Sashe 85
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Haka dai ze haqura ya barshi da ya samu kakannin ma masu so su riqe jikan, nan Hajiya data dauko Inteen kina ganin yanda suka qare" Khalil ya fada suka fashe da dariya gaba daya. Seda suka lafa Jalila ta kalle shi tace
"Toh ya ake ciki ranar mun fara magana a waya?"
Tattara hankalinsa yayi akanta yace
"Wato wata yarinya ce muka hadu da ita kin gane, harga Allah tana burgeni kuma ina sonta amma kuma ni banyi tunanin nan kusa zata kawo maganar muyi aure ko wani abu ba kuma ita bala'in sona takeyi, nidai in taqaice miki magana yanzu kinsan dai matsayin da nake ciki a yanzu bazance zanyi aure ba saboda kowa seya tambayeni dalili idan kika duba aurena shekara biyu kwata kwata ni kuma bani da wani dalili me qarfi dazance gashi ya saka zanyi aure".
Shiru Jalila tayi tana kallonsa har ya kai aya kafin taja numfashi tace
"Ita yarinyar yaushe kuka hadu, kuma tsahon wane lokaci kuke tare?"
"Bamu wani dade ba wata uku zuwa hudu kenan da haduwarmu lokacin da naje aiki Lagos din nan, dukda dai mun taba haduwa a nan Kano amma dai Officially mu fara magana da ita yanzu za'ayi 3 months" Khalil ya bata amsa tayi shiru tana kallonsa, so takeyi tace masa lokacin da Umaimah taqi binsa Lagos kenan kuma ta tambayeshi wace irin alaqa ce tsakaninsu dukda bata zargin qanin nata amma tasan abinda Umaiman tayi masa yana iya sakawa shedan ya zugashi ya fada abinda ba halinsa ba. Itama ta samu labarin ne a bakin Khalifa kuma ya roqeta akan dan Allah karta gayawa Kowa dan Yaya Khalil yaja masa kunne kawai ya kasa hadiye maganar ne yasa ya gaya mata dan ita ana sirri da ita ba irin su Yaya Jamila faransai bace.
"Kinyi shiru kina kallona kamar wanda nayi miki qarya" Khalil ya fada se tayi murmushi tace
"So nake na auna soyayyar da kakeyi mata da irin wadda na gani a idonka sanda kake gaya mun ka hadu da Umaimah"
"Babu hadi Jalila babu macen da zata kamo qafar Umaimah a zuciyata" Khalil yayi saurin tareta a zuciyarta tace
"Ta gano lagon ka shiyasa take garaka kamar kwallo a fili kuwa seta gyara zamanta tace
"Toh tanada wannan matsayin ya akayi har idonka ya iya hange hange ka samo wata ka fara so, kuma a yanda kake jaddada soyayyar nan tata ace a ayan shekarun nan zaka mata kishiya Khalil?
Idan har da gaske ka daukeni yar uwar da zamu kashe mu rufe ka gaya mun gaskiyar meye damuwarka, meye dalilinka na son qara aure? Ni kuma zanyi maka hukunci bisa adalci in sha Allah dan bazan so ka tauye kanka ba haka itama Umaimah bazan bi bayanka kayi mata rashin Adalci idan har ya zamana son ranka ne kawai".
Shiru Khalil yayi yana nanawa maganarta a zuciyarsa, yanada yaqinin Jalila zata riqe masa sirri idan ya gaya mata amma yana tsoron ta farayiwa Umaimah wani kallo na daban a matsayin me musgunawa dan uwanta, yasan zata qullaceta dan Jalilan nason duk abinda yake so tana kuma qin abinda yake bata masa.
"Kayi shiru dan qanina ko da akwai matsala ne" ta fada cikin tsokana ya dago ya harareta tayi dariya tace
"Sarkin son girma duk tsiyarka dai minti biyar ba wasa bace" dole yayi murmushin shima ta sake cewa
"Yawwa ina jinka kayi magana mu samu mu san ta inda zamu kamo bakin zaren maganar nan"
"Kina ji Jalila ina son Umaimah kuma bani da wata matsala da ita, damuwata guda daya ce kawai yanayin aikina da bana zama guri daya a koda yaushe ana turani garuruwa nayi ayyuka kuma ina yin kwanaki wani lokacin ma satittika ni kuma ina da sha'awar duk ina zani na tafi da Matata, matsalar anan ita kuma Umaimah bata son tafiya.
Duk sanda wata tafiya ta taso se rayukan mu sun baci kafin ta bini, kinga last tafiyar da nayi Lagos har na gama zamana na dawo bataje ba acan nema na hadu da Hadiza dan a lokacin fushin da nake ciki na yanke shawarar aure kawai zan qara na auro wadda ko bangon duniya nace zanje zata bini"
Yaci gaba da bata labarin yanda ya hadu da Hadiza da irin soyayyar fa sukayi har zuwa matsayin da suke yanzu akai na zancen turowa da tayi masa. Ya rufe da cewa
"Banaso haqqinta ya kamani dan dagaske yarinyar tana so na ni kuma bansan ya zanyi ba yanzu.
Tun bayan dawowata na tuntubi Hajiya da maganar dan naji ta bakinta tayi futufutu tace babu wannan maganar ba yanzu ba har gaba babu ita.
Toh ni maganar Hajiya ma da sauqi nasan idan na lallabata tana iya yarda, Umaimah nada bala'in kishi irin wanda bakiyi tunani ba, idan zancen auran nan ya fito na tabbata babu sauran zaman lafiya tsakanin mu".
"Hmmmm" Jalila taja dogon numfashi tareda sauke taguminda tayi tana kallon Khalil tace
"Ni har na rasa ta ina zanfara ma, idan na fahimceka abinda yasa ka fara kula Sabuwarka saboda rashin Umaimah a kusa ne bari na fara da wannan bangaren in har kana ganin cewar Umaimah bazata haqura ta ringa binka duk inda zakaje ba kana da hujjar da zaka qara aure kuma duk wanda ka gayawa dalilinka baze hanaka ba kodan gudun fadawa halaka.
Amma idan shawara kake nema se nace maka qarin aure ba shine mafita ba ka zauna da ita kuyi magana ta fahimta ka nuna mata buqatarka da abinda bijirewa hakan ze iya janyowa idan har bata gyara ba daga nan kana iya daukar mataki na gaba sannan ita wannan Hadiza kace kowa sunanta ba son ta kakeyi ba, Umaimah ta riga ta siye filin a ganina ka saurareta ne kawai a lokacin saboda fushin Umaimah inda dagaske ka gantan kake sonta zuciyarka bazata kawo maka wani tunani ba balle har kaji shayin tunkarar kowa da maganar auranta.
Kuma koda ace ka aureta be zama lallai ka iyayin adalci a tsakaninsu ba, idan auran kake so dagaske ka bari ka samu wadda soyayyarta tayi takara data Umaimah a zuciyarka idan ba haka ba yanda kake Son matar nan kake tsoronta duk wadda ta shigo gidanka bayan ita wahala kawai zata sha".
"Kema bakya goyon bayan maganar kenan?" Khalil ya tambayeta fuska babu walwa kafin tayi magana yaci gaba da cewa
"Ni wallahi tsoron hakkinta ya kamani nakeyi na san soyayya nasan zafinta, bakiga irin Kukan da takeyimun ba jiya tana nanata tana sona naji tausayinta sosai"
"Tausayinta kakeyi ba Son ta ba Khalil, idan kuwa hakane ka barta kayi mata Addu'a Allah ya bata wanda ya fika dan bata da gurbi a zuciyarka Umaimah ta gine duka filayen sedai idan rusau za'ayi" Jalila ta fada cikin tsokana a zuciyarta tana sake auna maganar Khalil din, ita dai a iya tata Basirar abinda ta gani kenan, ba son hadiza yakeyi ba tausayinta yake kuma fushin Umaimah ne ya saka shi harya fara kulata, ko a yanzun bata raba daya biyu bata masa rai tayi shiyasa har yake tunanin yayi auran.
Tattaunawa suka cigaba dayi akan Abubuwan da suka shafesu har suka gangara batun gidansu daze siya da yanda yake so yayi dashi, be bar gidan ba se gurin qarfe uku na rana shima saboda Mansur ya kirashi yana so su hadu ya tafi bayan ya cikata da Alkhairin dayaje mata dashi tanata godiya, suna son dan uwan nasu saboda yanda yake sonsu.
Maganar da sukayi da Jalila ta saka ya qara ja baya da Hadiza kuma ya yarda dagasken ba son ta yakeyi ba tausayine da kuma huce takaici da yaso yayi da ita amma dukda haka yana tausaya mata, kullum cikin rarrashinta yake da gaya mata cewar ta fawwalawa Allah idan hat ya qaddara zasuyi aure zasuyi a sanda yaso.
Data matsa masa akan Yayanta yace yana son ganinsa ranar ya haqura yaje, be boye masa komai ba ya gaya masa uzurinshi ya kuma fahimce shi yayi musu fatan Alkhairi idan Hadiza matarsa ce Allah ya tabbatar, bayan ya gama da Yayan ya turo masa ita sukayi magana, kamar ze zubda Hawayen tausayinta saboda yanda duk ta rame dalilin damuwar da ta saka kanta a ciki. Haquri ya bata tateda lallashi, yace mata baze ce ta jirashi ba, amma idan da rabon aure a tsakaninsu yana fatan Allah ya matso musu dashi kusa sannan ya roqeta da suci gaba da gaisawa idan tana ganin babu matsala tace zatayi tunani haka suka rabu rabuwar da yake ganin sunyi ta kenan shida ita.
Ciwon kai da jirin da suka matsawa Umaimah ya saka dole sukaje Asibiti wata ranar Litinin, bayan likitan yayi mata yan tambayoyi ya auna jininta ya rubuta mata magunguna akan taje tasha idan bata samu afuwa ba su sake komawa. A hanya Khalil ya ringa mata fadan rashin bacci da wuni da takeyi akan waya dan hatta idonta jini ya kwanta shiyasa likitan be kawo tunanin kowanne ciwo ba yace rashin bacci ne ta ringa samun isashshenhutu suna tafe ta tunzura baki gaba saboda fadan da yake mata kai tsaye gidan su ya kaita, idan da Umaimah tasan can ze ajiye ta yasan bazata yarda ba dan tunda ta gudo kamar yanda Anty ta fada bata sake komawa ba.
A tsaitsaye suka gaisa yayiwa Mama bayanin bata da lafiya daga Asibiti suke, ya qarasa da cewa
"Dan Allah Mama ki saka mata ido ta samu tayi bacci karta zauna danne dannen waya"
"Uhm abin nata har ya kai ya saka mata ciwo kenan ko, jiyan nan naji Salman yana maganar tsakar dare tayi masa magana akan yaje zata aike shi seda Safe yaga saqon ya duba lokaci yake cewa Ashe Umaimah bata dena kaiwa dare tana chatting ba toh Allah ya shirya" tayi masa fatan Alkhairi ya wuce Umaimah dai tunda ta shige daki tayi luf, da mama ta tashi yi mata tsiya wayar gaba daya ta kwace, Mu'ayyad daman suna shiga yara suka dauke shi dan haka tana cin abinci tasha magungunan tana nan zaune shiru Mama nata shige da ficenta kota kanta bata bi ba baccin dole ya dauketa saboda magungunan data sha.