← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 267

Sashe 162

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aa yanzu kuma? Yaushe ne kike cewa kedai kin matsu ki ganshi seda zezo kuma kice wani ba haka ba saboda gulma" Khalil din ya sake fada seta rufe fuska kamar tana gabansa a ranta tace
"Shi komai mukayi magana s ya gayawa Yah Khalil" a fili kuwa tace masa
"Ni dai Aa, indai be fito ba kace ya bari ba yau ba wannan ma ai kwange ne dan kwanakin basu cika ba ai".

"Toh sedai idan kin fita ki gaya masa dan gashi nan yamun Text cewar ya iso yana qofar gidan, kiyi masa iso".

Ba shiri ta kashr wayar qirjinta ya shiga bugawa jin cewar ya iso, ta rasa me yasa take ta faduwar gaba akan haduwar tasu, ita dai ba zata ce bata damu dashi ba dan tasan ba wai Sonsa ta fara ba kawai tana jin dadin hira dashi kuma bata so su dena magana shiyasa ma tace ya bari se ya dawo daga tafiyar duk ma lokacin da ze dauka acan.

Qarar wayarta ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi, Noor ne, gabanta ya sake faduwa data tuna sunyi dashi zezo tasan kuma ya iso din ne shiyasa ya kirata dan Habibu yana gida yazo hutu shi kuma baya shigowa cikin gidan idan Habibu na nan dan basa ga maciji da dai baya nan daman a falon Mama ake hirar kosu saka kujera a tsakar gida.

A salube ta zura Hijabin da tayi sallar La'asar ta fita, babu batun tsayawa gyara fuska duk irin burin da ta ci na shan kwalliya randa zasu hadu da Ibrahim har kayan da zata saka ta ware su ta ajiye amma shirinya rushe. Mama na zaune tana Lazumi ta fito, da kallo ta bita ganin yanda take jan qafa fuska kamar me zazzabi tace
"Ke se ina haka kike jan qafa kamar me ciwo?"

Dakatawa tayi tana kallom Maman tace
"Abokin Yah Khalil ne yazo"
"Abokin Khalil? Ina gobe kika ce ze zo har na bawa Maryam tayi masa kayan kwalama kuma in shi din ne haka zaki fita da farar fuska qozai qozai kamar wadda ta tashi daga jinya?" Mama ta fada tana tashi tsaye daga inda take seta sake narke murya kamar zata fasa mata kuka tace
"Nima bansan ze zo yau ba kawai kirana yayi wai gashi nan zuwa goben zeyi tafiya, kuma ni munyi magana da Nuru zezo yana waje ma shima ya kirani".

Se Mama ta tafa hannu tace
"Ni Asiya naga ikon Allah. Yanzu saboda Allah kinsan mutum ze zo gurinki tun dazu ba zaki tashi ki gyara ba haduwar farko zaki fitar masa a haka kamar wata tsintacciya? Shi kuma Noor din da kika gayyato na magani da menene? Da yace miki ze zo ba zaki ce masa Aa ba?"

"Nifa Mama bansan yau zezo ba, seda muka gama magana da Nuru kafin shiya kirani nama kira Yah Khalil ko zece masa ya dakata yace wai ai ya kusa qarasowa ma da tare zasu zo" Humairan ta sake fada se Mama ta aika mata daquwa tana cewa
"Ba Nuru ba Fitila ma taci gidansu. Wuce ki cire wannan Hijabin kamar me takaba ki nemi kayan Arziqi ki saka kuma ki gyara fuskarki, shi Nuran zan saka Habibu yanzu ya korashi in Baqon ya tafi ya dawo kuci gaba da shashanci da batawa juna lokacin" tana gama fadar haka ta shiga kwalawa Habibu dake cikin daki kira.

Juyawa Humaira tayi dakinta dan tasan Mama ba zata bari ta fita a hakan ba tunda tace, ta bude Wardrobe din kayanta tana kallonsu, bata ma bi takan kayan da tayi niyyar sakawa ba ta zaro wata Abaya baqa Mansur ne ua aiko mata dasu kwanaki. Hijabin Jikinta ta zare ta mayar da Abayar. Ribbon din data daure gashinta me tsaho da santsi irin na Asalin fulani ta zare ta sake matse gashin ta mayar dan bata da lokacin tajewa, bama tason taba kan se dole zafi yake mata.

Farar hoda ta goga da Vaseline a bakinta kafin ta qara turare kadan dan bata jima da wanka ba ta shafa turare kuma, mayafin rigar ta rufe kanta dashi, qirjinta ya buga sanda taga kiran Noor, hannu na rawa ta daga wayar tasan za'ayi haka muryarsa a hade cikin fushi yace
"Da kinsan kina aiki me yasa zaki ce nazo kinsan daga inda na taho yanzu kuma ba zaki gaya mun da kanki ba se ki aikomun wancan Ajawo din yazo yanawa mutane hayaniya wallahi ki ja masa kunne ya kiyayi randa zamu hade dashi kuma karki kuskura ki kirani" be bata damar cewa komai ba ya gama bambaminsa ya kashe waya. Ta maida wayar kan mudubi jikinta na daukar rawa yanzu tasan yayi fushi kafin kuma ya sakko se Allah saurin da take tayi akan ta fita ita ta lallabashi ya tafi kafin Yah Habib yaje dan tasan daman seya ja mata gashi yanzu yace karma ta sake kiransa.

Goge kwallar data ziraro mata tayi jin Muryar Mama tana shirin shiga dakin, Maman ta shigo ta kalleta yanda taga fuskar Maman kamar wadda aka biyawa aikin Hajji ya bata mamaki amma tayi shiru
"Kina nan tsaye kina solobiyancin naki ga mutum zaune yana jiranki, yi maza da Allah ki fita in banda ma Allah me kyauta da qari har ina ke ina shi koda yake Addu'a tace ta karbu kai Allah na gode maka".

Ita dai bin Mama tayi da kallo danbata fahimci inda zancenta ya dosa ba, wannan murna da takeyi kuwa itama bata san ta mecece ba sedai jin da tayi tace baqon yana jiranta ta gane ciki suka shigo dashi kenan, to ko Mama tasan shi ne? Zama ta sanshi tunda shima Abokin Yaya Mansur ne. Tsaki taja a fili ta fito ranta babu dadi duk wani zumudin ganin Ibrahim ya disashe mata saboda batawa Nurun ta rai da akayi. Ji tayi bugun zuciyarta ya qara sauqi ta tsaya daidai corridor da ze fitar da ita daga inda dakunan su yake zuwa cikin falon tsabar yanda gabanta ke tsinkewa seda ta dafe qirjin da hannu biyu. Muryar Khalil take jiyowa qasa qasa yana magana da alama waya yakeyi, wannan ne ya bata kwarin guiwar daga qafarta taci gaba da tafiya kenan ba shi kadai yazo ba amma da Yah Khalil yace baze rakoshi ba.

Kanta a qasa kamar farin shigan munafunchi ta shiga falon da sallama. Daga bakin qofar ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya, ganin Khalil din shi kadai a zaune yana waya yasa ta qarasa shiga ta samu kujerar gefensa ta zauna qirjinta naci gaba da bugawa a gefe kuma tana satar kallonsa yanda yayi kwalliya yasha shadda kamar wani sabon Ango se zuba qamshi yake ga Turanci yanayi yanda kasan Rainon Ingila. Seda ya qara kusan minti biyar bayan ta zauna kafin ya kashe wayar yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi.

Murmushin itama tayi ta shiga gaisashi ya amsa yana kallonta sukayi shiru na dan lokaci Humaira ta waiwaya ta kalli qofa, so take ta tambayeshi ina Ibrahim amma tanajin kunya dan haka ta mayar da kai qasa tana wasa da zoben hannunta. Khalil kuwa ido ya zuba mata yana sake qare mata kallo a yanzu ne yake sake ganin quruciyarta yarinya ce sosai kodan da da Jilbab yake ganinta shiyasa take dan cika masa ido? Lallai se abar zuciya idan ba haka ba shi da yake da cikakkiyar Mace ta ko ina me zeyi da wannan yar yarinyar.

"Yaya, naganka kai kadai" Humaira tayi maganar a hankali ganin kusan minti goma ya zura mata ido bece komai ba, komawa yayi ya jingina da kujerar da yake kai sosai ya sake zuba mata idanunsa da suka saka taji zuciyarta na tsinkewa ga wata sabuwar faduwar gaba da takeji seta miqe tsaye danbazata iya cigaba da jure kallon da yake mata ba Khalil na ganin ta miqe shima ya miqe da sauri ya tareta ganin tana neman barin falon yace.
"Ina kuma zakije?"

"Uhm ruwa zan sha" ta bashi amsa tana ja da baya tareda rarraba ido saboda yanda ya matsota. Da ido ya mata nuni da ruwa da Lemon da aka kawo masa seta hadiye yawu dakyar tace
"Daman na manta wayata ne a ciki zan koma na dakko"
"Koma ki zauna" ya fada yana sake tsareta da ido, kamar kuwa zata fasa masa kuka haka ta tabe fuska ta koma inda ta tashi ta zauna. Allah ya sani wannan kallon da yake mata ita tsoratata yakeyi kuma shi Ibrahim din ina ya tsaya da har yanzu be qaraso ba bayan yace ma ba tare zasu zo ba.

"Aisha" ya kira sunanta da wani sauti da seda tsigar jikinta suka zuba, sautin muryar da Ibrahim yake mata magana taji dan haka ta daga kai a hankali ta kalli bakin qofa dan taga shigiwarsa amma bata ga kowa ba.
"Aishatu" ya sake kiranta da ainihin yabda Ibrahim din yake kiranta gaba daya ta shiga rudani, me kenan hakan yake nufi? Wannan Yah Khalil ne amma ya akayi yayi muryar Ibrahim har ya kirata da sunan da shi yake kiranta.

"Aishatu, na kasa zurewa na jira har zuwa gobe, son ki yayi mun yawa idan na wuce yau banji matsayina a gurinki za'a iya wayar gari a ga na sheqa Soyayyarki tayi Ajalina" ya sake fada kansa tsaye yana kallonta, yanda take mutsu mutsu ya tabbatar masa da ta shiga rudani.
Humairah kuwa wannan karon a mugun firgice ta daga kai ta kalle shi jin abinda yake fada, kasa fassara maganar sa tayi dan haka tace kawai tace masa
"Ina Ibrahim?" Shi kadai ne amsar da take da buqatar ji a yanzu
"Gani" ya bata amsa kai tsaye seta ware ido akansa tana kallonsa jin abinda yace
Chapter 162 · 0% Book details