← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 267

Sashe 143

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KHALIL
Rasa inda ze nufa yayi bayan daya bar gidan ga Dr Sabitu dake ta faman antayo masa kira a waya shi har mamakin yanda yake abu kamar wani qaramin yaro yakeyi. Daman yayi blocking number Zahra, yana ga Mahaifinta ya sanar mata da halin da ake ciki ne data fara kiransa babu qaqqautawa take ya jefa lambar a blacklist.

Shi tun farko ma meya aike shi ya yarda da wannan abunne gashi nan yanzu babu biyan buqata se damuwa da ya jefa kansa duk Anwar ne yaja masa da baqin nacinsa babu yanda beyi akan su haqura ba ya kafe yace su gwada ai gashi nan yanzu basu samu ba kuma sun janyo matsalar da zata iya shafar company su gaba daya.
"Umaimah, Umaimah, ya fada a fili zuciyarsa na tafasa.
Ya yarda Umaimah bata da hankali, tsantsar raina shi da tayi ne kuma tana taking nasa for granted shi yasa har tayi masa hakan tunda ta saba sha idan tayi masa abu ya qyaleta to an gama, baze sake daukar iskancinta ko misqala zarratin ba tunda bata san Annabi ya faku ba toh dole ya saita mata tunani.
Kiran Hajiyarsa ne ya sakashi komawa gida saboda yanda ta bashi umarni duk inda yake yazo tana neman sa.

Dafe kuncinsa yayi yana kallon Hajiya data sharara masa mari abinda ko zamanin yarinta da wayonsa baze tuna sanda ta mare shin ba se yau a shekarunsa kusan Arba'in Hajiyar ta mareshi a tsakar gida gaban ma'aikatan gidansa duk saboda Umaimah. Hadiye wani qululu daya taso masa yayi dakyar Hajiya dake huci kamar ta hadiyi wuta ta ce
"Kana kallona ko nima zaka shaqe nin ne kamar yanda ka kusa hallaka yar mutane iye? Anya Khalil kanka daya kuwa baka fara kora abinda yake gusar maka da hankali ba?" Ta sake fada cikin tsananin fushi.

Kallon su Sammani da sukayi cirko cirko suna nadar gulma yayi kafin kace me sun fashe daga gurin ya juya dakyar ya iya bude baki yace
"Hajiya mu shiga ciki kiga abinda tayi mun"
"Me tayi maka? Har akwai abinda yafi ranta da lafiyarta ne a gurinka" Hajiyan ta fada se ya miqe daga tsugunnan da yayi a gabanta ya shige bangarensu dan a compound ya tarar da ita ta sharara masa Welcome Marin. Bin bayansa Hajiya tayi tana cewa
"Tabbas wuyanka yayi Kauri Khalil wato harni zan maka magana ka tafi ka barni a tsaye saboda ka isa ko?

Shidai be tanka ba kai tsaye ya haye sam, roba ya samu ya zubo takaddun a ciki dan daya taba suke narkewa ya dawo palour inda Hajiya take bambami kamar ta ari baki ya ajiye mata yana kallonta yace
"Takaddun kwangilar da kullum nake ce miki kiyi mana Addu'a ta jiqa, ta kuma goge na cikin laptop dita sannan ta kira wanda ya bamu aikin tayi masa zagi na rashin mutunchi" ya fada dakyar saboda zafin da zuciyarsa take masa.

Tsam Hajiya tayi tana kallon takaddun, kwangilar da iya abincin sadaka da ruwa da akayi akanta bazata iya qayyade nawa suka lashe ba ita ta kora a ruwa haka kuma tabi wanda ya samo musu ta qare masa tanadi akan me?
Ji tayi kamar an kwada mata guduma akai saboda wani tunani daya fado mata, jiyan nan Hajiya Saude maqociyarsu take mata zancen yanzu lalacewar da duniya tayi ba iya mata ake neman lalata dasu ba kafin ayi musu abu harda maza, wani dan Qawarta yaje neman aiki aka ce seya yarda anyi Homo dashi yace ya haqura shine abin basu mamaki suke ta jajantawa karfa ace abinda Khalil dinta yayi kenan shima ya samu kwangilar Umaiman ta gane shine ta lalata?

"Hajiya wanda ya samo mun munyi yarjejeniya dashi akan zan auri yarsa, ranar nan da wancan abin ya faru bina tayi a baya naje gidansu yarinyar shine ta dawo tayi wannan haukan ta fasa kayan dakinta tsaf har ta jiwa kanta ciwo. Shine yau saboda na fada mata gaskiyar abinda yake faruwa na kuma bata tabbacin ba auran yarinyar zanyi ba na karba ne kawai dan na samu kwangilar nan kuma da zarar komai ya kammala shikenan zan rabu da ita shine yarinyar nan tace nazo na karbo mata danwake bayan na fita ta dauki wayata ta kira Dr tayi masa cin mutunchi sannan ta lalata mun takaddun ta goge softcopy din, ko inda zanyi backup bata barmun ba ta goge komai, Hajiya kinsan wahalar dana sha akan aikin nan kuwa? Kinsan tsahon lokaci da kudin dana kashe akan kwangilar nan amma wannan yarinyar ta lalata komai saboda haukan baqin kishinta?" Khalil ya fada idanunsa suka sake rikidewa sukayi jaaa bakinsa da hannunsa suna rawa.

Kasa cewa komai Hajiya tayi dan ita da kanta tasan irin qoqarin da yake akan kwangilar, kullum ne seya nanata mata akan tayi musu Addu'a, haka abincin sadaka tunda aka fara maganar sau biyu akeyi a sati sabanin da da sukeyi Juma'a Juma'a sadakar ruwa da alawa kuwa basa yankewa akwai masallaci a layin gabansu hade da Islamiyya can ake kaiwa kullum asha ayi alwala yara kuma a raba musu alawa
(Sadakar ruwa nada matuqar tasiri yan uwa mu daure koda sau daya a sati ki siya akai masallacin mutane suyi alwala haka alawa a ringa rabawa yan yara Sadaka maganin Musiba ce).

Gwauron numfashi ta sauke kafin a sanyaye tace
"Dukda haka wannan be kai ace ka shaqeta ba Khalil idan wani abu ya sameta fa me zaka cewa iyayenta? Akan ka rasa kwangila ka illata musu yari ya kome, ina rabaka da wannan zuciyar idan rai ya baci ai hankali ne yake nemo shi kuma abinda be faru ba shi ake gudu wannandaya rigada ya faru sedai ayi adfu'a Allah ya taqaita na gaba bata kyauta ba kaima kuma beci kayi hakan ba tunda kasan idanta sani ranta ze baci"

"Ranta ze baci Hajiya? Yanzu bacin ran Umaimah kike gudu akan Asarar dani ta janyo mun?" Khalil ya fada cikin zallar mamakin Hajiyar tasa seta gyara zama tace
"Ba haka nake nufi ba, gani nayi kuna zaune lafiya da matarka wata matsala bata taba giftawase irin haka ta faru tunda kasan zafin kishin matarka se kayi haquri da duk wani kule kulen mata tunda babu abinda ta rageka dashi koba haka ba?"

"Babu abinda kika sani akan zamana da Umaimah Hajiya ban kuma san dalilinki na bin bayan duk abinda take aikatawa ba amma inajin tsoron ranar da haukarta zata gifta ta kanki" Khalil ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se ta miqe jiki a sanyaye tana cewa
"Asibiti zan koma na gano yanda take ka tashi muje tare dan iyayenta sunzo nasan dole zasu buqaci jin abinda yasa kayiwa yarsu haka"

"Kiyi haquri Hajiya amma bazan iya zuwa ba, kuma daga can ta wuce gidansu bana buqatar ta sake dawomun cikin gidan nan" Ya fada se Hajiya data fara tafiya taci burki baki na rawa ta kalleshi tace
"Karka ce mun sakinta zakayi Khalil akan abin duniya me faruwa ya qare zaka saki matarka da tun baka dashi take tareda kai?"

"Ni ban yanke hukunci ba amma idan kika matsamun naje inda take a yanzu zan iya furta abinda duk baze mana dadi ba, ta tafi gidansu kawai" ya sake fadawa Hajiyan daga haka ya miqe yana tafiya dakyar ya haye sama kansa ne yake masa ciwo kamar me, ga Dr Sabitu shima kamar m kwantaccen kai se kiran sa yake a waya yana iko masa da Text kala kala, Threatening nasa yake akan seya saka an kwace masa Licence din company, seya lalata masa career ta yanda sharar fili baze samu a bashi ba ballantana gini kai shirme dai kala kala gashi nan.

BAYAN SATI DAYA
Uncle din Anwar daya yi musu hanyar ganin Dr Sabiyu shiya shiga ya fita dakyar ya kashe wutar dake tsakanin su Khalil da Dr Sabitu bayan ya kai masa burbushin takaddun daya ajiye suka bushe, Khalil ya roqi daya maido masa da copy din proposal da paper work din da yayi submitting tunda bashi zeyi aiki ba se a maido masa da basirar sa da wahalarsa Dr Sabitu ya banka masa harara ba tareda yace komai ba haka suka baro gidan zuciyar Khalil na masa zafi, idan ya tuna wanine ze mori wahalar sa se yaji kamar yayita kurma ihu irin basirar daya zuba a gurin tsara yanda ginin ze kasance ba kadan bace amma yanzu a bagas wani ze mori abinda yayi wallahi Umaimah ta cuce shi.

Wayarsa ce ta shiga qara ya zarota a Aljihu ganin me kiran ya sakashi daidata muryarsa kafin ya daga.
"Barka da Rana Alhaji" ya gaida Aminin Mahaifin nasa daya kirashi Alhaji Garba daga daya bangaren yace
"Barka dai Ibrahima ya gida ya mahaifiyar taku?"
"Lafiya lau Alhaji" ya sake fada kafin yayi shiru se Alhajin yace
"Waliyyin matarka ne ya kirani a matsayina na waliyyinka, yace kusan sati daya kenan ashe matarka tana can gidansu shine suka kira suji ma'anar zaman nata saboda tunda ta koma kamar yanda sukace daga Asibiti aka sallameta ko basuji komai daga gareka ba".

Numfashi yaja kafin yace
"Eh hakane Alhaji, sabani muka samu na barta ta zauna ne a can zuwa wani lokaci kafin muga yanda hali zeyi"

"Wace irin magana ce haka Ibrahimu kamar yaya yanda hali zeyi jingine musu yarinya zakayi ba tareda tasan matsayinta ba kenan se sanda kayi ra'ayi tukunna?" Alhaji Garba ya fada se Khalil yayi shiru dan be san me zece masa ba, shidai wallahi baze dawo da Umaimah yanzu ba se ya gama jinyar asarar data janyo masa sannan
Chapter 143 · 0% Book details