← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 267

Sashe 113

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama da tsabar qarfin Hali ta miqe tana watso kwanukan abincin da Anty Bilkisu take kai musu suka taho dasu ta tsaya tana kallonsu, dakyar ta iya bude baki tace
"Isma'il ka rabuda yarinyar nan idan ba so kakeyi fushinta ya shafeka ba"
"Mama ki tsaya ki saurareni Hadiza bata da laifi sharri akayi mata munyi kuskure da muka kasa yi mata uzuri har bincike ya tabbatar da gaskiya ko akasin haka akan abinda ake zarginta dashi. Wallani sharri akayi mata kuma yanzu haka wadanda suka aikata suna hannun Hukuma.

Kabbara Malama Lawisa ta dauka tana kallom Mama data sandare a tsaye tana kallon Isma'il din sw tace
"Allah nagode maka daka wanke yarinyar nan tun ba'aje ko ina ba. Kin gani ko Karimatu kinga abinda ake fada miki akan kibi komai a hankali? Yanzu wa gari ya waya, da wanne ido zaki sake kallon yarki bayan duk mugayen kalaman da kika gamayi akanta kin gagara daukar qaddara gashinan tun ba'aje ko ina ba Ubangiji ya wanketa sol ya bar munafukai da jin kunya".

Jiki babu kwari Maman ta juya ta zauna a inda ta tashi, Isma'il ya kamo Hadiza da itama take cikin mamakin kalamansa, ya akayi ya gano wanda suka qulla mata wannan sharrin 'Khalil ne' Zuciyarta ta bata amsa. A gaban Maman suka zauna shida ita yana kallonta yace
"Kamar yanda na fada miki Mama an gano cewar sharri akayiwa Hadiza kuma yanzu haka ana kan bincike. An kama biyu daga cikinsu dayar ce bata rigada tazo hannu ba kuma wallahi Mama bazaki yarda ba idan kikaji su waye keda saka hannu a cikin wannan abun".

"Zan yarda mana Isma'il tunda har ka iya gamsar dani cewar Hadiza ta aikata abinda ake fada akanta babu kuma sauran wani abu da zaka fada ya bani mamaki kona kasa yarda" Maman ta fada tana kallon gefe. Yanda kasan qasa ta bude ya shige ciki haka yaji kunyar furucin Maman, shi ya kawo mata labarin ta qaryata ya kuma tabbayar mata da yayi bincike gaskiya ne se a yanzu yake nadama tabbas be kasance dan uwa na gari ba ya tabbatar idan Hadiza ce a matsayinsa zata kare shi da iyakar iya warta.
Kansa na qasa ya bude baki yace
"Ki yafe mun Hadiza na cutar dake ba akan haqqinki ba, nayi gaggawar yanke hukunci ba tareda na samu qwaqwqwarar hujjaba ki yafe mun dan Allah, kuma nayi miki alqawari bazan zauna ba har se na tabbatar da anyi miki aldalci s an bi miki kadin bata miki suna da sukayi".

"Ka dena bani haquri Yaya ba kai ba koma wanene irin wannan al'amari ya riske shi ze iya aikata abinda yafi wnada kayi. Baqin cikina guda daya ne dana rasa samun yardar ko mutum daya daga cikinku, daga kai har Mama kuka kasa shaidata amma nayi muku uzuri zamanin da muke ciki ne yayi lalacewar da bazaka iya shaidar halin Dan Adam ba saboda munfi Hawainiya saurin rikida a yanzu. Kuma ni na rigada na gayawa Khalil na yafe musu dan haka karka wahalar da kanka gurin yin shari'a da kowa, ni suka sabawa kuma na yafe musu Allah yasa hakan ya zama izina ga sauran mutane baki daya" Hadiza ta fada hawaye na sakko mata idanunta akan Mama data juyar da fuskarta gefe ta gagara ce musu komai.

Harga Allah nauyi da kunyar Hadizan ne ya kamata, ta haifeta a cikinta ta raineta, halayyarta babu wadda bata sani amma lokaci daya wani al'amari ya bijiro ta kasa bata mafaka a lokacin da duk duniya take mata kallon fasiqa.

Tana jin Malama Lawisa nata jefa mata magana, Isma'il yayi musu sallama akan gobe da safe ze zo su tafi can tare gaba daya yana kuma jaddadawa Hadizan da tayi haquri ta yafe masa ita dai tayi shiru har sannan tana durqushe gaban Mama, jira take yi tayi magan, so take taji ta yarda da ita ko kuwa har yanzu tana kan bakanta kuma bazata barta ta zauna a gidan ba.

"Ki tashi kije dakinki ki kwanta saboda jikinki" Maman ta fada kamar bata son magana ba tareda ta kalleta ba, se Hadizan ta miqe dan daman abinda take jirane ta wuce cikin dakin tana jin wani nauyi daya danne mata zuciya yana raguwa. A gaba daya abinda ya faru yardar Mahaifiyarta da Dan uwanta data rasa su suka fi komai yi mata ciwo kuma ko a yanzu idan har suna tareda ita zata iya fuskantar duk wani qalubale da ze tunkarota a gaba.

Mama kuwa Hadiza na shigewa daki ta fashe da kukan da take dannewa daidai nan kuma Mama Innani da Hajiya Barira suka shigo, masifa Hajiya Barira ta farayi akan kukan me Maman takeyi, Malama Lawisa tace
"Ku tambayeta dai, qila baqin ciki takeyi Allah ya bayyana gaskiya ya wanke yarinyar nan dukda muggan kalaman data gamayi akanta. Ni kunga tafiyata, Hadizan na ciki ga ledar Magungunanta nan kuma se an taimaka mata saboda Daurin da yake hannunta. Ke kuma Karimatu wannan ya zamar miki ishara, Jarabawa ce ubangiji ya saukar miki kuma kika gaza dauka se kije kiyita istigfari kuma ki nemi gafarar yarki dan idanbata yafe miki ba la shakka se kun tsaya a gaban Allah cikin wadanda suka yi mata qazafi" a fusace take maganar tana gamawa ta figi jakarta tayi waje bata ko tsaya amsa tambayar da suke mata ba.

Kan Maman suka juya, tana kuka ta gaya musu yanda sukayi da Isma'il,
"Nayi kuskuren daukar fushi ba tareda anyi bincike ba, yanzu da wanne baki zan bawa Hadiza haquri? Kuna kallo wasu a bakina suka qara gasgata maganar a maimakon na zama me kareta ni na sake zama silar tona mata Asiri kaicona" ta qarashe tana kuma rushewada kuka Hadiza dake maqale jikin qofa ta sulale a qasa tanaci gaba da nata kukan mara sauti. Tabbad Qazafi yanada radadi kuma wanda aka tabayiwa ne kadai ze fahimci halinda dan uwansa yake ciki amma dukda haka ta yafe musu Allah ya yafe mata nata kura kuren itama.

KHALIL
Daga CID rasa inda ze tafi ya zauna yayi, baze iya zuwa gidan Hajiya ba dan besan me ze gaya mata ba, gidansa kuma ya manto muqullin hannunsa acan SA ba kuma ze iya komawa gidansu Umaimah ya karbi nata ba dan haka kawai ya karya akalar motarsa ya kama hanyar Chilla hotel ze fi masa sauqi ya kama daki acan ya kwanta ko ze samu nutsuwa a jikinsa da zuciyarsa gaba daya. Wayarsa ya fara sakawa a chaji dan ta mutu tuntuni, Seda yayi wanka ya rama sallolin da ake binsa kafin ya zura Slippers din bandaki ya dauki wayarsa da wallet ya fita dan ya samu abinda ze saka a cikinsa da kuma Paracetamol saboda ciwon da kansa yakeyi.
Abubuwan da suka faru sun dagula masa lissafi kwarai, har yanzu daya rufe idonsa Hadiza yake gani yana kuma jin sautin Kukanta me ciwo wanda matarsa ce sila.

Ita kanta Umaimah a dayan hannun yanzun abar a tausaya mata ce. Idan da ace Hadiza ce ko yan uwanta suka shigar da qarar da abinze iya zuwa da sauqi qila a sasanta a gida ba tareda anje gaban Alqali ba amma fa Hukumar Human Right ce gabadaya yanzu ta karbi case din ahannunta, baya tunanin ko ta furta a gabansu cewar ta yafe musu kamar yanda ta gaya masa zasu yarda su janye qarar nan. Dan sauqin da yake da yaqinin zata samu shine idan an samu nasarar kama Khausar kuma ta amsa laifinta wanda ba lallai tayi hakan ba amma koma menene Umaimah ita ta jawa kanta. Rashin tunanita da Baqar zuciyarta su zasu kaita su barota a inda ba zata iya fiddo da kanta ba. Idan ba Mahaukaci ba wa ake cewa yayi barna kuma yayi ba tateda tunanin me hakan ze janyo masa daga baya ba.

Tsaki yaja yana qoqarin kulle qofar ya tuna da ba lallai a ya smau magananin a ciki ba dole seya fita dan haka ya koma dakko muqullin mota. Har ya shiga ya juyo da baya saboda gilmawar wata daya gani kamar Khausar. Saurin mayar da qofar yayi ya kulle ganin sunfara sauka daga benen sunyi qasa a hankali yabi bayansu, tana gaba wani Dogon saurayi fari na binta a baya waya ce kare a kunnenta daga yanayin fuskarta ya karanci cikin tashin hankali take da alama ta samu saqon anje nemanta ne.

Bin bayansu yayi har suka fita yana ganin sun nufi wata mota yayi saurin yin inda ya ajiye tasa motar ya dauka, seda ya bari sunfita kafin yabi bayansu, a sannu yake binsu cikin kwarewar da shi kansa besan yana da ita ba ta yanda babu yanda za'ayi su fahimci ana binsu a baya. Dukda Gajiya da mugun ciwon da kansa yakeyi masa haka ya daure yaci gaba da binsu, Hadeja road yaga sun dauka, to ina zasuje? lissafinsa dai yasan ba zasu bar Kano a daren nan ba,
Amma koma inane baze taba bari su tsere masa ba.

Wani gidan mai daya ga babu kowa ya tsaya ya qara saboda gudun karya qare masa a hanya man motar yayi qasa. Gudu ya ringa shararawa a Titi ko tsoron dare ba yayi da yanayin hanyar da take Titi daya ya ringa tafiya amma ko qyallin motarsu be hango ba, be sare ba yaci gaba da tafiya, yasan dai babu wata hanya da zasu dauke subi indai ba kuma cikin qauyuka suka shiga ba Titin dai yaci gaba da bi harya kai Munjibur basu gamu ba ya gama saddaqarwa sunyi masa nisan da baze iya taddasu ba danhar idan tafiya sukeyi kuma Titin nan suka bi a irin gudun da yayi da ya tarar dasu a hanyar.
Baze yuwu ya juyo Kano a sannan ba dan Goma har ta gota ga muguwar yunwa da ciwon kan da suke damunsa se kawai ya dauki hanyar Munjibur park, canze kwana zuwa da safe ya koma cikin gari.
Chapter 113 · 0% Book details