Sashe 74
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ta fara maganar yake kallonta, qawar wannan mayyar yarinyar ce, to wai su a nan garin suke ko kuwa yawon rashin jin nasu ne ya kawo su?
Kallonta yayi sama da qasa yanzuma tana sanye da doguwar rigar Atamfa ta saka Hijabi Light blue daya zarce guiwarta, sosai Hijabin ya baci da ruwan kwatar daya watsa mata, cikin gajiya da masifar da takeyi masa yace
"Kiyi haquri, banganki bane"
"Dama ai bazaka ganni ba"
"Nace kiyi haquri" yayi saurin tareta ganin tana neman tara masa mutane, shiru tayi shima ya tsaya, kamar baya so yace mata
"Ina zakije ga magriba tayi?" Sedata harareshi sannan ta gaya masa, kallonta yayi fuskarsa na nuna mamakin jin sunan Hotel din data fada amma kuma meye nasa a ciki ma, juyawa yayi ya bude motar yana cewa
"Muje na saukeki" seta juya tabi bayansa. Tafiya sukeyi babu me magana da wani, wayar dake hannunta ta dauki qara ta daga da sallama yanda take maganar ya fuskanci da Mahaifiyarta suke wayar, sannan a maganganunta ya gane cewar aiki ne ya kawota Lagos din to amma aikin me takeyi? Bayan ta gama wayar ta kashe haka kawai ya tsinci kansa da tambayarta aikin me tazoyi nan, seda ta harareshi kafin ta gaya masa suna aiki da NGO ne kuma an turo su yin wani assignment ne.
Har qofar Hotel din ya sauketa, ta kalle shi fuska babu yabo babu fallasa tace ta gode, kallonta yayi yace
"Nawane kudin wankin Hijabin naki da kike tayi mun tsaki a mota saboda ya baci" seta harareshi bata ce komai ba, murmushi yayi dan se ya ganta kamar Umaimansa dukda a yanzu daya qare mata kallo ya fuskanci ba yarinya bace, a qalla zatayi shekara Talatin ko fin haka. Wayarsa dake ajiye ya miqa mata yace
"Ki saka mun number ki idan kin tsayar da farashin se ki gaya mun".
Kallonsa tayi kamar bazata karba ba kuma seta miqa hannu ta karbi wayar ta shigar masa da number ta bashi yayi Dialing wayarta tayi qara ya kalleta yace
"I'm Khalil, and you"
"Hadiza"
"Nice to meet you Khadija" ya fada yanayiwa motar key ta dan ya mutsa fuska tace
"Hadiza sunana"
"Khadija ne sunanki na Asali ni dashi zan kiraki, ki shiga ciki se wani lokacin" yana gama fadar haka ya taka motar ya bar gurin.
Yana tafe yana tuhumar kansa dalilin daukota har zuwa karbar number ta da yayi, zuciyarsa ta bashi amsa da yana da buqatar Abokin hira ne daze debe masa kewa shine dalili, sannu sannu Abota ta qullu tsakaninsu a hankali shaquwa me qarfi ta shiga ya zamana cewa a kullum se sunyi waya dukda Hadizan ta koma Kano amma a koda yaushe suna maqale da juna a waya musamman da dare bayan ya koma gida bashida abinyi sedai ya kiraya su sha hirarsu. Yasan kusan komai a kanta, Ita din Lauya ce me zamankanta kuma tana aiki da qungiyoyin kare haqqin mata da qananan yara.
Yanzu idan ya tuna da Umaimah to kewar Mu'ayyad ce ta dame shi akan dole kuma ya sakawa kansa haquri tunda bashida hanyar da zeji lafiyarsa ko ya ganshi, abinda ya sani dai ko bajima ko ba dade dole ta nemi shi, idan bata neme shi ta arziqi ba zata neme shi ta tsiya.
UMAIMAH
Tun tana daukar abun a wasa harta fara shiga taitayinta ganin ana neman wata daya da doriya babu Khalil babu dalilinsa, a tunaninta data kashe waya ze nemeta kota wayar Mama ne ko ya aiko Khalifa se gashi babu daya daga ciki hasalima ita kanta Maman bata ce mata komai ba akan zaman nata, kowa ya zuba mata ido ne kawai suga iya qarshen Al'amarin.
Kudaden hannunta da suke rudarta sun qare tas ko na siyan Data bata dashi dan daman wayarta a kunne take, layinta da aka santa dashi ta cire ta ajiye ta dora wani duk a shawarar Rufaida taci gaba da sabgoginta, sanda tayi mata maganar ita zata Kira Khalil dan da alama yayi fushi da yawa ce mata tayi idan tayi haka ai ta zubda kanta, ta daure kawai harya gama fushinsa ya sakko duk tsiya dai ai ze dawo baze koma can da zama gaba daya ba.
Yau ta tashi gaba daya babu yanda take, Allah ya sani tana son mijinta kuma tana kewarsa daurewa kawai takeyi kamar yanda Rufaida take gaya mata wai ta kama Ajinta karta kuskura ta bari ya gane ta karaya dan daman yanayi ne dan ya qureta.
Salma ce ta shiga dakin da sallama ta ajiye mata Ruwan zafi a babban Mug se burodi a leda, kallon kayan tayi daman tun tuni ake wulaqantata a gidan nan abinci se a bata kamar wata mabaraciya wani lokacinma idan an dafa seta roqa za'a bata cewa suke sun manta da ita.
Kayan taja gabanta ta kalli baqin ruwan shayin ta ja tsaki, gwangwanan kayan Tea din da Khalifa ya kawo mata tun wancen watan da tulin siyayyar Mu'ayyad su Diaper, wipes, madararsa da cereals sabulun wanki da duk wani abun buqata seda ya hado musu da yawa kuma yanda zata dade kafin ta buqata.
Kallon Madarar tayi bata wuci kwata a ciki dukda qaton gwangwani ne amma ta kusa shanye shi cikinta ita kadai saboda yanda take barnarsu haka kawai ma kwabawa take tana sha gashi yanzu sun kusa qarewa bataji daga me siya mata dinba kai ita wannan zaman ma ya isheta haka ita ba sakakkiya ba ita bame aure ba bari kawai ta karya billenta ta kira shi ai durqusawa wada ba gajiyawa bane.
Layinta data ajiye ta dakko ta saka a wayar, Allah ya taimaketa tana duba balance taga akwai kudi a ciki, layin Khalil ta shiga kira tana kallon Agogo ta san dai yanzu duk inda yake yaja Gym kamar yanda yakeyi duk Asabar da Lahadi se yaje.
Seda tayi masa kira uku be amsa baana hudun yana shiga akayi rejecting se ta riqe wayar sororo a hannunta jikinta yana qarayin sanyi, tasan fushin Khalil yana daukar lokaci kafin yayi amma fa idan ta taboshi seta sha wahala kafin ya sauka amma dukda haka ita a yanzu buqatarta ya haqura da gayyatarta idan zeyi tafiye tafiyensa idan dai haka ta samu zata san yanda zata lallabashi su shirya.
Maida wayar tayi ta ajiye ta shiga karyawa a ranta tana ayyana qaryar da zatayi dan ta samu hankalinsa cikin ruwan sanyi batareda wata matsala ba. A dakin taci gaba da zaman tsammanin ko ze biyo bayan kiran da tayi masa, Mu'ayyad na can gurin Anty dan kusan kwanciyar baccin dare kadai ke kaishi gurinta se shan Nono wanda bema damu dashi sosai ba tunda ya kama abinci.
Tana nan jiran gawon shanu har aka kira sallar Azahar, seda tayi sallah ta quduri sake kiransa. Tana zaune akan sallayar ta janyo wayarta ta shiga kiran layin Khalil din ringing uku taji an daga taja wani numfashi ta dire ta narke murya kamar Kitse yaji wuta tace
"Habibi"
"Umaimah, ina aiki ne. Idan babu damuwa ki bari zuwa dare idan na koma gida zan kiraki ok" Khalil ya fada cikin dakakkiyar murya daga daya bangaren, kafin ta samu cewa wani abu dif ya kashe wayar seta cireta da kunnenta ta zura mata ido kamar zata ganshi ta cikin wayar, ita ze cewa yana aiki ta bari ze kirata daga baya? Khalil din data sani Sallah ce kadai zata kirashi yana yi da baze katse ya amsa kiranta ba shine yanzu ze gaya mata yana aiki ne.
Tagumi ta rafka hannu biyu karfa kwabarta tayi ruwa daga neman gira a rasa ido, to waima tsahon wannan lokacin da suka dauka Khalil din be nemeta ba ya ya yake rayuwa, wacece take debe masa kewarta da duk sauran buqatunsa ina yake kaisu? Kai wai ita wace toshewar basira ce ma ta sameta haka data sake shi a bariki shi kadai, sam ta manta da yanda Lagos din nan take. Mata ne suke neman maza ba maza ke neman mata ba ballantana irin Khalil daya hada duk wasu qualities da zasu saka mata su soshi, to yanzu shirun nan da yayi mata idan ya zama na wata ya samu take debe masa kewarta fa?
Zabura tayi ta miqe tana salati saboda wannan tunani daya fado mata dagaske idan ya zamana Khalil wata ya samu fa shiyasa ya manta da ita dan Khalil din data sani baze yi fushin wata daya da ita ba ballanta har ya iya zama a wani gari daban ba tareda ita ba na tsahon wannan lokaci bama ze yuwuba sedai idan kuma wani abin ne ya faru dashi bata sani ba kuma ba'a gaya mata ba.
Hannu ta dora aka tana juyi a dakin, tunani biyu ne suke mata zarya kodai Khalil ya samu wata ko kuma wani mummunan abu ya faru dashi an boye ba'a gaya mata ba. Wayarta ta dauka ta shiga sake kiransa, missed calls ta ringa tara masa ita kanta bata san Adadin kiran datayi ba kafin ya daga cikin fada fada yace
"Wai Umaimah bana gaya miki ina aiki bane ki bari zan kiraki idan na gama"
"Khalil ka amsa mun kawai lafiyarka qalau ko Aa? Idan kuma qalau kake wace yar iskar Karuwar ce ta dauke maka hankali da har ka manta damu tsahon wata daya baka waiwaye mu ba" ta fada cikin tashin hankalin daya rufeta ga mamakinta se ji tayi yaja wani shegen tsaki kafin tace wani abu ya kashe waya seta fasa ihu iya qarfinta tareda yin wulli da wayar ta fadi a qasa, Mama dake tsaye bayanta ba tareda ta sani ba ta watsa mata Marin daya sakata dauke wuta na wani lokaci, nuna ta tayi da yatsa tace
"Ki shiga hankalinki Umaimah, ki shiga hankalinki" kafin ta juya cikin matuqar bacin rai tabar dakin. Ta rasa wacce irin yarinya ce Umaimah, ita dai bazata taba yarda da lafiyar kwakwalwarta qalau ba dan abubuwan da Umaimah takeyi sam basuyi kama dana me cikakken hankali ba.