← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 267

Sashe 36

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansur da kansa ya dauki ledojin Kazarta da yoghurt ya nemi daya daga cikin yammatanda ya gani suna fira a qofar gidan ya bata da kayan ta data zubar kafin ya koma mota lokacin har Khalil ya dawo gaban ya cire hular sa yana shafa kansa.

"Khalil be kamata ka ringa mata ihu haka ba, kasab matsalar yarinyar nan nasiha da lallami ne ze tafiyar da ita bawai hargagi ko fada ba" Mansur din ya fada bayan daya tayar da motar suka fara tafiya, Khalil yayi shiru kamar baze yi magana ba can ya sauke ajiyar zuciya yace

"Mansur ina son Umaimah amma bazan boye maka ba ina tsoron irin zaman da zamuyi da wannan halin nata. Ace ita bata san ya kamata ba? Ka kalla fa Mansur idan badan Anty Hafsa tayi mata horo ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba na tabbata yarinyar se tayi abinda har a freedom radio se anji labarin mu sannan kana kallo ina mata magana a maimakon ta bani haquri ma se wasu hawaye takeyi saboda tasan bana son kukanta to ta dena yaudarata da su wallahi".

Shidai Mansur yayi bakan yana jinsa har suka qarasa gidansu, suna shiga Mukhtar daya daga cikin Abokansu ya kira wayar Mansur yana musu masifar gasu a Hotel tun dazu su ina suka tsaya dan sun hada Barbeque zasuyi, haquri ya bashi kafin ya shiga lallaba Khalil din da gaba daya Umaimah ta gama bata masa mood ya tashi ya shirya suka fita bayan daya bawa qannensa Kajin da suka siyo dan shaf ya manta da batun barbeque din.

Umaimah kuwa tana shiga cikin gida a sittin tayi kwana saboda hango Anty Hafsa data kasa ta tsare bakin hanya tana jiran shigowar Umaiman daman sedai ta makara dan tara tara suka mata Anty Laure na daga bayanta dan haka tana juyawa ta riqeta.

Yanda kasan sun samu Damin gero haka suka hau jibgarta ihun ta ya fito da yan biki ana tambayar lafiya Anty ta kwaceta da kyar daga hannunsu tana masifa tace

"Wannan wane irin wulaqanci ne Hafsa? Kema Laure zaki biye mata ku kama yarinyar da duka salon ku ja mata tsautsayi ta tafi gidan miji da jinya"

"Idan bata tafi da jinya ba ai mu data zubar mana da mutunchi ta barwa kanta abin magana har yaya da jikoki, banda tsabar iskanci dan ubanta ta rasa ranar da haukarta zata tashi se yau a cikin taron jama'ata bata mun tari?
Ai ba a nan ya kamata ku dake ta ba, so nayi seta tube ta shiga wanka zan kama yar banza ga Darbejiya can na saka Salmanu ya tsinko mun na farfasa wa yar banza jiki idan yaso tayi jinyar da kyau" Mama data qaraso gurin ta fada.

Ita dai Umaimah tunda ta samu Anty ta ceceta sukayi ciki shikenan, can uwar dakinta ta wuce da ita ta hada mata ruwan wanka tana yi tana mata fadan abinda tayin

"Yanzu Umaimah idan bakiyi hankali ba se yaushe zakiyi? Kina kallo Allah ya taimakeki ya hada ki da dangin miji masu sonki ki kalli yanda suke rawar jiki dake a gurin nan shine kikaje zaki bada kanki. Dan Allah ko koyi haquri ki kuma ringa sakawa zuciyarki salama dan wallahi yanda Khalil yake binki yana lallabaki a waje ina tabbatar miki daga gobe labari se chanza, halinki na gari ne ze zaunar dake a gidan miji, duk wannan buyagin da hayagaga babu abinda zasu ja miji se wahala" Antyn ta fada tana shafa mata dilka a jikinta.

Umaimah dake jin kamar ta sauke fushinta akanta ta dai daure ta ringa cewa toh dukda qasab ranta tasan gaskiya suke fada mata dan gashi nan tun ba'aje ko ina ba ta fara ganin chanji a gurin Khalil din, gashi jiya dakyar suka sasa ta yanzu ma ta sake kunno wata rigimar kai ita dai Allah ya shiga lamarinta.

A dakin Antyn ta kwana dan da Abba ya aiko kiransu shida yan uwansa zasuyi musu Nasihar bankwana ma Antyn ce ta rakata ta kuma kasa ta tsare har aka gama suka dawo ta bata Kazar data dafa musu da tafasashshiyar madarar shanu taci tayi nak kafin tayi bacci.

A safiyar washe gari dakyar ta yarda akayi mata light Make up ta shirya cikin fari da Golden din Lace iri daya dana Nuratu dake walwalarta kamar kowacce Amarya, ita kuwa ta samu guri ta zauna zugudi duk yanda qawayenta suke tsokanarta da amma ta kasa tanka musu dan rashin ji daga Khalil da batayi ba tun daren jiya ya bala'in daga mata hankali.

Furucinsa take tunawa da yace mata idan ta sake yin wani shirme ba ana gobe daurin auransu ba ko a ranar ne seya fasa yanzu ita ta rasa ma a wanne matsayi take dashi dan tun jiyan be kirata ba ita kuma tsoron abinda zeje ya dawo ya hanata kiransa a waya haka ta zauna ana ta hidimar daurin aure kowa ka gani cikin farinciki banda yana walwala banda ita.

Alqawarin Allahya cika, qarfe 11 na safiyar Asabar din Aka daura Auran Dr Nuratu Sabo da Angonta Dr Sagir Nafi'u Tareda na Umaimah Sabo da Angonta Architect Khalil Umar Bayero akan sadaki naira Dubu 100 kowaccensu.

Dafe qirji tayi lokacin data ji sanarwar daurin auran ta cikin lasifiqar masallacin layin nasu inda ake daurin auran, Khalil be fasa ba kenan?.

A zahiri babu wata murna ko farincikin data nuna amma badininta ko fadar yanayin da take ciki ma bata bakine, wai dagaske yau ta zama matar Khalil ta halal daga yau sun zama daya ita dashi ina zata saka kanta dan murna amma sam halin da take ciki ita da angon nata ya danne murnar se ya zamana kawai gatanan ne tana zaune.

Lokacin da Angon Nuratu da Abokan sa suka shiga gidan Dakin Anty ta shige ta zauna dukkiran ta da ake akan ta fito suyi hoto taqi to ta fita tayi musu me? Baqin ciki ya kasheta tunda ita nata angon ba zuwa zeyi ba?

Tana nan zaune ta jiyo wata maroqiya ta ware murya tana zabga kirari, idanba kunnenta ne ya jiyo mata qarya ba sunan Khalil tajiyo tana ambata sannanga wata sabuwar hayaniyar maza na shigowa seta miqe da sauri ta daga labulen window ta leqa idonta ya sauka kan Khalil daya sha Light blue din shadda yayi kyau har bata san yanda zata misalta ba, kumallon ya motso mata saboda yanda ake ta daukar Angwayen hotuna da wayoyi amma taringa qoqarin dannewa se numfarfashi take kamar wadda kunama ta harba daidai nan Maman Asad ta turo qofar dakin tana cewa

"Allah ya yaye miki baqin hali Umaimah, nan kika zo kika boye ga angonki can yana nemanki dalla wuce muje mutuniyar banza kawai da bata san Annabi ya faku ba" Maman Asad din ta qarasa tana kamo hannunta suka fice daga dakin.

Kasa riqe hawayenta tayi lokacin da Maman Asad ta qarasa da ita gaban Khalil dake tsaye fuskarsa babu yabo babu fallasa, girgiza mata kai yayi alamar kartayi kukan amma ina kamar yace tayi sega hawaye sha se kawai ya bude mata hannu ta fada jikinsa ta qarasa sake masa kukan harda sheshsheqa.

Ihu aka dauka masu daukar su hoto da Video kuwa daman sun samu nayi qawayenta se ihu suke suna daukar su a hoto
"Awwn love in Tokyo, Umaimah bazaku kashe muda salonku ba wanda bashi da masoyi ai se takaici ya qume shi" Yaya Naziyya ta fada cikin salon wasa aka sake fasa dariya Umaimah dai tunda tayi luf A jikin Khalil, a kunnenta ya rada mata

"I get you wife" .
Haka aka ringa daukar su hotuna, ran Umaimah kamar an saka Hypo an wanke matashi tas dukda fuskar Khalil din babu fara'ar nan data sanshi da ita amma kukawar daya bata a gaban mutane ta gama mata komai, ta kuma tabbatar da zuwa dare zasu sasanta dan bazata bari ta shiga gidan sa suna takun saqa ba.

Haka aka gama photo session Angwaye suka wuce gurin reception Amare kuma aka shiga hidimar yinin biki da shirin miqasu gidajensu saboda da wuri za'a kaisu dan Dangin Mijin Nuratu zasuyi Dinner.

Qarfe hudu aka dauki Amare, Nuratu aka fara kaiwa Umaimah tayi mata rakiya har cikin dakinta, shaquwa ba qarya ba, duk irij tarangahumar tashin hankalin da suke sha a gida kamar masu ganin hanjin juna se ga Umaimah ta fashe da kuka da batayi ba a gida har aka taho dasu ta fada jikin Nuratu suka rungume juna.

Yanda suke kukan dole suka karyawa sauran yayyensu zuciya suka hade gaba daya suka ruguntsune, jarumtar da sukayi a gida se gashi Umaimah ta karya musu dakyar aka yakiceta suka wuce nata gidan aka bar Nuratu da wasu daga cikin Masu halartar Dinner kafin sukaita itaka su koma gida su shirya.

A dan madaidaicin gidan na Khalil aka sauke Amarya Umaimah. Gidan two bedrooms ne a cikin madaidaicin palour asalin ginin daki daya da bandake ne daya babu daya tashi gyara ya tashi wani daki falle daya dake tsakar gida ya shigar da bandaki a dayan dakin ragowar ya qara mata a kitchen da yake atsakar gidan shima aka fitar fa store se qaramin bandaki na tsakar gida.

Gaba gidan bashi da girma dan filin tsakar gidan mota daya ze dauka amma yanda Khalil din ya saka kudi ya gyara gidan abinka da Architecture dole duk wanda ya shiga seda ya tafi da santin gidan ga hadaddun Furniture da suka qara qawata gidan sun saka komai yanda ya kamata.

A dakin da yake matsayin nata suka ajiyeta, Nasiha sosai Anties dinta sukayi mata irin me ratsa jiki da tasa Umaiman tayi tubus kamar wadda ruwan sama yayi wa duka kafin sukayi mata sallama aka barta da qawayenta uku, Rumasa'u, Farida Cousin dinta se Fatima.

Su suka gyara mata gidan tsaf suka wanke bandakuna. Seda sukayi sallar Magriba kafin Umaiman ta sake wanka, kafin ta fito sun bi gidan lungu da saqo sun saka hadaddun Turaren wutar da Akayi musu a gurin *Meerah_Perfumes_More* wanda Gudummawa ce takanas Aminiyar Mamansu Hajiya Findiga ta aiko musu shiga daga Adamawa inda take.
Chapter 36 · 0% Book details