gidan me suna Anty Haris kamar yanda ta gani a rubuce ce ta fara gabatar da ita a matsayin sabuwar member daga nan ta bata dama akan ta gabatar da kanta.
"Sunana Umaimah Sabo Mukhtar, ni yar Kano ce, ina da aure. Shekaruna 22" ta tura musu a taqaice.

"Masha Allah Malama Umaimah muna mik barka da zuwa wannan gida, amma baki fadi Unguwar da kike ba saboda idan da wanda kuke kusa kinga se ku qulla zumunchi haka mukeyi a nan" daya daga cikin Admins din ta bata amsa,

"Ina unguwar Tudun-yola Gate 4" ta sake turawa tana yatsina fuska, sun fiya iyayin tsiya Allah sa dai ana abin arziqi a group din.

"Aa kice yar unguwarsu uwar daba ce, Ke Rufy kina ina fito ga yar Area kin samu" Admin Anty Haris ta turo da Emojin rawa kafin ta sake ce da Umaiman
"Saura ki turo da Hotonki ki kuma yi voice note saboda mu tabbatar da Macece yar uwar mu ba masu shigewa cikin mata ba"

"Kan bala'i lallai ma mutanen nan da rainin wayo suke" Umaimah ta fada a fili tana gyara zama, Khalil ya juya ya kalleta beyi magana ba ya maida kai yaci gaba da kallon News dinsa se yaga ta miqe ta shige cikin daki kuma.

Tana shiga kan gado ta haye, hotunanta ta shiga dubawa ta samo wani da sukayi weekend din daya wuce sunje Zazu cin Abinci da yamma Khalil ya dauketa tayi kyau sosai dukda Hijabi ta saka tana turawa ta sake aika Voice note tace
"Inayiwa kowa fatan Alkhairi" daga nan aka bude group aka shiga yi mata barka da zuwa yan group dai masu kirki anata faran faran da ita nan da nan itama ta sake aka fara hira sam bata ankare da lokaci ba seda taji an turo qofar dakin tayi saurin tura wayar qasan pillow tayi lamo kamar me bacci dan daman ta kashe fitila.

"Umaimah" Khalil ya kira sunanta daga bakin qofa tayi shiru bata amsa ba, seya qarasa ya tsaya daidai kanta murya a cukule yace

"Tashi muje mu kwanta" nan ma tayi masa shiru bata motsa ba.

"Nasan kina jina dan haka ki tashi karki bata mun rai" ya sake fada, yabda yayi maganar sam babu wasa a ciki ya sakata yin miqa tana tura baki ta kalle shi tace

"Nifa bacci nakeyi ka tasheni"
"Wuce muje" ya fada yana matsa mata hanya, se data harareshi ta qasan ido kafin tace

"Kaje zan taho bari na shirya".
Kwafa yayi ya fita dan tunda dazu da ta tashin ya rage volume din Tv yana jiyo ta tana playing voice notes din mutane har kuma yazo jikin qofar yaji dariyarta seda ya taba qofar tayi qara kafin yasan ta ajiye wayar shine zatace masa bacci takeyi to dole ya taka mata burki dan baze dauki wannan salon chatting din daren ba, yana zaune ta mayar dashi hoto tana hira da wasu can a waje da mazansu basu damu dasu ba da har suke barinsu su raba dare suna chatting

Kusan minti goma da shigarsa dakinsa yaji ta shiru a fusace ya sake komawa dakin nata, bata ciki, jikin socket din da take saka chaji ya duba bega wayarta ba dan haka kai tsaye ya wuce bandaki.

Umaimah kuwa Khalil na fita ta dauki wayarta ta shige Bandaki, akan Masai ta zauna taci gaba da duba Messages din group dan wata ce take neman shawara akan mijinta nada kule kulen yammata shine ake ta bata shawarwarin abinda ya kamata tayi ta sakankance se jin bude qofa tayi, a sittin ta jefa wayar cikin kwandon kayan wanki ta durqushe a qasa ta fara kakarin Amai daidai sanda Khalil ya tura qofar ya shiga.

"Subhanallahi Amai kuma?" Ya fada yana qarasawa inda take duk fushin daya shiga dashi lokaci daya ya washe ya ruqota jikinsa yana shafa bayanta ganin yanda take kakarin Aman kuma babu abinda yake fita.

Sunfi minti biyar tana ta yunqurin iska kafin ta miqe tana riqe ciki a qaryarta wai juya mata yake Allah sarki haka ya ringa mata sannu yana lallabata ya tara mata ruwa me dumi ya wanketa tas ya dauketa suka wuce dakinsa, madara tace masa zata sha kuma se an tafasa, ba yanda ya iya haka ya kwantar da ita ya wuce kitchen din dukda sha biyu ta gota a sannan Umaimah ko tanajin ya sakaya qofa ta fito daga dakin sadaf sadaf taje ta dakko wayarta daga bandaki, bata tsaya bata lokaci ba ta kashe ta gaba daya kafin ta jona a chaji ta koma dakinsa ta kwanta. Daya kai madarar ma kurba biyu tayi tace ta qoshi ya karba ya ajiye yana ta mata sannu ita kuwa tayi kwanciyarta dan har yanzun fa ba wai ta yarda dagaske tana da wani ciki bane ma tunda babu abinda take ji ko wata alama da ake fada ta masu ciki.
Ita haushin ta katse mata hirar da yayi tana shirin bada tata shawarar, amma babu komai sa hadu da safe.

Washe gari da ta kama juma'a tunda Asuba yace ta shirya idan ze fita seya sauketa a gida ta wuni, sosai ta ringa murna, tare suka hada abin karyawa dan cewa yayi tabar shara kwanukanda suka bata kuwa suna gamawa yace ta shiga wanka shi kuma ya daurayesu kafin shima ya shirya. Qarfe tara suka fita seda zasu gota gidan Rufaida tace masa

"Au na manta wallahi matar gidan nan ta haihu idanna dawo yau ko gobe zan shiga nayi mata barka"

"Allah ya kaimu, idanda abinda zaki kawo mata se ki gaya mun" ya bata amsa kafin suka ci gaba da hirar su har suka qarasa, a gurguje ya gaisa da Anty dan basu tarar da Mama ba tun sassafe sun fita tareda Abban taje asibiti ganin likita idonta ya matsa mata da ciwo dan haka be zauna ba ya wuce Office dan ya makara, Umaimah kuwa guri ta samu ta fara zuba iskancinta yanda ranta yake so.

Da farko Doya da kwai Anty ta kai mata da kunun gyada, saboda tsabar shahara a iskanci irin nata da son ta nuna musu tayi ciki Antyn na ajiye flask din doyar ta toshe hanci da hannu biyu tana ja baya, kallonta Antyn tayi da mamaki tace

"Lafiya Umaimah?"
"Bana son qamshin doyar ki fita da ita" ta fada kamar zatayi kuka se Anty ta saki murmushi tace
"Toh ai da tun kafin kuzo ya kamata ki kira ki fadi abinda kike so a dafa miki, yanzu me zaki ci toh?"

Yatsina fuska Umaiman tayi tace "ba komai"
"To ko a baki kunun zallah shi zaki iya sha ai dan yanzu ma aka tafi kaiwa Nuratu tace tana so" Antyn ta sake fada.

Kamar wadda aka wa dole haka ta ringa wata yatsina tana shan kunun, can cikin ranta ko hadiyar yawu take dan doyar ta shiga ranta gashi ta rigada tace bata ci. Tana kallo Yaya Aminu yazo ya zubo doyar da kunun ya zauna kusa da ita yana ci Anty na ce masa daya koma gefe Umaiman bata son qamshin. Yace
"Ikon Allah su kuma daga ita har Nuratun daga zuwa ko wata biyu baku rufa ba se ciki tab Allah ya raba lafiya toh"

"Kaji mun mutun se kace shi ba wata tara tasa matar ta haihu ba ze sakawa Mutane ido" Umaimah ta fada a zuciyarta tana hararar sa qasa qasa dan duk rashin mutunchinta bata shiga sabgarsa dan ubanta yake ci, Anty ce ta tare musu ya gama cin doyarsa ya tashi daidai sanda Anty take tambayar Umaiman me zata ci

"Wai yau Juma'a ba wake da shinkafa akeyi a gidan nan gaba daya dana sadaka ba shine zaki tsaya kina tambayar me zataci se ta dafo abinda take so daga gidanta ai ta taho dashi ko" ya fada yana ficewa daga dakin

Haka ta wunitana nade a daki tana aikin dannan waya, sanda Mama ta dawo taga iskancin nata bana qare bane bata bi takanta ba, abincin ranar ma da aka saka mata man gyada har tayi loma biyu ta ture wai da Manja take so aka sake janzawa ana ajiyewa tace a fita dashi bata so Anty ce take ta jigila akan ta me take so me za'a mata se wana baiwar Allah take can qasan ranta tana tuntsura dariya tana kuma hasaso yanda zata saka Khalil a gaba da laulayin qarya ba ita ta samu salama ba se da Khalil ya dawo ya dauketa suka tafi bayan da Mama ta ja mata kunne sosai akan shegen Chat din da take tayi tunda taje gidan.
Chapter 42 · 0% Book details