Sashe 80
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qarar wayarsa ta maidoshi daga tunanin daya tafi, seda ya saci kallonta yaga tana tattare kayan abincin Mu'ayyad din kafin ya daga da sallama yana cewa
"Ina abu ne idan na gama zan kira" ya shige daki Umaimah da tun daga wayar tasa tayi sak dan sarai ta ga yanda fuskarsa ta canza ta bishi da kallo.
Bata so ta bar zuciyarta ta ayyana mata abinda ba shikenan ba amma yanda Khalil din yake abubuwa sun fara bata tsoro. Jiya kiran da aka masa yana cin abinci yanda ya rikice ya bata mamaki, sannan fitar da yayi ta kirashi taji call waiting tasan Khalil ko wayar aiki ce qarqarinsa qafe goma baya attending mutane bayan nan amma jiya sha daya ta gota sanda ymta kirashi call waiting dukda yace da Mukhtar yayi waya sannan A iya saninta dashi komai dare baya kashe waya se gashi jiya ta danna wayar da niyyar ganin lokaci ta ganta a kashe, tayi masa uzurin ko chaji ne ya qare gaba daya ta mutu kuma daya saka be kunna ba amma taga da safe harya futa tana lura bataji an kirashi ba kuma shima bata ga yayi amfani da wayar ba ga kuma na yanzu, dukma abinda yake boyewa ko yakeyi zata bincika idan kuwa taga abinda ba haka ba tashin hankali ne ze siyowa kansa dan ya santa bawai chanzawa tayi ba.
Khalil kuwa daya shiga daki Text yayiwa Hadiza akan tayi haquri ze kirata da safe yanzu ya rigada ya shiga gida tayi masa reply kan babu komai yana karantawa ya goge duka messages dinta, call log din ya shiga nan ma ya goge kiran da tayi masa har ya aje wayar wata zuciyar raya masa ya goge lambarta gaba daya bayan ya kalleta da kyau ya haddace haka yabi ya goge chat dinsu na WhatsApp ma sannan yaji hankalinsa ya kwanta.
A qasa ya ajiye Mu'ayyad ya kunna masa carton a Tv dakin ya shiga wanka, yana shiga ta tura qofar dakin ta shiga kai tsaye idonta ya sauka akan wayarsa dake ajiye akan gado, seda taje jikin qofar ta kasa kunne taji alamar saukar ruwa kafin ta dawo da sauri ta dauki wayar, call log ta shiga, lambar farko dataga an kirashi ta kwafe a wayarta cikin sauri ta shiga gurin messages tana yi tana kallon qofar bandakin ganin idan ta bata lokaci ze iya fitowa ya tarar da ita yasa ta ajiye masa wayar bayan ta goge shaidar da ze gani na ta bude wayar. Dakinta ta wuce tana shiga ta dannan kiran number data kwafo wayar ta shiga ringing seda ta kusa katsewa aka daga
Muryar Namiji ce daga ji ma ba bahaushe bane. Tambayarsa tayi ina me wayar yace mata shine, bata yarda ba ta sake ce masa Amina take nema yace shi besan wata Amina ba wannan layinsa ne sedai idan tayi missing number. Har zata kashe ta sake tambayarsa dan Allah waye shi toh dan dukda tabbacin daya bata na layinsa ne bata gama yarda ba, a fusace yace mata sunansa Bala kuma shi Electrician ne ya kashe wayarsa seta sauke ajiyar zuciya tanajin hankalinta ya qara kwanciya. Qila cikin jama'ar da suke kwangila ne masu aikin wuta kenan wani ya kirashi.
Palout ta fito jin yana kwala mata kira ya bata Mu'ayyad da yayi pupu ashe babu Diaper a jikinsa ya wanke masa ya sake masa wanka yace tayi masa shirin bacci. Ranar ma dai haka suka sake kwanciya kowa na juyi da murqususu a gado. Khalil ya qudure in har Umaimah bata bashi haquri akan abinda tayi masa ba ze zuba mata ido daga gaisuwa babu abinda ze sake shiga tsakaninsu haka itama ta ja nata layin dan ta san duk abinsa dole ya haqura ya sakko baze iya dogon fushi da ita ba, tana lura da yanda yake kwana wanka da shan Lipton da lemon tsami idan safiya tayi ta sake gigita masa kwakwalwa da zafafan shigar da takeyi sedai ya fita ya bar mata gidan wannan kuma tasan na dan lokaci ne dolensa ya bada kai bori ya hau a haka ya cinye hutun sati daya da aka bashi kafin yaci gaba da zuwa aiki office dinsa na nan Kano.
Tunda Sukayi maganar Hadiza da Hajiya ya fara jada baya da ita yawan wayar da sukeyi duk ya rage dan yana tsoron ta zargeshi da laifin yaudararta a gaba idan ya kasa shawo kan Hajiyarsa akan lamarin.
Tun tana yarda da uzururrukan aiki da yake bata ko kuma wani lokacin yace yana gidan idan ta kira harta fara gane kawai yana qoqarin yakiceta ne daman tun wancan zuwanda yayi gidansu ranar daya dawo be sake komawa ba ya dai je office dinsu sau biyu har suka je cin abinci a zuwansa na biyun tareda ita da Khausar a ranar ne yake nuna musu hoton Umaimah da Mu'ayyad Khausar din take tambayarsa ina Madam Hadiza tace har yanzu be hada su sun gaisa ba shine ya nuna musu hotonsu da suka dauka tare.
A hannun Khausar ya bar wayar tanaci gaba da kallon Hotunansu se zuzuta kyan da sukayi takeyi shi kuma suna yar hirar su da Hadiza seda lokacin break ya qare sannanya mayar dasu gurin aiki shi kuma ya wuce Site dan ranar be zauna a office ba.
A ranar chan gida kuma Umaimah ta karbi baquncin yayyenta Maman Asad, Yaya Naziyya data shigo Kano se Yaya Nuratu. A daki suka sakata suka fara dayi mata wankin babban bargo dan duk cikinsu babu wadda tasan zaman da Umaiman tayi a gida se daga baya. Yaya Naziyya na Minna, Maman Asad taje Umarah daman ta Somotto suka tafi garinsu Mijinta da suka dawo ma can suka yada zango Nuratu kuwa aiki ya hanata Sakat Mijinta ya tafi wani aiki ita take riqe masa Call tayi nata tayi nasa shi yasa bata samun lokacin kanta balle taje ko ina shiyasa basu sani ba seda Yaya Naziyya tazo Maman take gaya mata babu shiri ta kirawosu mitin din gaggawa.
"Amma Mama idan da laifin Umaimah kema da naki, na rasa wai fin qarfinku yarinyar nan tayi ko tsoronta kukeji da kuke zuba mata ido tana duk iskancin data ga dama. Me yasa sanda tazo baki saka ta a gaba ta kira Mijin kiji da kunnenki dagaske shi yace ta taho gida ba idan taqi kuma se ki kirashi ko ki gayawa Yaya Aminu? Gaskiya Mama sekun sake lale akan lamarin Umaimah idan ba haka ba kuma wallahi gaba se tayi abinda kowa zezo yana ya za'ayi tunda bata da tunani, ganin kuma idan tayi tana cin banza ya saka kullum iskancinta gaba yakeyi ba baya ba" Yaya Naziyya ta fada sanda Maman ta gama gaya mata yanda akayi washe gari da safe shine suka rankaya suka tafi gidan.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS🧕🧕*
*💞Barkan mu da warhaka en uwa mata, bugu da qari ba kadai a bangaren kayan gyaran aure ingantattu ta tsaya ba, ta na bada magunguna na musulunci akan cututtuka na yau da kullum wanda suke damun al'umma.*
*Cututtuka irin su matsanaicin ciwon mara a lukuta mabanbanta ko kuma lokacin al'ada, daukewan al'adan lokacin daukewan bai zo ba, al'ada ya rinqa wasa, rashin sha'awa ko ciwon kai, ciwon qirji wanda aka rasa gane kanshi ana tunanin ulcer ne, kuma anyi maganin amma har yanzu ba a dace ba, matsalar Ashiq wato aljanin soyayya(wannan sai bayan tambayoyi sannna za a tabbatar). Ciwon ciki, hawan jini, ciwon sugar, ciwon hanta, typoid/malaria, basir, ciwon baya da qafa, ciwon qashi da kuma matsalar infertility, duk da haihuwa Allah ne ke badawa amma kuma a wasu lokutan akwai cututtuka da kan kama mahaifa ko kuma reproductive system din mace wanda su kan iya hanata daukan ciki. Cututtuka irin su Endeomatriosis, cervicitis, fibroids, etc.*
*Ku karzayo domin lafiya uwar jiki💪💪, sannan ta bangaren gyaran aure, sumayyas herbal ta lashi takobin qara zage damtse wajen inganta kayayyakin ta domin samun maslahan ku a* *rayuwar ku da auratayyan ku. Aure dai ibada ne a don haka gyaran aure wajibi ne, musamman idan kin samu in da zaki gyara kan ki da kayayyaki na kwarai wanda basu da illa ga lafiya kuma ba irin kayan da zasu Kai ki ga halaka ba,su saki rasa imanin ki duk wai da sunan gyaran aure. Ah ah er uwa ayi hattara kar garin neman gira a rasa ido.🧏🏻♀️ Allah ya tsare mana imanin mu🙏🙏*
*Garzaya ki dannan link din kuma kiyi saving number ta domin kuwa akwai alfano mai yawa.*
*Wa.me/+2347031876677*
*Ko kuma akan Instagram*
*https://www.instagram.com/p/CqQJVrVIdjq/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==*
*Allah ya biya mana buqatun mu na alkhairi amin.*
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼
Page 35
An ci babbar Sa'a sun tarar da ita tana zaune a palour tana danna waya Hauwa na goye da Mu'ayyad tana mopping da yake Get din a bude yake ta aiki Aliyu bata so ya dawo yayi ta bugawa shiyasa sun zuwa suka shige se ganinsu tayi tsulum akanta.
Ashariya me maiqo Naziyya ta fara aika mata da ita sanda taga Hauwa ta fito daga dakin Khalil da bokitin mopping kafin taci gaba da cewa
"Babu shakka Umaimah kin shahara, kina zaune babu aikin fari balle na baqi wata zangamemiyar budurwa ce zata shiga ta gyara miki inda Mijinki yake kwanciya taga sirrin sa ko? To zakici ubanki, notikan kanki da suka kwance yau munzo da spanun da zamu daure miki su tamau"
Seta juya kan Hauwa da tayi tsamo tsamo tace
"Ke kuma a gidan nan kike ko kuwa?"
Da sauri Hauwa tace
"Aa zuwa nakeyi"
"Kwanto shi ki fita ki bamu guri" Naziyyan ta sake fada fuska babu wasa jiki ba rawa ta kwance yaron Maman Asad data fi kusa da ita ta karbeshi daman da Hijabin ta a wuya ta fice da sauri Umaimah dai tunda ta sunkuyar da kai bata dago ba tasan yau kan kashinta ya bushe a gurin Naziyya cinyeta ne kadai ba zata yi ba.