Sashe 78
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼
Page 34
Har wayar ta qaraci ihunta bata daga ba, ya sake kira nan ma haka, ajiyar zuciya me qarfi ya saki ya zari tissue ya goge zufar sata tsatstsafo masa a goshi dukda Ac motar a kunne take. Key yayiwa motarsa ya koma kan titi yaci gaba da tafiya. Tunawa da yayi beyi sallar La'asar ba dan yana qofar gidansu Hadiza aka kira yasaka shi neman Masallaci akan hanya yayi sallar sa. Tunanin inda zeje yakeyi, kamar ya koma gidan Hajiya sa seya tuna tace masa zataje barka matar dan qawarta ta haihu haka nan ya yanke shawarar zuwa ya gaida Mama babu bata lokaci ya kama hanya.
Seda ya tsaya yayi musu tsaraba kamar yanda ya saba baya tana zuwa gaida surukan nasa haka nan ko babu yawa seya riqe wani abun. A qofar gida ya hadu da Yaya Aminu wanda shima zuwansa kenan suka gaisa kafin suka shiga cikin gidan tare. Mama bata nan taje gidan Anty Hafsa dan tun Rasuwar Mijinta bata cika lafiya ba, shiyasa kusan duk sati Maman ko Anty wani zeje ya gansu dukda akwai yar Uwan Abban su Goggo Halima dake zaune tareda ita kafin ta gama takaba.
Be jima a gidan ba ya ajiye musu tsarabar daya je da ita ya tafi bayaj Anty ta hada masa kayan Mu'ayyad tana masa tsiyar ashe shi yayi kira Umaimah ta gudu babu sallama. Haka ya ringa yawo a gari bashi ya koma gida ba se da yayi sallar Isha. Da fargabar abinda ze tarar ya bude Get ya shiga da motarsa. Seda ya kwashe kusan minti biyar a bakin qofa yana gwada budeta yana fasawa, qin amsa wayarsa da kuma rashin fitowarta ta tareshi suka qara sakashi a rudanin abinda ze tarar haka dai yayi shahada ya tura qofar da sallama ya shiga.
Tana kishingide akan kujera ta miqr qafafunta akan centre table. Skin tight ne fari a jikinta ya matse ta tsam iyakarsa qaurin ta ga sarqar qafa silver data saka. Fuskarta ya kalla zuwa qirjinta se yayi sauri dauke kansa saboda yanda Armless rigar data saka bata boye komai na jikinta na, daman iya karta saman cibi kuma ta net ce ganin kamar bata ji shigowarsa ba ya saka shi hade fuska ya kama hanyar dakinsa se a sannan ta kalle shi, fuska a sake sabanin yanda yayi tunani tace
"Sannu da zuwa Honey"
"Yawwa ya amsa mata yana qarasawa inda Mu'ayyad yake akan tabarmar sa ta zuba masa kayan wasa.
Dagashi yayi ya kalli Umaimah da itama su take kallo yace
"Ya naji kansa da zafi sannan hancinsa kamar a toshe yake"
"Haqori ne inaga" ta bashi amsa daidai nan yaron yayi Atishawa me qarfi se khalil ya sake kallonta yana cewa
"Baki dena kunna masa Ac kuna kwana da ita bako, gashinan mura ta kamashi" seta zumburi baki ba tareda ta bashi amsa ba ya wuce dakinsa da yaron a hannunsa yanayi masa gwaranci ta rakashi da harara kafin itama tabi bayansa.
Ajiye yaron yayi akan gado yana sauke numfashi daidai nan ta turo qofar ta shigo ya zabura kamar mara gaskiya amma ganinta da Try da ruwa akai ya sakashi dai daita nutsuwarsa ya sake kame fuska. Ruwan ta miqa masa ya karba a ransa yana ayyana abubuwa da yawa. Wannan ladabin nata na gaske ne ko kuwa tarko take dana masa kafin ta fara buyagin nata.
"Dazu kin kirani wayar tana silent ban cire ba tunda naje masallaci na kira kuma baki daga ba" ya tambayeta yana cire rigarsa, seta ce
"Eh, daman so nake na gaya maka Unit ya qare lokacin kuma ina kallon wani series ne se kawai na ahiga gidan Maman Anam na qarasa bayan na dawo kuma Khalifa yazo ya kawo Abinci shine ya saka mana".
"Akan Unit ne kika mun ten missed calls na zata ma wani abun ne ya faru kuma da ya qare ba zaki kunna Solar ba" ya fada jin dalilin kiran da gaba daya ya saka jininsa ya kusan hawa saboda farga ba ashe shirmenta ne kawai,
"Toh idan da solar tana yi zan kiraka nema ai saboda taqiyi ne ya saka nake amfani da Nepa har Unit dinma yayi saurin qarewa" ta bashi amsa tana harararsa qasa qasa, se yaja qaramin tsaki yace
"Meya sameta? Kin qara dora mata abinda yafi qarfinta ko?"
"Nifa karka daga mun hankali a daren nan bansan meya sameta ba idan na kunna da safe rana na dagawa zata ringa mutuwa tana kawowa sedai da sanyin safiya ko da daddare ne kadai take tsayawa" ta fada tana miqewa tsaye. Be sake kulata ba ya shige bandaki bayan ya sauke Mu'ayyad qasa. Itama fita tayi tana mita, badan wallahi da abinda take so ba da ko kallo be isheta ba shima ya sani.
Kallonta taci gaba dayi, Khalil kuwa seda yayi wanka ya shirya kafin ya fito da yaron a hannunsa. Ajiye mata shi yayi ya fita Chemist din bakin layinsu ya karbo Masa Bonababe syrup da akace yana taimakawa yara gurin sauqin laulayin haqori. Kuka ya tarar dashi yanayi ita kuma tana dannan waya abinta kamar batajinsa ma, cikin bacin rai ya fizge wayar yana cewa
"Meye haka yaro yana kuka kina ji kin zauna kina danne dannen banza a waya"
"To me zanyi masa? Na bashi abinci ya qoshi rigimar sa ce kawai kuma bacci zeyi ba wani abu ba" ta fada tana nuna masa kwanon abincin Mu'ayyad din dake gefe.
Base ki goyashi ba tunda bacci zeyi amma se ki barshi yaringa kuka bayan kince baya jin dadi" ya sake fada yana jijjiga yaron. Zama yayi ya bude maganin, da kansa ya bashi sannan ya bashi ruwa yasha ya ringa zagayawa dashi a palour yana jijjige har yayi bacci hamshaqiyar kuwa tana nan zaune qafa daya kan daya tana dannan waya, ai yasan bata goyo ita shima rigimar banza ce saboda ya saba da suna gida Anty zata goyashi idan zeyi bacci da suka dawo ma haka Hauwa take masa.
Dakinsa ya wuce dashi ya kwantar, seda ya duba Diaper jikinsa yaga bata dade da saka masa ba beyi komai a cikinta baka kafin yayi masa addu'a ya kashe fitilar dakin ya fito bayan ya tokare qofar ya barta a bude.
Kan dining ya wuce ya zuba abinci yana kai lomar farko bakinsa wayarsa ta dauki qara gabansa ya bada Ras ganin me kiran Hadiza ce, kamar me ciwon wuya ya juya ya kalli Umaimah karaf suka hada ido dan tunda ya fito dakin take binsa da kallo kamar yaci mata bashi.
Abincin ya hadiye dakyar kafin ya danne wayar gaba daya ya kasheta dan dai baze iya wannan gangancinba, amsa wayar Mace a gaban Umaimah.
Har ya gama cin abincin tana nan zaune tana kallo a Tv tareda danna waya. Daga kan Dining din ya tambayeta akwai Maltina a Fridge tace masa babu, yasan Babun dan daman shi yake amfani da ita ita bata sha kuma tun kafin yayi tafiya ta qare be siyo ba seya miqe ya shiga dakinsa ya dakko kudi yana cewa
"Bari naje na siyo"
"A daren nan sekace shan ya zama dole ka bari da safe ka siyo mana" ta fada tana kallonsa, be kulata ba ya fice daga palour. Cana gaban gidan ya samu guri ya tsaya ya kunna wayarsa ya kira Hadiza, qarya yayi mata akan tana kira wayar ta mutu seda ya saka chaji yanzu ya kunnata tayi murmushi tace
"Nima seda na kira sannan na duba lokaci naga dare yayi karna shiga haqqin Yayata, ina taso tun dazu na kira naji yanda kaje gida ban samu kaina ba nima se yanzu".
Hira ce ta kunce tsakaninsu sam Khalil ya manta da me ya fito yi seda yaji alamar wani kiran yana shigowa kafin ya zare wayar a kunnensa ya duba, Umaimah ce take kira, ya kalli Agogo qarfe sha daya da kwata ba shiri yayiwa Hadiza sallama ya miqe yaci gaba da tafiya yana zuwa kantin ya tarar sun tashi dan daman basa wuce goma da rabi.
Auna abinda ze gaya mata ya samu bacci a daren nan kawai yakeyi haka ya qarasa gidan, a bakin Get ya tarar da ita da dogon Hijabi ga Mu'aayad ta sabo a kafada.
"Ina ka tafi daga siyo Maltina kafi awa daya na kira wayarka kuma baka daga ba" Umaimah da duk ta rikice ta fada seya kama hannunta suka shiga ciki dan da qarfi take maganar karta taso musu maqota a daren nan.
"Khalil tambayarka nakeyi fa ina ka tafi" ta sake fada yayi saurin tareta da cewa
"Ba gani na dawo ba, naje kantin Dan Baffa babu sena qarasa can titi ko zan samu, ina hanya kuma Muktar ya kirani kinsan bikinsa ya taho kuma be qarasa ginin sa ba shine muke lissafin abinda ze isa a qarasa gidan ban ankara dare yayi ba seda naga masu shagunan sun fara rufewa, kingama ko Malt din ban tsaya karba na taho" Khalil ya sheqo mata qaryar da shi kansa be san sanda ya qirqireta ba.