← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 267

Sashe 174

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mutumina ka rage tunanin nan haka, kowa yana da damuwa idan mukace zamu saka a rai muyi ta tunawa qila kama tafe a hanya sedai kaga mutane kawai suna ta faduwa damuwarsu ta kashe su" Anwar daya gaji dayi masa magana ta yaba shi yana fada. Ajiyar numfashi yayi kafin ya tashi zaune da kyau yana cewa
"Damuwar ma kala kala ce Anwar, kai dai ka godewa Allah kawai da be jarabceka ta fannin aure ba, kaga duk wani jin dadin rayuwa to Macece cikonsa idan kuma har ka rasa nutsuwa a gurinta wlh ko kafi qaruna wadata da iko seka tawaya ta bangaren nutsuwar zuciya Allah dai kawai yasa mu dace".

Wayarsa ya zaro a Aljihunsa ya kunna dan yana isa ya kasheta saboda baya son Humaira tayi ta kira shi kuma baze iya magana da ita a cikin fushi ba. Tana gama kunnuwa kuwa saqonta ya shigo, qorafi takeyi akan yace ze kirata idan ya isa kuma ta sake kira wayar a kashe
"Ka kirani da ka kunna wayar idan ba haka ba babu ruwana da kai, I love you Yayana" ta rufe saqon dashi. Be san sanda ya saki murmushi ba babu bata lokaci kuwa ya danna mata kiran kamar tana jira ringing daya ta daga wayar da sallama kafin ta dasa masa kukan shagwaba. Seda ya kwashi wasu mintina yana aikin rarrashi tareda kare kansa akan dalilin daya saka be kiratan ba kafin ya samu ta haqura bayan ta kafa masa sharadin daya shiga Kano seya je gurinta shine hukuncin hanata magana da shi da yayi wuni guda.
"An gama my Boss lady, amma idan nazo me zaki bani kinga dai na gaji da yawa ki taimaka ko dan hug ne da kiss na samu mana" ya fada cikin sigar tsokana kafin ya kai qarshe kuwa har ta kashe wayar ya zareta daga kunnensa yana sakin dariyar dabe shirya mata ba. Kunyar ta tana burgeshi duk sanda yake son ya tsokaneta da yayi mata irin wannan maganar zata dauki fushi ita ala dole ya kauce hanya. Be gama dariyar ba kuwa saqonta ya shigo tana cewa
"Na fasa karkazo, kuma kayi iatigfari tunda aini ba matarja bace kake gaya mun wannan maganar".

Sake tuntsurewa yayi da dariya har yana dukan gaban motar, Anwar ya kalleshi da murmushi yace
"Gida biyu maganin gobara mutumina"
"Fadi ka qara Abokina musamman ace ka samu danyan jini duk wata damuwarka ta yaye wlh" ya bawa Anwar din amsa yana sake kiranta amma taqi dagawa. Haqura yayi dan daman baya so yaje din ne shi yasa yayi mata haka se ya kunna Datarsa ya shiga WhatsApp, hotuna ya gani Jalilah ta tura masa ya bude yana ganin abinda yake ciki ya zaro ido tareda dafe bakinsa saboda mamakin abinda ya gani. Motarsa akayiwa haka? Bashida buqatar tambayar wa yayi dan yasan yar dabar daya ajiye a matsayin mata shi kansa zata iya masa haka ba motarsa ba se ya kashe Datar kawai ya fita daga WhatsApp din yana qoqarin hana bacin ran sake dawo masa.

Daya isa gidan ma kallo daya yayiwa motar ya hadiye wani abu me daci ya wuce, da Hajiya tayi masa maganar ma kai tsaye ce mata yayi
"Kiyi mun Addu'a Allah ya maidamun da mafiyinta" yayi shiru.
"Amma Babana haka zaka zuba mata ido ta ringa barnatar maka da dukiya babu gaira babu dalili?" Hajiyar ta sake fada seya miqe yana murmushi yace
"Wancan karon fa Hajiya ke kikayi mun fada akan me zanyi fushi saboda na rasa wani qyale qyalen duniya, wannan ma ba rabo bace shi yasa hakan ya faru da ita. Gobe kawai zan kora company suzo su dauka su bani abinda ya samu dan banida kudin da zan iya gyarata gara kawai na siyar yanzu dai ni ya maganar da mukayi jiya kin kira Baba Abu din?" Ya canza maganar da wata. Seta sauke numfashi tana kallonsa. A idonsa ta karanci bacin ransa amma ya danne ya nuna komai ba komai ba. Numfasawa tayi tace
"Na kirashi yace babu damuwa ze samu sauran kawun nanka suyi magana se suji sanda ya kamata suje din kuma gurin wa zasuje"

"Kuyi magana da Maman kawai Hajiya ita zata gaya miki duk ma inda zasuje, sannan dan Allah ina roqon Alfarma idan sunje karsu bari a saka lokaci me tsaho Hajiya, duk abinda za'ayi karya wuce wata biyu" ya fada kansa a qasa kafin ya miqe hahiyar tace
"In sha Allahu, Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi sannan kayi haquri da abinda ya faru Babana taci Albarkacin zuri'a".
Murmushi yayi mata ya fice daga part din ya wuce nasu.

Yana shiga dakinsa yaji kansa ya sara, ya dafe kan yana kiran sunan Allah ya zauna a gefen gado yana jin bugun zuciyarsa yana qaruwa, a hankali ya tashi ya fita palour, ruwa ya tsiyaya yasha dan ya fi ta'allaqa bugawar kan da gajiyar da yayi ga bacin ran da yake ciki Allah yasa ma ba jininsa ne ya hau ba. Seda yayi wanka yayi sallar Magriba kafin ya zauna cin Abinci. Kallon tuwon yana jin yunwa amma gaba daya abinci ya fita a ransa bacin rai ya cika masa ciki taf kuma bayaso ya fitar dashi anyi masa ne da gayya dan yayi magana shi kuma ya qudurce baze ce mata komai ba ze tarata yana kuma dab da ramawa. A hankali yayi bismillah ya fara cin tuwon, kadan yaci ya ture ya tsiyaya shayi a cup ya koma cikin falon ya zauna. Yana fara sha aka kira sallar Isha seya ajiye ya fita, Umaimah dake tsaye bakin qofarta tun zaman Khalil din tana ganin fitarsa ta fito daga dakin. Cup din shayin ta dauke ta wuce kan Dining ta maidashi cikin butar shayin kafin ta dauka ta kai kitchen. A sink ta korashi, ragowar wanda bata saka komai ciki ba ta dumama ta maida masa dan tasan be gama sha ba ta sake dakko flask din miyar shima ta zubarda ta ciki ta maida wata ranta duk a dagule.

A falon tayi sallah ta zauna a gurin harya shigo, kallo daya yayi mata ya wuce gurin Dining din ya tsaya yana kallon kayan dake gurin. Yana da tsananin lura da abu, ko takadda ya ajiye aka canza mata mazauni yana ganewa dan haka nan take ya fahimci da an canzawa kayan yanayi. Butar shayin ya bude dan ya tabbatar da zarginsa ilai kuwa yaga yawan wanda yake ciki ya zarta wanda ya bari kamar ma be taba ba. Kallon Umaimah dake h
Jan carbi yayi ya girgiza kai a ransa yace
"Idan ma kasheni kike so kiyi nayi shahada ke kuma kiji da dakon haqqina" ya maida murfin ya rufa ya haye sama yana jin wani iri a jikinsa. Gaba daya ji yayi ya kasa nutsuwa se kawai ya dauki muqullin motarsa ya fita. Ya fahimci Umaimah tayi nisa ba yanda ya santa bace a baya, wannan Umaiman ta yanzu zata iya aikata komai akan cikar muradinta.

Asibiti ya wuce, be samu nutsuwa ba seda akayi masa gwaji aka tabbatar masa da babu wani abu me kama da guba a jikinsa kafin ya sauke a jiyar zuciya a ransa yana zargin kansa da yi mata rashin Adalci. Me yasa ze zargeta akan abinda bashi da tabbaci? Ta yuwu an maida wanda ya zuba ya fara sha ne ciki shi yasa yaga shayin ya qara yawa sannan an kwashe plate din daya bata dole zata gyara zaman kwanukan. Yasan ma Ruqayya ce tayi amma zuciyarsa ta tafi ga zargin Umaimah tayi masa wani mugun abu. Hakannan yakeji be kyauta mata ba, can qasan ransa wata soyayyarta ta qara motso masa yana tafe a hanya yana tunani Ya sani Umaimah tana sonsa kuma tabbas se ana son mutum ake kishinsa kenan soyayyarsa ce ya janyo take aikata duk wadan nan abubuwan idan har ya karbeta a yanda take zasu zauna lafiya ya yarda ya kuma karbi laifin akan cewar shi yake tsokanota a koda yaushe har take sauka daga layi tayi abinda kowa yake ganin bata kyautawar.

Wasu tunani barkatai suka shiga gewaya masa kwakwalwa, yanda kasan wanda Iska suka shiga haka ya kama hanyar gida jikinsa na rawa dan so kawai yakeyi yaje ya bata haquri ya kuma gaya mata duk abinda ya fada mata dazun wasa yakeyi tayi haquri su zauna lafiya. Daya isa gidan ta koma daki ya murda qofar yajiya a kulle, a hankali ya shiga bugawa, kusan minti biyu yana bugu bata bude ba jikin qofar ya tsaya ya shiga kiran sunanta nan ma shiru haka ya haqura ya wuce sama ransa duk babu dadi. Raba dare yayi yana tunanin halin da take ciki, daga qarshe dayaga ya kasa bacci ya miqe yayiwo Alwala, yana tayar da sallar dakyar ya kai raka'a biyu yana sallamewa bacci me nauyi ya kwashe shi a gurin.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 64

Hasken ranar daya galle masa ido ne ya farkar dashi ba tareda ya shirya ba. Dakyar ya iya bude idanunsa da sukayi nauyi yanda kasan wanda ya kwana be runtsa ba, yabi dakin da kallo, hasken daya gani ya tabbatar masa da cewar safiya ta rigada tayi cikin hanzari ya miqe yana istigfari wayarsa dake kan mudubi ya janyo ya duba lokaci qarfe bakwai harda minti Arba'in seya ajiyeta ya shige bandaki da sauri a ransa yana mamakin meya shiga kansa haka?
Chapter 174 · 0% Book details