← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 267

Sashe 45

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umaimah lafiyarki kuwa" Khalil ya fada yana jijjigata ganin yanda ta zura masa ido tana hawaye tunda ya bude qofar ya shiga har ya isa gabanta bata motsa ba yanayinta kuma ya tabbatar masa da bata cikin hayyacinta.

Ajiyar zuciya me qarfi ta saki kafin ta fada jikinsa ta fashe da kuka kamar wadda aka kwadawa Mari, yanda take kukan har jikinta na rawa ya dagawa Khalil hankali babu shiri ya shiga karanto addu'oi yana tofa mata dan abinda zuciyarsa ta bashi gamo tayi dan haka ya dage yana karanto Addu'oin tsari yana tofa mata Umaimah kuwa banda kuka babu abinda takeyi, idan ta kalli fuskar Khalil ta tuna abinda matar can ta gaya mata seta sake rushewa da kukan.

Ganin da yayi bazatayi shiru ba ya kuma tabbatar in har shaidanu ne dagaske irin addu'ar daya tofa mata zasu lafa sedai idan nata shedancin ne ya motsa dan haka ya jata gefen gado ya zaunar da ita yana cewa

"Ya isa kiyi shiru menene?"
Seda ta kwashi kusan wasu mintuna biyar kafin ta fara tsagaita kukan tana jan shashsheqa da Ajiyar zuciya.

"Babe, kiyi magana meya same ki dan Allah wani abu ya faru a nan ko a gida?" Ya sakw fada cikin sanyin murna dan ya fara tsorata da kukan nata kar fa wani mugun abun ne ya faru da ita ko bayan fitarsa.

Dakyar Umaimah ta iya bawa kanta haquri ta fara magana cikin muryar kuka tace
"Ba wata mata ce ba haka kawai tace wai in sha Allahu se kayi mun kishiya kuma..kuma ta kwace mun kai sedai na zama yar kallo, na rantse da Allah duk inda take a Nigeria sena nemota naci ubanta, sena nuna mata ni ba sa'ar ta bace idan ma itace take shirin shiga rayuwarka zan dakatar da ita sena mata abinda ko ance ta sake kallon mijin wa...."

"Ke da Allah ya isheki haka" Khalil ya fada a fusace yana janyeta daga jikinsa,idan da ace yasan sakarcin da yake damunta kenanda ko dakin baze shigo ba ze juya abinsa. Ya kwaso gajiya tunda ya fita tsaye yake akan qafafunsa shine zata qara masa wani zafin da wauta da rashin nutsuwarta, tsaki ya sake ja me qarfi ya shige bandaki ya bar Umaimah da tunda yayi mata tsawar ta saki baki tana kallonsa.

Wankansa yayo da alwala ya fito daure da towel a qugunsa har sannan tana tsaye fuska shabe shabe da hawaye kamar wata qaramar yarinya ya wuceta ya bude qaramar Akwatinsa daya sako abubuwan buqata tana ajiye yanda suka shigo da kayan bata motsa su ba sema tata Akwatin data bari a bude data dauki Hijabi. Vest da Boxers ya dauka da jallabiyya se mai da turare ya koma gefen gado ya shiga shiryawa, tamkar babu wata halitta a dakin haka ya shareta ya gama shirinsa tsaf ya dauki wayarsa ya nufi qofa daidai lokacin da aka kwada kiran Sallar Magriba Umaimah da ta sandare a tsaye babu La'asar ga Magriba tayi ta bi bayansa da sauri tana cewa

"Ina zaka tafi kumaka barni?"
"Masallaci zanje" ya fada yana bude qofar ya fice gaba daya ransa babu dadi. Duk irin burin daya gama ci akan zuwan su Kd baya tunanin ko daya daga ciki ze tabbata, yanzu dawowa yayi da niyyar idan sukayi sallah su fita yayiwo mata shopping kayan sakaqa tunda ya ce karta dakko amma bayajin ze iya dan in sun fitana bacin raine kowannen su ze sha dan bazata fasa abinda ta faro ba shi kuma ya dena daukar shirmenta dan ya kamata ace yanzu tayi hankali ta gane daidai da rashinsa.

Daya idar da sallar a Restaurant din Hotel din ya zauna yaci abinci ransa a jagule musamman yanda yaga mutane kowa da yar matarsa ko budurwa suna cin abincinsu suna nishadi, daya gama ma waje ya fita can inda suka zuba kujeru ya zauna se kusan qarfe tara ya koma dakin nasu.

Umaimah kuwa bin bayan Khalil daya rufe qofa tayi da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya ta koma jiki ba kwari ta zauna ta rafka tagumi, yanzu kuma meye abinda ya bata masa rai shi kuma? Amma koma menene waccen matar ce ta jawo kuma tayi alqawarin setaci uwarta wallahi bari su koma Kano zata biya kudi duk inda take a lalubo mata ita toh shi kuma da yayi wanka ya fesa turare ina zashi daga masallacin?

Kuka wiwi ta dasa, seda tayi dagaske ta iya tashi tayo Alwala tana sallar tana goge hawaye tana idarwa ta haye kan gado taci gaba da kukan dukda yunwar data ji tana taso mata har sannan kayan data zo dasu tun safe ne a jikinta, dakin data tarar tsaf ko ina a kintse ta hargitsashi da shirgi.

Tafi qarfin awa daya tana aikin kuka har akayi sallar Isha'i bata motsa daga inda take ba tana ji ana buga qofar daga waje tayi banza dasu dan tasan idan shine yana da katin qofar a hannunsa sedai ko Ma'aikatan Hotel din, idan ta tuna gurin wata ya tafi ya kulleta a daki seta sake rushewa da kuka zuciyarta nayi mata suya, Wani tunani ya zarga mata ta miqe da sauri ta isa jikin window da yake kallon Harabar hotel din inda swimming pool yake tuni gurin ya fara cika da mutane saboda duhun dare yayi ga motoci nata shigowa Mata nata yawo da shiga kala kala yanzu a haka ya ratsa su ya fita a ina ma masallacin daya ce zashi yake?

Anya ba bakin da waccen yar iskar tayi mata bane ze fara kamata wata budurwar Khalil yayi shine ze ce mata ya tafi Masallaci dan ita dai bata ga alamar masallaci a cikin hotel din nan ba ko kiran sallar da take jiyowa tana ganin daga waje ne amma ba a nan ba ai kuw fita zatayi ta nemo duk inda masallacin yake ta tsaya ta jirashi, juyawa tayi zata bar gurin seta koma da sauri saboda hango wani da tayi kamar shi a zaune.

Ido ta gwalo tana kallon sa, Khalil din ne a zaune ga wata yarinya a tsaye gabansa ta saka wata shegiyar rigar Atamfa bata ga fuskarta ba amma ta ga bayanta da dikin ya matse tsam kamar idan ta sunkuya rigar zata yage suna fuskantar juna shida ita idan ba gizo idonta ya mata bama hannayensu take gani kamar a sarqe.

Wani jiri taji ya kwasheta ta kama qarfen window ta riqe da kyau tana jera numfashi kamar wadda tayi tsere kamar kuma wadda aka tsikarawa Allura seta juya da sauri ta zari Hijabinta dake kan sallaya har tayi gaba ta hango wuqar data yabka Apple da ita akan Plate ta dauka dukda bata san me zatayi da ita ba haka ta nufi qofa batareda ta saka hijabinba ta dai riqe a hannu.

Daqarfi ta finciko qofar zata bude ta jita a bame, ta jijjiga ta gama murde murdenta qofa taqi buduwa take ta fahimci ya kulleta ne ta waje saboda yasan abinda ze fita aikatawa. Dukan qofar ta shigayi kamar mahaukaciya tana kuka amma ko gezau qofa batayi ba dan kanta ta gaji haka ta fada kan gadon tana ci gaba da kuka tamkar ranta ze fita nan da nan ciwon kai da zazzabi suka rufeta cikinta ya murda kafin kace me ta shiga kelaya Amai akan gadon har tana neman shidewa saboda yanda ya taho mata har ta hanci daidai sanda Khalil ya bude dakin ya shigo hannunsa da ledojin abincin daya taho mata dashi.

Da sauri ya dire ledar yayi kanta yana salati ganin yanda take yunqurin kamar zata amayar da kayan cikinta, ya ruqota ta fincike dukda yanayin galabaitar da take ciki be hanata harararsa ba ta ce
"Karka tabani da qazamin hannunka da kaje ka taba karuwa dashi"

Be damu da kalanta ba ya sake matsawa yana qoqarin riqota yace
"Umaimah ki tsaya na taimaka miki jikinki yayi zafi, ki bari muje Asibiti kinsan dai bake kadai bace ko" amma ina ta fitittike ta shiga kai masa duka tana kuka da zaginsa akan yaci Amanarta a kan idonta taga ya riqe karuwa kuma tsahon lokacin nan daya dauka qila daki suka kama wallahi seta kashe kowacece ai ta ganeta shidai be kulata ba kamota yake tana zillewa dayaga tana neman bashi wahala ya saka mata qarfi gaba dayanta ya dauketa ya shige toilet da ita, jikinta ya rigada ya saki saboda Zazzabi da kuma Aman da tayi se bakinta ne be mutu ba, babu yanda ta iya yayi mata wanka tas tana kuka da koma ya saka mata qaramar Riga da Hijabi ya sake daukanta a kafada ya fita da ita suka wuce Asibiti

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wannan wace irinmasifa ce" Khalil ya fada yana dafe kai saboda yanda Umaiman ta ware Murya tana masa ihu a mota tana zaginsa kamar wanda ya satota, a fusace ya juya ya kalleta ya daga hannu kamar ze kwada mata mari yace

"Na rantse da Allah idan baki rufe mun baki ba sena tattaka ki a nan karki dauka tsoronki nake da yasa nake rabuwa dake kina mun duk iskancin da kika ga dama,mata kuma yanzu na fara kulawa tunda baki da amfani baki iya komai ba se tashin hankali da masifa kala kala, mtsw" yaja tsaki.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 22

Tsit tayi saboda ta tsorata dan yanda yayi mata magana seta maida kanta ta kalli window taci gaba da share hawayen da suka qi tsaya mata, idan ta tuna ganin da tayi masa da karuwar dazu se taji kamar ta shaqeshi idan yaso motar ta kwace masa su mutu gaba daya kowa ya huta amma yanda ya hade girar sama data qasa ta saka ko motsi me kyau ta gagarayi, alwashi taci a zuciyarta wallahi se ya gane kurensa.
Chapter 45 · 0% Book details