← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 267

Sashe 104

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jalilah" Khalil ya kira sunanta cikin qosawa da maganar da sam be gane inda ta dosa ba kafin yace
"Dan Allah kiyi magana irin wadda zan gane, ban san wane hoto kike magana akai ba ballantana na fada miki gaskiya ko qarya akansa".
"Toh, kana WhatsApp da wannan number ne? Gara na tura maka ka gani da idonka zefi sannan muyi magana, ak na zata kaima ta aika maka ne shiyasa kaji ina maka magana kaitsaye" Jalilan ta sake fada ko kafin ya amsa mata da yana WhatsApp din ko bayayi ta kashe wayar se shima ya shiga WhatsApp din yana jiran saqonta.

Wayarce ta subuce daga hannunsa tsabar kidima ya bita ya dauka ilahirin jikinsa babu inda baya rawa. Khausar ce ta fado masa arai, wato abinda ta fada kan wanda zatayi musu a gaba se yafi na baya kenan innalillahi amma Khausar ta cika la'ananniya da bata tsoron Allah, me Hadiza ta tsare mata a duniya data zabi ta cutar da ita cuta mafi muni tayi mata qazafin Lesbian, Lesbian fa? Tasan girman Zunubinsa Neman Jinsi kuwa laifi ne babba wanda akansa aka halakar da Al'ummar Annabi Lud. Dabi'ace da ko cikin dabbobi basa aikata ta se a cikin mutane gafalallu da suka rigada suka juyar da zukatansu daga neman Rahamar Ubangiji.

Number Jalilah ya shiga kira a ransa yana tunanin toh a ina har Khausar ta samu numbobin yan gidansu dukka dan idan yaji daidai har Hajiya Jalilan tace an turawa, tana dagawa yace
"Jalilah yaushe ta turo muku da wannan saqon, bama wannan ba a ina ta samu numbobinku kinsan yarinyar data aiko ne?"

"Bangane a ina ta samu numbobinmu ba kuma Umaiman zaka ce na sani kana cikin hankalinka kuwa Khalil?" Jalilah ta fada cikin mamakin kalamansa da basuyi kama da yasan me yake fada ba. Se ya tsaya cak yana maimaita Sunan Umaimah a zuciyarsa, Umaimah fa yaji tace Umaimah dai wadda ya sani ko kuma wata shaidaniyar aka samu me irin sunanta? Sabida ya tabbatar yace mata

"Wace Umaimah haka ta gaya miki sunanta?"
"Karka rainamun wayo Khalil, Umaimah nawa muke da ita banda matarka? Daman ta fada tace idan ka sani qaryatawa zakayi ashe kuwa dagaske ne gashi kana neman ka rainamun wayo ka nuna itama baka gane wa nake nufi ba. To wallahi ba'a zuri'ar mu ba, idan aure kake so kaje ka nemo yar mutunchi amma ba zaka kwaso mana kara da kiyashi ka kawo mana ba" Jalila ta fada cikin qunar ran jin ze raina mata wayau.

Cikin tsawa Khalil ya mayar mata da cewa
"Ya isheki malama, yanzu saboda kema bakida hankali har Umaimah ce zata gaya miki abu ki hau ki zauna saboda baki san halinta ba ko? Ita Umaiman a ina ta jiyo wannan maganar kuma yanzu bayan ku se waye ya sani?"

"Tabbas abinda take fada ya tabbata tunda gashi har mara hankali kake kirana saboda asirin lalatacciyar da kake neman kwaso mana ya tonu, daman ginin daka digirgiri hankali ka tada ita zaka kawo kusada mahaifiyar mu ka goga mata bala'i ana neman Mata a cikin gidan da take ko? to ka kirani da komai ma kai kajiyo amma wallahi baka isa ba. Ko asiri tayi maka se mun karyashi kuma da ni nace kar a gayawa Hajiya amma yanzu da kaina zan tafi na gaya mata yau base anjima ba tunda naga akamar baka san me kake yi ba" Jalilah ta hayayyaqo masa se yaja tsaki,hannu ya sa ya dafe kansa daya dauki ciwo lokaci daya kafin yace

"Qarya takeyi wallahi sharri sukayi mata kuma itama Umaiman bayin kanta bane na sani sakata akayi amma duk ma wanda yake da hannu a cikin wannan al'amarin wallahi bazan barshi ba, sena bi mata haqqin bata mata suna da sukayi kuma karki kuskura ki gayawa Hajiya komai kinji na gaya miki idan kuma kika fada kika tayar mata da hankali shikenan"
"Ba shakka Khalil to Allah ya taroka dan naga alamar ka zauce" Jalilah ta fada kafin yace wani abu ta kashe wayarta a ranta tana gasgata zancen Umaimah datace yasan komai akan maganar. Badan tana tsoron ta zama silar motsawar Hawan jinin Hajiya ba da a daren nan zata je ta gaya mata amma dukda haka se ta sani dan ita kadaice zata iya hanashi auran nan ya hanu.

Khalil kuwa tana kashe wayar layin Umaimah ya kira, bata daga ba harta katse ya sake kira sannan ta daga ta bashi Uzurin Alwala takeyi Ankira sallah. Seda yayi namijin qoqari gurin danne bacin ransa ya saisaita muryarsa yace mata
"Kunyi maganar Hadiza da Khausar ne?"

UMAIMAH
Ranar da take jira ce tazo gashi ya kawo kansa da kansa dan haka yanzu za'ayi maganar, shigewa daki tayi ta zauna gefen gado wutar kishin daya qyastawa ashana ta shiga ruruwa a zuciyarta tace
"Daman ina jiran Allah ya kawo ranarda kai da kanka zakayi mun zancen yar iskar karuwar da kake nema a matsayin mata. Ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan ido na toh Asirinka ya tonu munafikin Allah dakai da yar iska ragowar Maza da Matan da kake nema. Wallahi kaji kunya Khalil, in ma mace zaka nema ka nemi me aji mana amma se yar Lesbian dabba me neman jinsinta"

"Ya isheki Umaimah" Khalil din ya daka mata razananniyar tsawar da seda taji dan cikinta ya juya kafin yaci gaba da cewa
"Tambayarki nayi kunyi magana da Khausar kuma naji amsata, sannan ina so ki sani ita Wadda kike kira Dabba karuwar tafi ki sau dubu a gurina, ban taba sanin wawiya ceke mara tunani ba se a wannan karon Umaimah, kinsan girman laifin da kuka aikata kuwa? Kinsan girman qazafi kuwa qazafi ma mafi muni saboda ke Mahaukaciya ce a hada kai dake a ruguza rayuwar yar uwarku mace, To ki shirya kin tayata kun lalata rayuwar wata a dalilina yanzu kece next target dinta, sannan ki shirya karbar sakamakon abinda kika aikata nan bada dadewa ba" yana kaiwa nan ya datse kiran wayarsa wata irin tsanar Umaimah nayi masa dirar mikiya.

Zare wayar tayi daga kunnenta tana so ta tabbatar da Khalil tayi magana ko kuwa wani ne yayi mata basaja. Ita Khalil yake kiran karuwarsa ragowar Mata ta fita daraja a gurinsa? Anya ma kuwa yana cikin hayyacinsa?
Neman guri tayi ta zauna saboda yanda taji kanta yana juya mata, ita Umaimah dai har tayi lalacewar da Khalil ya zabi karuwa akanta kuma yake iqirarin zeyi shari'a da ita saboda wata banza, ai kuwa seta tabbatar masa da be gama sanin wacece Umaimah ba, fili zata siya a gidan Radio da Jarida ta buga labarin idan yaso ya kaita Majalisar dinkin duniya ma qarewar Shari'a. Qwafa tayi tasaka Hijabi ta tayarda sallar da sam babu nutsuwa a cikinta saboda hankalinta gaba daya yana ga daukar fansa.

Tana idar da sallarta kira Rufaida, a taqaice tayi mata bayani Rufaida ta janyo Jimlar Ashar ta dire kafin tace
"An dira ki da ka Umaimah, kinfa san daman masu neman matan nan babu wanda ya kaisu bin Malamai da haka suke Asirce Yaran mutane suna lalata su toh Wallahi Khalil ma ta gama dashi dan dai kinsan da hankalinsa da mutunchinsa baze taba bari ko gaisuwa ta hadashi da irin matan nan ba. Se kin tashi tsaye kin rabasu in kuma ba haka ba kinaji kina gani za'a kwaso miki jangwangwama"

"Ai wallahi ko zan tafi tsirara Khalil be isa ya aureta ba, bama ita ba duk wata mace me daura zani da dankwali ita da Khalil sedai hange daga nesa dan nawa ne ni kadai ba Asiri ba ko tsafi Mace takeyi sedai ta gaji amma Khalil yafi qarfinta, ni kinga gobe inda ranka zan tafi na kai musu rahoto har address din unguwarsu dana inda take aiki duk zan hada na basu, badai Mahaukaciya ya cemun ba? Zega qarshen hauka kuwa" Umaimah ta fada se Rufaida tayi saurin tareta da cewa
"Aa karkiyi haka, wannan ma da mukayi ya isa. Ki ga ki bari gobe zanzo mu zauna se musan abinyi na gaba. Amma Su Mama basu san labarin nan ba ko naji baki ce komai ba?"

"Oho in ma sun sani banji kowa yayi zancen ba, jiya nema da Maman Asad tazo take maganar wai ta gani a Facebook suka taru sunata surutansu wai wadda ta yada bata kyauta ba wanda ya rufawa wani Asiri shima Allah ze rufa masa a raina nace kanku akeji na shige daki, duk tsiya dai zasu sani idan ta fashe kowa zeji ai" Umaiman ta sake fada daga nan suka qarasa shiryawa akan Gobe Rufaida zata zo dan haka ta dakata karta dauki wani mataki har se sun tattauna sannan.

Khalil

Be taba zaton rashin tunaninta yakai haka ba, koda ace Khausar ce ta shirya komai Umaimah tafi kowa laifi tunda ai ba mahaukaciya bace ita ko qaramar yarinya da bata san me takeyi ba, tayi amfani da wauta da rashin tunaninta ta sakata a matsala dan yanzu duk inda akaje aka dawo Umaimah ce a ciki ita za'a kama da laifi ba Khausar ba.
Tunanin kiran Khausar din yazo masa har yayi dialing number ya katse saboda yanzu idab har tasan yasan da hannunta a ciki zata nemi hanyar kare kanta ne, gara ya rabu da ita ta yanda z samu dama ya kanata a hannu cikin sauqi.

A daren ya hada dan abinda zeyi amfani dashi, yasan akwai jirgin Nigeria gobe dan a cikin wadanda suke aiki akwai wanda zasu taho goben take shima ya yanki ticketz ya rubuta uzurin cewar buqatar gaggawa ta same shi ta zuwa gida washe gari kuwa qarfe sha biyu na rana tayi masa a Kano bayan ya sake hawowa jirgi daga Lagos inda suka sauka. Already Jalilah daya gayawa dawowar tasa tana jiransa a Aipirt, ita ta dauke shi kai tsaye yace mata Na'ibawa zasuje yana mata kwatance har suka isa qofar gidan su Hadiza.
Chapter 104 · 0% Book details