← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 267

Sashe 211

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Anty Hafsan ta ringayi harta gama sababinta kafin a hankali idonta ya ciko da kwalla tace
"Idan kin kwantarda hankalinki ma Anty hafsa ni nasan tawa ta qare a duniyar dan idanhar Khalil ya mutu da gaske nima mutuwa zanyi"
"Dallah rufe mun baki maqaryaciyar banza, Idan Khalil ya mutu zaki mutu sannan har ki nemi ransa da hannunki saboda kin rainawa kanki hankali to idanso kikeyi ki tabbatar da qudurinki to bakici nasara be mutu ba yana nan da ransa Allahya kubutar dashi daga sharrinki ya kuma raba shi da Uqubar auranki. Kaiconki Umaimah, tunda kika yiwa kanki sanadin rabuwa da nagartaccen Mutum kamar Khalil har ki mutu ba zaki maida makwafinsa ba idan kuma baki tubarwa Allah ba haqqinsa baze taba barinki ki zauna lafiya ba" Anty Hafsa ta sake hayayyaqo mata cikin daga murya da har seda wata Nurse ta shigo tana cewa
"Haba baiwar Allah ya zaki ringa yi mata ihu akai bayan an gaya miki tana da buqatar hutu da kwanciyar hankali a yanzu? Idan ba zaki iya kulawa da ita ba ki tafi wata tazo amma ba zakizo kina ma patient dinmu ihu akai ba"

Banza tayiwa Nurse din data matsa gurin Umaimah dake kuka a hankali tana rarrashinta da abin ya isheta ta fita ta bar musu dakin badan Mama cetace ta zauna ba bataga abinda ze saka tayi jinyar Umaimah ba.
Umaimah kuwa dakyar Nurse ta lallabata tayi shiru, ta kalli Nurse dinda idonta da yayi jage jage da hawaye tace
"Nurse Dan Allah ki taimakmun ki kaini naga halinda Mijina yake ciki shine kadai abinda ze saka hankalina kwanciya dan Allah"
"Kiyi haquri kinga yanzu kika farka jikinki na buqatar hutu ko magana da kikeyi yanzu da yawa be kamata ba ki yi haquri zuwa gobe idan kika ji qarfin jikinki se a kaiki ki ganshi" Nurse dinta fada mata cikin lallashi.

Washe gari da Safe ta kwarzabi Nurse akan seta kaita taga Khalil, jijjiga gadon da take kai ta shigayi saboda tsabar takaici daman Anty Hafsa fita ta sakeyi ta bar musu dakin Nurse din ganin Umaiman na neman ta janyo musu sabon Aiki bisa tilas ta kirawo Dr, jijjigar qarya ta shigayi babu shiri ya basu Umarnin su turata akan Wheel chair su kaita dakin da Khalil yake, haka Nurses din suka fita da ita cike da zumudin ganinshi take, kwata kwata bata tuna wani abu makamancin saki ya gifta tsakaninsu Allah Allah take ta ganshi taga lafiyarsa a haka suka shiga dakin da aka kwantar da Khalil din a bangaren VVIP.

Yana zaune akan Gadon ya jingina bayansa da Pillow da aka saka masa dan ya bashi support Humaira na zaune a gabansa da bowl me dauke da Quaker oat tana bashi a hankali wani kalar tsadadden murmushi ne akan fuskarsa yake jifanta dashi a wannan yanayin Umaimah ta riske su wani abu me kama da saukar Aradu ya dirar mata a zuciya take komai ya tsaya mata wani tuquqin baqin ciki ya tokare mata maqoshi ta kasa cewa komai nan da nan hawaye suka balle mata.

Khalil daya ga shigowarsu lokaci daya murmushin dake kan fuskarsa ya disashe. Ya zuba mata ido yana kallonta wani abu me kama da tsanarta yana mamaye tarin soyayyar da yake mata a baya. Ganinya zubawa bakin qofa ido ya saka Humaira kallon gurin itama a tsorace ta saki Bowl din hannunta a qasa abinda yake ciki ya zube Jikinta ya dauki rawa saboda ganin Umaimah hannu biyu Khalil ya saka ya kama kafadunta yajata ta fada jikinsa ya lumshe idanunsa da suka fara canza kala saboda bacin ran ganin Umaimah.
"Ku fita da ita" ya fada a hankali ba tareda ya bude idonsa ba Nurses din da suka zama hoto suka shiga tura Umaiman dake kuka kamar ana zare mata rai, baqin cikin abinda Khalil din yayi a gabanta kamar ya kasheta da ace zata iya tashi tsaye kan qafafunta da babu abunda ze hana ta janyo yarinyar nan daga jikinsa tayi mata dukan mutuwa. Wai me yasama ba ita ta kwalawa abun akai ba ta mutu kowa ya huta?

Da wannan tunanin suka maida ta dakin da take, Anty Hafsa taja tsaki ba tareda tace musu komai ba. Nurse nagama maidawa Umaimah drip Jalilah ta shigo dakin kamar an korota ta nuna Umaiman da yatsa tace
"Ki kama sauran mutunchin daya rage miki karki kuskura ki sake rabar dan uwana. Aurene ya hadaku kuma ya sawwaqe miki Ubangiji ya sake gajarta tarayyarku ya yanke Miki iddarsa kinga babu sauran Kare bin damo idan kuma ba so kikeyi ki hasalamu mu dauki matakin daya kamata a akanki ba ki fita daga rayuwarmu Umaimah, iya daukar Alhakinmu da kikayi Allah yabi mana haqqinmu amma bama buqatar ki sake rabarmu har abada" tana gama fadar haka ta juya ta fita Umaimah ta bita da kallo cikin kaduwa da kalamanta.

Tabbas bata manta Khalil ya saketa ba amma bata yarda cewar aure ya qare a tsakaninsu ba. Ta sani Khalil yana sonta itama tana sonsa duk abinda ya faru tursasashi akayi amma badan ra'ayinsa ya saketa ba kuma tasan baze taba haqura da ita ba duk ma a yaya ze dawo su ci gaba da rayuwarsu. Ranar wuni tayi zuciyarta babu dadi, idanta tuna wai babu igiyar auran Khalil akanta se taji kamar tayita kurma ihu. Ita dai Anty Hafsa tafi ki mutu batace mata, idan kaji tayi magana yan dubiya ne sukazo wanda da yawa tsurku ne yake kawo su saboda irin labarun da suke ta yawo a gari.

Randa suka cika kwana uku a kwance ranar Abba da Mama suka sake komawa duba Khalil, Hajiyarsa ma an sallameta tun washegarin ranar ta koma gida shida Umaimah ne a kwanceda jaririyarsu da itama a ranar aka fito da ita dan Alhamdulillah jikinta ya murmure ta samu sauqi. Jalilah ce ta karbota kai tsaye ta wuce da ita dakinda aka kwantar da Khalil din yana zaune bayan Humaira ta gama bashi abinci sun tafi gidada Jamila saboda ita ta kwana dashi ranar Khalifa ya tafi wani aiki ta shiga da Babyn ta miqa masa ya karbeta yana kallon kyakykyawar fuskarta sak Umaimah.

"Kamar uwarta tayi kaki suna bani ita nayi addu'a na tofa Mata Allah yasa ta tsaya a iya kamannin karta kwaso baqin hali irin na uwarta" Jalilan ta fada Khalil dai kallon yarinyar yakeyi wata irin qaunarta me zafi tana shigarsa. Sallamarsu Abban ce ta katsewa Jalilah Mitar da takeyi, cikin girmamawa ta gaishesu dan duk abinta ba zata zargi Iyayen Umaimah da saka hannu a cikin abinda yarsu take aikatawa ba. Dattijai ne gaske da suka nuna hakan a cikin al'amuransu. Iyakacin jajaircewar da sukayi gurin tabbatar da samuwar yancin Khalil ya isa ya qara siya musu qima da mutunchi a idon kowa.

Ta karbi Babyn daga hannunsa ta bawa Mama ta karbeta tana kallonta itama tausayin yarinyar ya kamata ta fado a yanayi mara dadiz tazo a ranar da Uwa da Ubanta suka raba hanya.
"Masha Allahu Allah yasa ko dakko Haliyyar kwarai ta mahaifinki tunda kinyi karar dakko fuskar mahaifiyarki" Abba ya fada har zuciyarsa bayan da Mama ta miqa masa yarinyar ya sake kallon Khalil bayan yayi masa ya jiki yace
"Wane suna kukayi mata huduba dashi"
"Daman sunan Mama za'a saka mata ba'a rigada dai anyi hudubar ba" Khalil ya fada a sanyaye se Abba ya dagata yana cewa
"Allah ya raya yayi akbarka yasa ki gaji me sunanki gurin haquri" Jalila da Khalil suka amsa da Amin. Sun jima sosai a dakin suna sake tattaunawa har zuwa sanda wasu Abonana Khalil suka zo dubashi kafin suka fita har sannan yarinyar na hannun Abba.

Bisa tursasawarsa Mama ta bishi dakinda Umaimah take, tana kwance kan gado ta zubawa Bango ido dan ta mayar da kanta kurmar qarfi da yaji, jinyar zuciyarta kawai takeyi ta daga kai ta kalli Mama da Abban da suka shigo da Sallama Nuratu da Anty Hafsa suka amsa tareda basu gurin zama suka shiga gaishe su. Seda Umaimah ta dauke hawayen daya zubo mata kafin cikin rawar murya ta shiga gaida iyayen nata. Abba ya amsa a gajarce Mama kuwa daman ko kallon inda take batayi baya miqawa Nuratu yarinyar yana cewa
"Ga ta Mahaifiyarku yayiwa takwara"

"Ni bana so sanda na ce ya saka mun ai be saka ba ya je ya canza mata suna infact ni bazan riqe masa yarsa badai ya sakeni ba yaje ya kaiwa Hajiyar ita ko matarsa su riqe masa amma wlh bazan shayar masa da Ya ba" Umaimah da basu saka ta cikin maganarsu ba tayi tsugul ta amshe tana gama fada ta rushe da kuka me sauti kamar daman jiran dalilin yinsa takeyi. Kallonta sukayi gaba daya, Abba ya sauke ajiyar zuciya Mama kuwa sake maida kai tayi tana kallon qofar fita badan tana kokawa da shaidan dake mata hububar tsiya ba da qila tsinewa Umaimah zatayi tabi duniya kawai kowa ya huta. Ganin tana neman caza musu kwakwalwa babu gaira babu dalili gaba daya suka fice suka barta a dakin tana kuka tamkar ranta zefita. Turo qofar akayi ta daga kai bazato suka hada ido da Safina data shigo dakin a kidime kamar an jefota.

Gajiya tayi da kiran Umaimah a waya bata samu yau taje gidan Sammani ya shaida mata Umaiman tana Asibiti bata da lafiya hankali tashe ta nufo wajenta ta taki sa'a Umaimah na neman wanda zata kwance sauran haukan daya rage mata a kwakwalwa.
Chapter 211 · 0% Book details