← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 267

Sashe 23

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salman ya bawa takardar da katin bankinsa yaje ya biya kudin sannan ya kira Mama ya shaida mata abinda ake ciki, "Allah ya bata lafiya tace" sukayi sallama, Abban na shirin tafiya saboda ana jiransa zasuje Gumel wata Gaisuwa ta Abokinsu sega Anty Laure qanwar Mama nan tazo, nan suka barta suka wuce shida Anty Saratu da take son zuwa ta debo abubuwan da zasu buqata.

Sanda ta koma gidan yaran sun dawo daga makarantar Asuba, da yake weekend har Sharifa da Abida yammatan ta sun qarasa abin karin sunci tunda Su Nazifi sun gaya musu sunje Asibiti ne, su ta barwa girkin rana ta gaya musu idan sun gama su kai Asibitin kafin ta debarwa Umaimah duk abinda tasan zata buqata ta sake komawa Asibin har sannan Umaiman bata farka ba, Anty Laure dai tace mata ta farka tana surutai aka qarayi mata wata allurar baccin.

Khalil
A bangaren Khalil kuwa kasa zama yayi a office din, yana tsaye daya daga cikin ma'aikatan sashin su ta shiga office din Balaraba tasha gayu se yauqi takeyi, tuntuni ya gane abinda take nufi dashi amma ko a fuska be taba nuna mata ya fahimceta ba, za dai su gaisa idan aiki ya hada su suyi amma ya qi bata qofar da zata gabatar masa da qudirinsa.

Yanzun ma yana cikin wannan hali na tashin hankali da rudu ta shigo tana karairaya ta zauna a kurar dake gaban office din,
"Architect ashe ka shigo banga wuce warka ba kuma yau na shigo da wuri" ta fada tana fari da ido,
"Uhm" kawai ya iya ce mata dan bashi da nutsuwar jan wata magana a yanzu, seta sake gyara zama tana narke fuska tace

"Ni na rasa yanda akayi so ya zama laifi Khalil, tunda ka fahimci ina sonka shi kenan ko kallo me daraja na dena samu a gurinka bare a je ga batun murmushi ko magana me dadi, wai me yasa? Ban kai ace ina sonka bane ko yaya?"

A firgice ya dago kai daga dannan wayar da yake ya kalleta, Mansur yake so ya kira dan yana da buqatar wanda zasu tattauna wannan al'amati na Umaimah dashi sega wata sabuwar maganardaga bakin Balaraba kuma.
"Sena kashe duk macen data rabe ka" kalaman Umaimah sukayi masa shawagi a kwakwalwa, se ya kalli Balaraba cikin rarrabewar murya yace

"Ki fita indai kina son rayuwar ki"
"Ban gane ba? Saboda nace ina sonka kake nufin zaka kashe ni ko yaya?" Balaraba ta fada a kidime tana miqewa tsaye, seda ya kalli cikin office din dan ya gama tsorata da Umaimah, ji yake kamar maganar nan da suke yi ma tana ganinsa.

Qoqarin daidaita kansa yayi ganin yanda ta rikice take daga murya tun bata tara masa mutane ba yace
"Ina da wacce nake so kuma tana da tsananin kishi, idan ta samu labarin kina zuwa gurina zata iya aikata miki komai".

Se Balaraba taja tsaki ta koma ta zauna tana cewa " wallahi ka bani tsoro ni na zata ma cewa zakayi Aljana ce ta aure ka, amma mutum fa mace yar uwata zanji tsoro wadda baka ma aureta ba aikin banza kenan nida itan duk daya idan na fita Sa'a ma na same ka"

"Balaraba please go out i need privacy" ya fada yana nuna mata hanyar waje, ta yatsina fuska tana kallonsa tace
"Wai lafiyarka ma kuwa kaga yanda ka jiqe da zufa duk wannan uban sanyin AC"

"Zazzabi nake ki fita ki bani guri dan Allah" ya sake katseta, seta juya tana cewa
"Toh ai da clinic kaje aka duba ka amma kazo ka zauna haka duk wanda ya kalle ka yasan ba lafiya ba, Allah ya qara sauqi if you need help ina Reception" taja masa qofar office din ta fice.

Bin bayanta yayi ya sakawa qofar key kafin ya kuma kan couch dake gefe ya zauna, Mansur ya sake kira yaci sa'a kuwa ya daga
"Malam inada patient idan na gama zan kiraka" Mansur din ya fada bayan daya amsa wayar kafin ya kashe Khalil yayi saurin tare shi da cewa

"Kana Asibiti? Gani nan zuwa dan Allah ka sallami duk wasu patient zanzo ka dubani" qit ya kashe wayar ya shiga tattara abinda ze fita dashi, yana zuwa reception tun kafin ya bada excuse suka hau yi masa sannu dan fuskar sa ta nuna yanayin dayake ciki, dakyar ya tuqa kansa zuwa Asibitin su Mansur sanda yaje ya tarar da patient a office din haka ya azazzala Mansur daya sallame su ragowar na waje dake jira se gurin wani likitan Mansur ya kaisu.

"Wai Khalil me yak faruwa ne, ka ganka kuwa yanda ka hargitse kamar wanda kura ta biyo me yake faruwa?" Mansur ya fada sanda Khalil din ya zauna akan kujera.
"Mansur Umaimah ce, na rasa yaya zanyi da yarinyar nan gaba daya nema take ta zauta ni" Khalil ya fada.

Tsaki Mansur yayi yana kallonsa yace "Yanzu daman akan wannan gyaran malam din ne duk ka tashi hankalinka ka tashi na mutane? Ina kao kace kaji ka gani yanzu kuma meya faru, ko Jama'ar tata ne suke firgitaka?"

"Gaskiya nima na fara yarda da maganar ka da alama yarinyar nan kanta da motsi" Khalil ya fada kafin ya fara zayyanowa Mansur duk abinda ya faru tun daga case din Jalila har zuwa na Jamila da matsayar da ake akai yanzu.

Dariya Mansur ya bushe da ita da har seda Ran Khalil ya baci ya miqe yana cewa
"Wato ga Mahaukaci na kawo maka damuwata a maimakon ka bani mafita shine zaka saka ni a gaba kana dariya, ba laifinka bane laifi nane dana gaya maka" ya yi hanyar fita Mansur ya tareshi yana cewa

"Matsalata da kai saurin fushi a inda be dace ba mutumina, ga qaramar yarinya can ta gwara maka kai ka hargitse ka rasa abin yi shine ni marainin wayonka daga nayi dariya zaka yi fushi"

"Get out of my way" ya fada yana janye hannunsa daga riqon da Mansur ya masa,se Mansur din ya shanye dariyar sa yace
"Na dena toh, zauna bari na hada maka coffee ya danyi calming naka" ya zaunar dashi akan kujera kafin ya wuce inda Coffee maker take ya shiga hada musu coffee din yana kallon Khalil dake ta zare ido.

"Toh yanzu kai me ka zaba a ciki, fa fasa auran nata ta sheqe duk wacce ka kula ko kuma zaka aure din a yanda take?" Mansur ya fada yana miqa masa cup dake cike da Coffee.  Seda ya kusan shan rabi kafin ya ajiye yana kallon Mansur din yace

"I don't know Mansur, nima ban san me zanyi ba. All i know is i do love Umaimah alot, kuma ko maganar fasa auranta da nayi barazana kawai nake mata amma wannan maganar da tayi itace ta qara tsoratani ta saka mun shakku akan ta. Kisa fa Mansur she is saying it with full confidence zata kashe ko wacce mace akaina sedai itama a kasheta, what do you think she will do randa aka ce na aureta ina so na qaro wata kaga ni zata kashe kenan"

"Wannan ma ai a rubuce take Abokina kai dare zata bi ta yanka ka sedai da safe kawai ace mana Bayero ya sheqa matar sa ta masa yankan rago" Mansur ya sake fada, wata harara Khalil ya maka masa yace

"Kaidai wallahi mutumin banza ne, ana neman mafita zaka sake tayar mun da hankali, please Mansur give me solution, kaina baya aiki kwata kwata i can't think" ya qarasa maganar yana dafe kansa daya ji ya dauki ciwo.

"Nifa ko a duk abin nan banga wani abin damuwa ko tashin hankali ba,  daman yarinyar nan kasan bata da saiti ka kwasota babu yanda banyi da kai akan ka kyaleta ka nemi wata ba kace No, se yanzu da ake maganar lessthan a Month biki zakace ka fasa?

Yarinyar nan fa har certificate na brain check dinta kace Dad dinta ya nuna maka to tell you that ita dinKwankwararriyar mara jin magana ce har ana zaton tana da mental illness amma kace kaji ka gani a haka kake so se dan yanzu tayi maka wannan dan qaramin shirmen ai ni banzata za'a ja lokaci bama har haka halinta be fito ba kuma ai you should expect morethan this ma duk wani shirme da zatayi maka dole ka shanye tunda kai ka kai kanka.

Yanzu dai abinda za'i kawai dai kayi qoqari ka dora mata saiti, ka zare mata ido sosai ka kuma kora mata warning, tunda tana sonka nasan she will comply with all your conditions".

Tagumi kawai Khalil ya zabga yana kallon Mansur dake koro bayani kamar besan girman kalmar kisan da Umaimah take ambata ba ko dan bashi tace zata kashe ba oho, jin yayi shiru alamar ya gama ya saka ya numfasa yace

"No Mansur I'm scared, like I'm fucking scared wallahi. Dane fa mata suke kurari akan abu su kasa yi amma yanzu kana kallo kullum a social media se kaga sabon case na mace ta kashe Mijinta akanabinda be kai ya kawo bama and you are saying duk kurari kawai takeyi wadanda basu akita ba ma yara qanana zakaga sun aikata, yarinyar nan fa Kishi ne da ita na Bala'i".

"Toh Khalil yanzu ya kake so ayi? Kuma maganar wani kishi kowacce mace tana da irin nata, yawanci kum loud ones din nan nasu Kishin iya baki ne suyi hayaniya shikenan, amma masu shirun sunfi hadari, sune suke kashe mutum din lokaci daya a ringa mamakin bazasu iya ba.

Umaimah ka barta da shirmenta harda yarinta duk suna damunta amma maganar Kishi ko zata kashe wani saboda kai duk shirme ne tana fada ne kawai saboda ka tsorata and she succeeded ga kanan ka birkice kamar wanda ya bigi motar sojoji amma bazata iya ba, beside wanda zeyi abu ai baya fada sedai a gani a aikace" Mansur ya sake fada, se Khalil ya girgiza kai yace

"Aa Mansur, i wish you were there kaji yanda take jaddadamun da zata kashe kowa sannan zan saka kaina a ciki? Aa gaskiya, ina son Umaimah amma barinta shi yafi mun Alkhairi Mansur".
Chapter 23 · 0% Book details