← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 267

Sashe 166

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kika sake shiga sabgata se naci kaza kazan ubanki" ta dannawa yari yar ashariya ita dai bata waigo ba haka Baban Asad daya tasata gaba suka fice daga gidan. Masifa Hajiyayyen ta shiga surfa mata tana cewa ta wulaqantata a gaban baquwa yanzu zata tafi da ita tana cewa yar uwarta bata da mutunchi
"Ina budurwarsa ce ya kawo miki ita har cikin gida kike washe mata baki baki dauki tabarya kin raba kan yar bura uba biyu ba?" Umaimah ta jefa mata tambaya seda ta harareta kafin tace
"Budurwarsa ce se akayi Yaya? Dan kiji da kunnenki ma an saka musu rana wata shida masu zuwa zata zo gidan nan mu zauna tare".

Tsaki taja na tsabar takaicin Hajiyayen ta miqe tana cewa
"Idan har wannab rashin zuciyar Mama take cewa na koya a gurinku to wallahi bazan iya ba, in zauna Namiji ya takani, saboda tsabar rashin mutunchi ya dakko mun mace har cikin gida da sunan tazo gaisheni ko? Na rantse da Allah da nice sedai uwarta ta haifi wata, fetur zan zazzagawa yar iska na qoneta tas yanda zata zama izina ga sauran mata masu kula mazan mutane"

"Ai kuwa da kema a tsakiyar kasuwa za'a ratayeki bayan an feraye miki naman jiki saboda ki zama izina ga sauran mahaukata irinki" Maman Asad ta fada tana jifanta da wani mugun kallo juyawa tayi ta fice tana cewa
"Wallahi dana san abinda zan tarar kenan da banzo ba, ina neman maganin matsalata haka kawai nazo na sake haduwa da wani ciwon zuciyar ai dai Yah Hajiyayye kinyi asara wallahi kuma mata kika rako duniya".
Ita dai Hajiyayye da kallo ta rakata harta fice daga falon kafin ta koma ta zauna akan kujera tayi shiru, idan tace ranta be sosu da zuwan budurwar Baban Asad ba tayi qarya. Kamar wasa ta fahimci ya qulla alaqa da wata a waje, da ta kwantar da hankali tayi amfani da wayo da fikira se gashi da kansa ya fito ya gaya mata yana neman aure har ya sanar mata da wacece yarinyar ya na hadasu a waya suna gaisawa kuma koda wasa bata taba nuna masa damuwa akan hakan ba. A kullum addu'arta Allah yasa su zauna lafiya da koma wacece ze kawo cikin gidan, abinda yake shirin yi ba haramun bane haka tashin hankalinta baze hana ba dan haka ta zabi da dayi haquri ta kuma maida komai nata ga Allah shiya qaddara qarin auran tana fatan ya sanya zaman lafiya da lumana a zaman su.

Hajjaju Umaimah kuwa tana fita gidan Safinah ta nufa, wato Mama so takeyi ta zama lusara ta zauna namiji ya takata son ransa shiyasa tace duk damuwarta ta ringa sanarwa da yan uwanta su zasu nema mata mafita irin wannan sakarcin da sukeyi take so itama ta koya kenan kome? Kamar yanda ta zauna Anty Saratu take baza sharafinta a cikin gidansu da sunan ita ga Amarya haka take so kenan itama ta zuba ido tana zaune Khalil ya kawo mata wata su rabashi tare kenan ai kuwa hakan baze yuwu ba, dole ta tashi tsaye duk kuma yanda zatayi seta hana faruwar hakan.

Horn ta ringa fafarawa a qofar gidan Safina kusan minti goma kafin aka bude qofar. Mijinta ne da kansa suka gaisa bayan ta ajiye motar ta shiga ciki har Bedroom din Safina ta tarar da ita tana kwance daidai akan Gado tana shan fruit salad ga waya a hannunta tana chatting.

"Yanzu tsabar rashin mutunchi kina jina ina ta horn amma baki saka an bude mun qofa ba" ta fada tana cire Hijabin jikinta dan ya dameta se Safina ta miqr zaune tana cewa
"Yi haquri qawata, na aiki Ado Baban Maya nace yazo ya bude miki na manta kuma yana soya mun Irishi inaga shi ya tsaya kwashewa kafin yazo ya bude".

Seta saki baki tana kallon Safina jin abinda take fada. Baban Maya da soya dankali daman tasha Mamakin bude mata Get da yayi mutumin da a izza irin tasa ko shine ya dawo gidan me gadi baya nan sedai Safinan ta fito ta bude masa amma yau shiya budewa baquwarta qofa. Kwankwasa qofar akayi Safina ta bada umarnin shigowa se gashi dauke da Try ya doro Irish din daya siya ga kuma butar shayi da kwanon sugar. Hijabinta taja ta rufa ya ajiye kayan ya tsaya yanda kasan dan aiki yana tambayar Safinan ko da abinda take da buqata ne ta wani yamutsa fuska tana cewa
"Babu komai daman Toilet dina nake so a adauraye amma ka barshi idan na tashi ko zuqa Anjima na wanke".

Jikinsa na rawa yace bari ya wanke, Umaimah ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah ya shige kuwa ya hau wankin toilet din ita dai yau ta fito a Sa'a daga ganin abin Takaici sena Mamaki wani na bin wani. Seda Alhaji Lawal ya wanke Toilet tas kafin safina ta sallameshi ya fita, Umaimah ta rakashi da kallo Maganar Safinan ta maidota hankalinta tana cewa
"Qawata me kike kallo ne haka ina magana har bakya jina?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Hmm abin mamaki na gani wai dagske Baban Maya ne haka ko kuma wani dan aiki kika samu me kama dashi?"
Dariyar shaqiyanci Safinan ta kwashe da ita kafin tace
"Shine nan Lawal dai da kika sani daman ai na gaya miki duk Wanda yaci tuwo dani miya yasha, kuma jada baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne. Lakwa lakwa na musu daga shi har yan uwan nasa da suke zugashi na shirya a nutse, gashi dana farka na taso musu gaba daya nayi maganin yan iska yanzu Lawal da Ahalinsa kafin da suka isa dashi kara idan na ajiye basu isa su tsallake ba wallahi se yanda nace haka za'ayi ai Allah ya jiqan Malam na kan tudu badan ya mutu ba haqurin nan dai da yake ta cewa na qara zanci riba a gaba gashi na gani, na ci wuyar jira amma da aiki ya kammalu yanzu dadinsa kawai na kwasa".

Tagumin da tayi ta janye tana kallon Safinan dan sam ba gane kan surutanta takeyi ba tace
"Kinga ba wannan ya kawoni ba qata wutar ce take shirin kunnomun Khalil neman aure yakeyi har kuma yana iqirarin babu abinda ze hanashi. Bana son nayi tashin hankalin da ze sake saka ran Mama ya baci shiyasa kika ga nazo da yamman nan ki bani mafita, me zanyi na watsa al'amarin tun kafin yayi girma dan wlh wannan karon da gaske yake a gabana ya shirya ya tafi zance gurin yarinyar babu wata shakka ko tsoron bacin raina da yakeyi a baya ya kalleni yana gaya mun gurin wata zeje Khalil fa Safinah Khalil dina ke iqirarin ze auro wata ya kawo cikin gidan da nake" seta dafe kai ta fashe da kuka tana cewa
"Wallahi ji nakeyi kamar zan haukace, na je gidan Maman Asad na kai mata kukana na tarar da baqin cikin daya fi wnada na baro kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

Ido Safina ta saka mata har ta kai qarshr kafin ta kwashe da dariya harda kwanciya tana cewa
"Kice abin yazo inji me tsoron wanka".
Dakatawa tayi da kukan ta kalli safina a fusace tace
"In gaya miki damuwata ki maidashi abin dariya saboda wukaqanci? Koda yake laifi nane dana zo na fada miki" tana gama fada ta miqe ta shiga kici kici da Hijabinta zata saka.

"Haba qawata daga wasa kuma se ki maida abun zafi" Safina ta fada tana riqe hannunta, Umaimah ta fizge dan taji haushin abinda ta matan Safina na qunshe dariya ta samu ta zauna tana ce mata
"Toh kiyi haquri"
Banza ta mata tana jan hanci, Safina ta gyara zama tace
"Yanzu kinyarda da abinda nake gaya miki da nace miki Maza duk sunansu Maza karki taba bugar qirji akan Namiji kice bazeyi abu kaza ba sedai idan lokacin yin beyi ba. Gashi nan kina kwance ze tattago miki tashin hankali, lokacin da nace ki tashi a tsaye ki kamashi ta yanda babu wani motsi da ze iya se da yardarki me kikace ke kinsan Mijinki kin yarda babu macen da zata burgeshi bayan ke toh ai yanzu da kikaji daga bakinsa na tabbatar ba qarya ya miki ba Allah nema ya soki da rahma kikaji da sedai azo ana ki matsar da kaya za'a zuba na Amarya qila".

"Kinga Safina ni ba cewa nayi ki qaramun damuwa ba, mafita na nema idan baki da ita ki barni na tafi"
"Mafita kam a kwaita sedai ke dince nasan zaki iya cewa ba haka ba, amma idan kin shirya ganauce dai ke ba jiyau ba kinga yanda na samu kan Lawal idan kina son haka koma abinda be kai haka ba mintina kadan ne kn samu biyan buqatarki"

"Kinga ni wannan abin ba burgeni yayi ba ta yaya zaki maida Mijinki Bawa ni aurene bana so yayi shi nake so a fasa ta sigar da baza'a ga laifina ba, badan Mama ba wallahi da yanzu na gano gidansu koma wace shegiya ce naje na qare musu tanadi ta yanda bazasuyi gigin bashi auran yarsu ba. Kawai yanzu ki gayamin idan da wata hanyar me sauqi da zanbi" Umaimah ta fada cikin qaguwa se Safina tayi fari da ido tana kallonta tace

"Yo wannan ai yafi shan ruwa wahala bama se kinje da kanki ba, a waya kawai zan kira Malam yanzu kiga aiki da cikawa sedai ki aika masa da abin sadaka ta Account kawai"

"Banda Harkar Malamai kinsan bana so" Umaimah ta fada, se Safina ta watsa hannu tace
"To nidai a bangarena taimakon da zan iya yi miki kenan na hadaki da wanda ze miki aiki bayan nan banida wata Mafita Sayyada Umaimah".

Shiru tayi tana kallon Safinan, itafa bata yarda da wasu Malamai ba gani takeyi cinye musu kudi kawai suke suna musu qarairayi kuma ace abu sedai kayi tayi ita ba zata iya ba, tafi gane ta dauki mataki da kanta kawai a wuce gurin
Chapter 166 · 0% Book details