← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 229 OF 267

Sashe 229

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa tayi mata gwatson kenwa, idan kaga yanda Umaimah ta koma a shekara daya da fara Zawarcin gaske se ka tausaya mata kuma ka sake gasgata Al'amarin Ubangiji dakan sauya abu a sanda yaso. Ta yi wata irin rama da baqi babu rashin Abinci amma ta fita a hayyacinta kana kallonta kasan bata da nutsuwar zahiri data zuciya a koda yaushe idan ba aiki takeyi ba zaka sameta ta zauna tayi shiru tana tunani, a yanzu kam ta gama yarda da cewar Khalil ya barta tunda har ze iya daukar tsayin shekaru biyu cif ba tareda ya waiwayeta ba tabbas ya zareta daga rayuwarsa. A kullum dare kwana takeyi cikin kuka da juyayi, nadama mara amfani ta dirar mata akan abinda ta aikata har yayi sanadiyyar barinta da Khalil. Me yasa batayi haquri ba? Me yasa bata karbi qaddara a yanda tazo mataba ta gaza fuskantar duk wanda ze tausheta a baya ya nuna mata tayi haquri me yasa basu fito sun bayyana mata makamanciyar wannan rayuwar da take fuskanta a matsayin abinda zata tarar sakamakon butulcewa? Ta biyewa kururuwar shaidan da zigar qawayen banzan da tsayin lokacin nan babu wadda ta waiwayeta balle harta san halin da take ciki koda yake duk tarin qawayen nata da daman ita take bauta musu ita suke mora babu wadda ta bi sahun sanin inda take tsayin shekara guda da rasa wayarta. Tayi mamaki kwarai da ace Rufaida bata nemeta ba, daman batayi tsammanin Safina ba kodan kalar rabuwar da sukayi a Asibiti amma Rufaida fa a baya baya dabda Al'amura zasu rikice mata ta dawo sun qara dinkewa amma ace tajita shiru bata zo inda take ba tunda dai tasan gidansu ai ya kamata ta tun tuba taji tana da rai ko ta mutu.

Babbar damuwarta irin yanda Iyayenta da yan uwanta gaba daya suka banzatar da ita, irin yanda suke mu'amalantarta na mata ciwo amma ba laifinsu bane a yanzu ta fahimci tarin wautarta a baya da abubuwan da tayi ta kuma ji irin zafin da sukaji a lokacin data banzatar dasu itama ta daukaki wasun su suka zame mata komai yau gashi a sanda ta shiga halin da take buqatar dan uwan da zata jingina dashi tayi kuka ta rasa badan bata dasu ba sedan kunya da nauyin abinda ta aikata musu a baya baze barta ta iya tun karar su ba. Tana kallo su Nuratu zasu zo gidan su qule da Mama a daki suna hira cikin nishadi da jin dadi ita tana rabe a tsakar gida ko tana aiki tsakaninta da Maman umarnine na yin abu idan ta sakata aiki dan a tsahon lokacin nan bata taba ce mata Umaimah karkiyi ba, ta rasa damar shiga dakin Mamanta tayi hira da Ita Antyn ma da take ta tata tun wancan lokacin ta watsar da ita ta dawo tsakaninsu ga Yayanta da suka mayar da ita tamkar Tabarma Yanda Sharifa da Firdausi suke tata mata rashin mutunchi a gidan kuma bata isa tayi magana ba dan akwai ranar data Mari Firdausin Abba da kansa yayi mata kaca kaca har yana fadin idan tana da kunya har taji Haushin wani dan ya mata rashin kunya kota manta sanda taringa kallon Idon Sa'ar Uwarta kuma Matar data tsugunna ta haifa mata Miji ta ambato iyayenta ta zaga har akwai rashin kunyar da za'ayi mata taji haushi? A ranar tayi kuka tamkar hawayenta ze qare ta shiga rudu da Dana sani kuma se a ranar hankalinta ya dawo jikinta ta shiga tariyo zamanta da Khalil da irin mugayen ta'adundata ringa aikatawa.

Ta ringa hakaito tarin qaunar da Khalil da yan uwansa suka nuna mata domin babu wanda zata cire a ciki duk sun sota, mugayen halayanta suka sanya su yi mata tawaye kuma duk da haka Khalil da Hajiyar sa basu barta ba, tana iya tunawa har a daren da Khalil ze saketa dukda hauka da Tijarar da takeyi Hajiya bata fasa yi mata uzuri ba ta shafawa idonta toka ta manta Alkhairan matar a gareta tayi mata zagin da idan da ita ta kirki ce ko wani taji ya kwatanta yiwa Hajiyar se inda qarfinta ya qare amma a gaban Danta da iyayen da suka haifeta bata dubi Alfarmarsu tayi musu kara kodan Haifarta da sukayi suka bata tarbiyya ba ta watsar tayi abinda taga dama toh waima banda son zuciya irin tata ta ina Khalil ze sake waiwayarta bayan duk abinda tayi masa hatta ubansa dake kwance cikin kabari besan an aureta na seda ta ambato ta zaga to ya dawo gareta kuma a wanne matsayi idan dai da kunya ai itama ba zata yarda ta sake hada ido da wani daga cikin Ahalin Khalil ba dan bata da kwarin guiwar da zata kalle su ba kuma tasan da irin Kalaman da zatayi amfani gurin wanke kanta ba.

A hankali ta yada duk wasu makaman da take taqama dasu ta fuskanci rayuwa da abinda take tafe dashi ta kuma yarda da cewar lokacin girbar abinda ta shuka a baya ne ya zo mata. Duk wanda ya santa a shekara uku baya idan ya ganta a yanzu baze ganeta ba saboda yanda ta koma. Bayaga aikin bauta da takeyi domin a yanzu Umaimah da bawan da aka siya banbancinsu kadan ne, a rana bata samun hutu na cikakkun awanni hudu, tun Asuba idan ta farka ta fara gyaran gida da dora abincin safe data gama aka karya zata yi wanke wanke ta maida na rana duk a qoqarinta na kiyaye duk wani abu da ze qara mata laifi a gurin Abba da Mama da yanzu take neman hanyar wanke kanta a guri su sannan duk inda Qarfe shida take ta sauke abincin dare. Da itacen data qi jini take aikin tunda bata da Asi yanzu kuma komai ruwa ko iska haka zatayi aikinta ita da Gas dinsu sedai Kallo dan sau da yawa idan aka samo danyan itace Mama takance ta dora a Gas dinse tace Aa, muddin ba Abba ne ya bata umarnin taba masa abu ba ba zatayi ba.

Sosai take shan wahalar rayuwa ta jeme ta fige idan ka kalle ta se ido kawai babu wannan gayun bare ta samu damar zuga iskancin data saba to dame zatayi gayun ma suturu dai gasu nan tana dasu bila Adadin amma babu damar sakawa dan kayayyakinta gaba daya yanzu sun mata yawa saboda rama. Man shafawarta Vaseline ne Habiba se Sabulun Give da Abban yake bata dubu daya duk wata wai ta siyi sabulun wanka, wanki da man shafawa kamar wata yar tsana babu zancen tutare daman Alumun take gogawa a hammatarta kayanta kuwa qaurinitace ya isheta ba seta qara dawani turare ba koda yake a hakan ma ya mata bata tsammaci zata samu ba tunda Mama da take zaton zata fishi laushi abinda bata so bata bata a haka take jalauta rayuwarta duk buqatu a cikin dubun nan zatayi wanda ya zama dole, hatta da Pad data ga cewar tana cinye mata fiye da rabin dubun a hakanma kuma leda dayar na wadatarta takeyi ba seta yankewa kanta amfani da ita, ta samu wani zani a kayanta ta yayyankashi tayi qunzugu wadatattu. A ranar data fara amfani dashi tayi kuka tamkar ranta ze fita da tana wankewa, ta tuna a gidanta drawer guda take da ita ta pad hatta baqo idan tayi buqatarta ta kamashi Pack haka take kyatarta kuma yar waje me kyau ma ba made in Nigeria ba take amfani dasu amma wai yau itace take amfani da qunzugun Atanfa a gidansu tabbas a tsoraci rayuwa.

Cikin wannan qangi da matsatsi taci shekara uku babu kuma wani sauyi ko sassauci kullum tana cikin gida tana aiki zata iya cewa ma ta manta da kalar qofar gidansu ita abu daya da zata iya cewar na jin dadi daya sameta shine fara kawo Yaranta gidansu da akayi tun shekara daya data wuce dukda zuwan nasu wuni ne basu taba kwana ba sannan su kansu yanda suke Mu'amalantarta abin na matuqar duk zuciyarta ranar da suka fara zuwa batayi tsammanin tayi kewarsu har haka ba se a lokacin tana tsakar gida tana shara suka shigo su ukun cikin kyakykyawar shiga Bibi da Iman sunyi Anko da gudu suka wuceta suna kiran sunayen yan gidan da alama suma cike suke da murnar zuwa gidan kakannin nasu.

Sakin tsintiyar tayi ta bisu da kallo, shekara uku kenan rabon da ta saka Mu'ayyad da Bibi a ido sunyi wani irin kyau da girma Musamman Mu'ayyad din ya zama sauriyi ga Iman ma da take shekara uku kenan yanzu tayi wayo sosai tana bin yayyenta tana maimaita sunayen da suke fada tunda ita dai bazata tuna yan gidan ba. Dakin Mama suka fada gaba dayansu, tana jiyo muryar Maman daga inda take cikin tsananin murna tana tambayarsu daga ina waya kawo su seta kasa ci gaba da sharar ta tsaya a gurin wasu hawayen tausayin kanta suna zubo mata wata qila sun manta da ita shiyasa babu wanda ya nemeta a cikinsu se su Yasir suke cigiya. Dakinta ta wuce ta fada kan gado ta fashe da kuka a hankali amma irin me cin ran nan, me tayiwa rayuwarta haka? Wace riba taci? Da ranta bata mutu ba yayan data haifa sun haqura da ita basa tunawa da ita anya idan mutu ba ta gyara alaqarta ba kuwa zata samu wanda ze ringa tunawa da ita kuwa yana mata addu'a?
Chapter 229 · 0% Book details