← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 267

Sashe 207

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kutumar bura ubanka ce ta faru Khalil, ka bude mun qofar idan ba haka ba wallahi har kaje lahira kana dana sanin abinda zan aikata maka Maci amana Macuci" Umaimah ta fada cikin hargagi.

An rigada an kai gabar da bayajin komai dan Umaimah ta zageshi, a yanzu tashin hankalin sa daya ne, idan ya bude qofar ta shigo taga Humaira besan me zata aikata ba haka idan yaqi budewar nan ma besan me zata yi ba waima ta yaya akayi ta farka har aka sallameta daga Asibiti tsakar daren nan wannan wane irin bala'i ne haka.

"Khalil bazaka bude bako? Shikenan ka zauna a ciki kaida Yar iskar Karuwar da ka dakko amma ka jirani na dawo zakaga abinda zanyi" Umaimah ta sake fada kafin ta juya dakyar take daqa qafa ta sauka qasa. Tana jin ana buga qofar kuma ta tabbatar da Sammani ne ze taso yan cikin gidan amma bata kukasu ba ta wuce.

Kitchen ta nufa, zuciyarta ta rigada ta gama qeqashewa abinda ta ayyana mata tayi kawai shi zatayi kota mutu ko ta rayu wannan duk ba damuwarta bace amma dole ta koyawa Khalil hankali na cin Amarta da yayi.

ASIBITI

A nutse Mama ta fito daga bandaki bayan data dauro alwala taja qofar ta rufe a hankali gudun karta tashi Umaimah. Kai tsaye idonta ya sauka akan gadon da Umaimah take kwance se taga babu kowa, da mamaki ta qarasa Gurin ta daga bargon dai dagaske bata nan.

Hijabin ta ta zura ta leqa waje ta tambayo ko Ma'aikatan ne suka dauki Umaiman tunda daman sunce akwai gwajin da za'a mata amma ta dauka ai seda safe.

Bacci sosai ta tarar da Nurses din sunayi abinsu, seta qarasa kusada wadda take kula da Umaimah ta shiga tashin ta, Nurse Halima ta farka bakinta dauke da salati ganin Mama a tsaye yasakata wartsakewa tana cewa

"Aa Mama badai jikin Umaiman bane? Muje na dubata mu gani se a taso likita"

"Ba ku kuka dauketa ba ne Nurse? Na shiga alwala na fito yanzu banganta a dakin ba" Mama ta fada cikin firgicin jin maganar Nurse, to ina Umaimah zata tafi a daren nan ita da ba lafiya ba?

Kafin kace me Asibiti ya hargitse ana neman Umaimah daki daki, da yake Asibitin  ba wani girma ne dashi ba cikin dan lokaci suka bincike ko ina amma babu Umaimah babu me kamar ta har Get an tambayi masu gadi sukace basuga fitar kowa ba zuwa sannan tuni Mama ta fara kuka, wayarta ta dakko ta shiga kiran Abba ta gaya masa halin da ake ciki seda ta kira sau biyar kafin ya daga wayar.

GIDANSU UMAIMAH
A daidai sanda Mama take kira Anty Saratu ta farka yin fitsari, da yake wayar a vibration take bata ji ba, seda ta yiwo fitsarin ta dawo, dakyar take bude ido saboda bala'in baccin da take ji to kusan kwana biyar kenan a jere baccin su ragagge ne ko yau din se gurin qarfe daya suka dawo gida daga Asibitin kafin ta kwanta biyu tayi.

Hasken data hango wayar Abba tayi ya saka ta miqa hannu tana hamma ta jawota dan tasan qila Alarm din nasa na fama ne ze fara kadawa ya hana mutane bacci, sunan Maman Yara da ta gani ya saka fara tashin Abban ya yi juyi yana cewa

"Ohni Saratu wai me kuma kike so dan Allah ki barni na huta mana idan dai ba so kuke ku qarasani na mutu kawai ba"

"Alhaji Maman ce take kiran ka a waya, ina ga jikin Umaimah ne fa" ta fada tana miqa masa wayar, seya karba da sauri ya saka a kunne, Mama ta fashe da kuka tana cewa

"Alhaji An sace Umaimah, daga na shiga Bandaki nayi Alwala na fito babu ita a dakin gashi mun duba ko ina amma ba'a ganta ba".

"Kamar yaya ba'aga Umaimah ba? Ita Umaiman Allura ce ko me da za'ace ta bata wannan ma ai zancen banza ne, jira gani nan zuwa" Alhaji Sabo ya fada yana miqewa tsaye, jiri ne ya jashi ya koma dabas ya zauna da sauri Anty Saratu ta taro shi tana cewa

"yi a hankali Alhaji kasan kaima fa ba lafiyar ce dakai ba"

"Ba'a ga Umaimah ba Saratu, wannan abu har ina daga wannan tashin hankali se wannan kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miqomun riga ta muje Asibitin mu gani".

"Ba'a ganta ba kodai wani gurin ta shiga taya za'a ce baa ga mutum ba a Asibiti Ahaji sudai duba dakyau ko bayan gida ta zaga" Anty Saratu ta fada tana miqa masa jallabiyya se ya karba ya hau kici kicin sakawa amma ya gagara saboda yanda jikinsa yake rawa.

"Saratu bane babbar riga ki gani na dora zata fi mun sauqi" ya fada yana zama a bakin gadon ya dafe kansa da hanna ye biyu, al'amarin Umaimah nema take yi ta kashe su kawai ta huta dan ya tabbatar yanzun da kanta ta tashi daga Asibitin wannan kadan ne daga aikin ta.

Tareda Salman suka fito daga gidan, Salmanun ne yake jan motar. Seda suka hau titi ya kalli Abban yana cewa

"Abba ya kamata a sanar da Yaya Khalil fa yasan halin da ake ciki?"

"A kyake shi kawai Salmanu muje mu gani idan ba'a sameta ba sannan se mu sanar musu" Abba ya fada yana rufe baki wayar Salmanu da take gefensa ta fara qara, seya cirota yana duba.

"Lah Abba kaga Yaya Khalil din nema qila toh yasan abinda yake faruwa" Salmanu ya fada yana daga wayar ya sakata a speaker.

"Salman ku taimaka mana, ga Umaimah nan tazo ban san me zatayi ba tace na bude qofar dakin da muke ciki idan ba haka ba se tayi abinda har naje lahira ina dana sani. Tsoro nake ji karna bude tayi mana wani abun kuma idan ban bude din ba bansan me zata aikata ba" Khalil ya fada cikin rawar murya dan da gaske ya gama karaya da lamarin Umaimah. Ya shaida yar daba ce ta gaske, a HALIN KISHI irin nata za ta iya aikata masa duk abinda zuciyarta ta raya mata tunda ai ba yau ta fara ba.

"Muje gidan, bari na kira Maman ku na gaya mata, yanzu ita wannan yarinyar bazata bar rayukan mutane su huta ba ko? Ai Shikenan" Abba ya fada yana latsa waya.

Sanda suka isa sun tarar dasu Hajiar su Khalil a tsaye har sannan Sammani da Halifa na qoqarin buge qofar amma abu ya gagara saboda qofar ba ta wasa bace, Cikinsu Salmanu ya shiga suka ci gaba da kici kicin, Abba na kusada Hajiya da ta kasa cewa komai ya na bata baki.

Kamar an ce Habiba ta waiwaya ta hango haske ta gurin qofar Kitchen ta baya, hannun Hajiya ta janyo da qarfi ta nuna mata suka yunqura zasu tafi gurin Abba ya dakatar dasu da yi musu alamar kar suyi motsi ya fara sanda a hankali har ya isa gurin da Umaimah take kiciniyar kunna cylinder Gas saboda duk dare suna kashe ta ne daga wajen idan zasu kwanta gudun tsautsayi, ko wani abun zasuyi sedai suyi amfani da electric.Abba na zuwa kuwa ya shammaceta beyi wata wata ba ya dauke ta da marin da seda taga taurari a idonta Halifa dake bayansa yayi azamar kashe Gas din data kunna dan sosai suka jiyo qarar fitar sa daga Kitchen din alamar ta zare pipe din ne yana fita kaitsaye.

"Me kike yi Umaimah" Abba ya fada ciki matuqar bacin rai yana dubanta.

"Igiyar Gas na cire daga jiki, zan sake shi ya cika gidan sannan na kunna mana wuta dani dasu dukka mu qone dan wallahi da nayi zaman KISHI da wata mace akan Khalil gara mu mutu, kuma yanzun ma ba fasawa nayi ba, ko ba yau ba wallahi se na kashe ta, na kashe Khalil sannan na kashe kaina" Umaimah ta fada babu alamar wani tsoro ko nadama a fuskarta.

Duka Abba ya sake kai mata a zuciye kafin ya angizata suka shige cikin gidan Hajia ta tare tana cewa
"Kayi Haquri Alhaji kodan halin da take ciki, Umaimah me yasa kike haka me yasa bazaki bar mu mu huta ba ki dauki haquri da dangana dan Allah?"

"Karki sake taba ni munafuka Annamimiya, idan da kina so na haqura ai tun farko seki hana danki yin auran tunda yana jin maganar ki amma saboda baqin munafunci kika mara masa baya yanzu kuma kizo kina bani haquri se kace ke har naki mijin ya mutu kin bari anyi miki Kishiyar.
To wallahi bazan fasa abinda nayi niyya ba kuma duk wanda yayi yunqurin hanani se ta shafe shi Idan yaso kowa ma ya mutu a huta" Umaimah ta fada tana fizgewa daga ruqotan da Hajia tayi, ta sake yunqurawa kafin su ankare har ta kai matattakalar benen kai bazakace ciki wata tara ne a jikinta ba a yanda take tafiya.

A daidai lokacin Khalil ya fito tareda Humairah dake sharbar kuka a bayansa ta tsorata sosai ta gama saddaqarwa yau kwananta kawai ya qare a gidan, Umaimah na hangota ta kai mata wata muguwar cakuma ta goce, mantawa tayi da duk wani ciwo da take ji a jikinta ta ware qafa uku uku ta hada matakalar ta diro qasa tana ganin mutane da mugun gudu tayi bayana Hajia tana sauke numfashi.

"Ka fito ko to kuwa ka shirya baquntar lahira yanzu Khalil sena kashe ka" Umaimah ta fada tana daukar Abin flower da yake akan benen ta nufi Khalil da yayi mutuwar tsaye gadan gadan, tana dagawa marata ta katsa mata ba shiri ta wullar da abin hannunta ta dafe ciki tareda durqushe wa Khalil yayi kanta kafin ya qarasa taja baya tana cewa

"Karka taba ni munafuki karka kuskura qazamin hannunka ya tabani kuma ba barinka nayi ba se naga bayanka da duk wata mace da kace zaka hadani da ita"

"Kai Khalil wuto daga nan ka rabu da ita" Abba ya daka masa tsawa kafin da kansa ya hau benen ya kamo hannunta, tana tirjewa da komai seda ya direta a tsakiyar palour sannan ya qyaleta.

Idanunta da suka rigada suka qeqashe ta daga tana binsu daddaya da kallo kamar yanda suma suke kallonta ko wanne da kalar tunanin da yakeyi akanta.
Chapter 207 · 0% Book details