← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 267

Sashe 231

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaskiya Mama ta fada a duk lokacin da taji wani al'amari me nauyi ya taso mata a zuciya a maimakon ta miqa komai ga Allah seta zabi tayi ta zunduma ihu irin yanda take karantawa a littattafan turawa da gani a finafinan su idan abu ya samesu sukayi irin wannan ihun me qarfi kamar yana tafiya ne da dukkan damuwarsu ta dauki hakan kuma ta gwada taga yayi mata tun daga nan ta mayar dashi dabi'a da wata damuwa ta sameta zata taqarqare tayi ta zunduma ihu har ada suke tunanin tana da shafar Jinnu bata mantawa kullum Maman cikin nuna mata falalar addu'a takeyi amma ta gagara riqewa, ko Malamin da aka taba kaita ruqiyya gurinsa seda ya jaddada mata yin addu'a a duk sanda zuciya ta bijiro mata da abinda yake harqitsa mata tunani.

Haka a islamiyya Ya sayyadin su kullum seya karanta musu falalar Hasbunallahu da sauran lazumai da suke sanya nutsuwar zuciya kuma idan yanayi yawanci ita yake kallo alamar in directly da ita yake dan ita ce majanuniyar ajin tayi shura kaf makara tar babu Wanda besan Tijararta ba, Headmaster idan aka fita sallar la'asar takanas yake sakawa a kirata bayan yayi alwala ya bata butar yace tasha ragowar ruwan ciki akan wannan abun har dena zuwa Islamiyyar tayi wai ya raina mata hankali yana sakata shan ruwan buta idan suka tafi gaba daya se ta zame tayi wani wajen tayi zamantahar se an tashi sannan zata biyosu su dawo gida seda Mama taci Ubanta bayan da su Nuratu suka ce basa ganinta idan anfito sallah tunda kowa ajinsa daban se an tashi suke haduwa a get sannan fa ta nutsu ta koma zuwa Islamiyyar amma bata yarda ta sake shan ragowar ruwan Alwalar Uztaz Muslim ba.

Ta muskuta ta gyara kwanciyarta ta sake fadawa kogin tunani, ita da kanta ta yarda da cewar rayuwarta akwai dazgado a cikinta. Tana salloli biyar na farilla tana Azumin Ramadana baya ga haka babu wata Ibadah ta neman lada da takeyi ta bari sharholiyar duniya da abinda yake cikinta yayi tasiri a zuciyarta. Idan da ace mutum yana haifar Da ya haifi halinsa tabbas data kasance daga cikin mutane masu kyawawan dabi'u da ake misali dasu domin ba fariya ba Mahaifiyarta maceceta gari me matuqar kirki da riqo da Addini kuma tayi iyakar qoqarinta gurin basu tarbiyya kuma duk cikinsu kowanne yana kamantawa daidai misali banda ita data fita zakkah. Ta tashi a gidansu taga Mahaifiyarta ta kasance me yawan ibadah tasha ji a bakin Abba yana fada yana nanatawa Maman ita ta koya masa tsayuwar dare da Azumin litinin da Alhamis kuma tunda ya kamasu yake ganin haske a Kasuwancinsa da rayuwarsa gaba daya shiyasa a kullum yake qara godewa ubangiji akan hadin da yayi musu domin Malika ta zama haske a rayuwarsa. Tun suna qanana sanda suke kwana a dakinta tasan tana tashi kullum dare tayi sallah koda raka'a biyu ce haka nan koda ace tana fashin sallah wannan abin ya zame mata jiki seta tashi tayi addu'a tayi musu idan suna bacci haka zata shiga dakinsu ta tsaya akansu ta ringa tofa musu addu'oi yawanci tanayin hakan akan idonta saboda bata da nauyin bacci koya akayi motsi seta farka amma bata mori wannan baiwa da Allah yayi mata ba gurin ringa tashi tana bauta masa cikin dare sanda sauran jama'a suke bacci tana kallo su Nuratu zasu tashi subi Maman suyi sallar koda ba kullum sukeyi ba amma banda ita tun suna ganin yarintarta su barta har ya zamana suna tashinta wani lokacin tayi wani lokacin ta tsaya daga bayansu suna sallah tayi kwanciyarta bawai sallar dare ba har lokutan Azumi idan anje Tarawi haka takeyi tasha baccinta ta dawo gida ayi fadan a daka duk a banza har suka haqura suka zubamata ido randa Allah yaci da ita tanada rabon samun ladan tayi randabata dashi taqiyia haka ta tashi ta girma ta auri Khalil ta same shi shima me tsayuwar darene a farko farko tana binsa suyi daga baya ta saki tana kallo ze tashi yayi sallolinsa ita ko ta shanya baki tana bacci wani lokacinma idonta biyu sedai ta dauki waya tayi ta danne dannenda bazasu amfaneta da komai ba idan ya matsa mata tace da wanne zata ji gajiyar daya tara mata ko kuwa ya barta tayi baccinta tunda ba farilla ta tsallake ba bare yace ta sabawa Allah seya rabu da ita kawai taci gaba da rayuwarta a yanda ta zabar ma kanta babu Allah a ciki waddaga sakamakonta ta fara girba tun BA's ko ina ba duniyar ta nuna mata cewa ita ba koman kowa bace ba a dan qaramin lokaci ta zama abar tausayi.
Daren ranar kwana tayi cikin jimami da tunanin neman mafita da hanyar da zata bi ta gyara kura kurenta, tana da buqatar wanda ze saurareta ya kuma nuna mata hanya domin kwakwalwarta ta rufe ruf bata tunanin gaba baya kawai take hasko mata tana tariyo irin mugayen abubuwan data aikata a rayuwarta da tun a nan duniya sun fara farautarta sun hana mata nutsuwa.

KHALIL
Kallon qofar gidan ya ringayi abubuwa da yawa suna bijiro masa tun daga farkon fara zuwansa gidan har kawo yau din nan dayazo daukar yaran. Jiya suka hadu da Abba a wajen wani daurin aure, ba qaramin kunyarsa yaji ba harya kasa hada ido dashi shi kuwa Abban ko a jikinsa suka gaisa ya tambayeshi iyali har yake ce masa
"Malam Khalil mun tuba kar laifin Umaimah ya shafe mu a taimaka a ringa kawo mana yara muna ganinsu ko da a wuni ne, kaga Amaren nan nawa biyu ba qaramar kewarsu nake yi ba a dubamun na dan samu na gansu ko naji sanyi a raina" Abban ya fada cikin raha abinda ya sake jefa Khalil cikin matsananciyar kunya kenan dan haka da yamma yana komawa gida yace musu washe gari da sun taso daga Boko zasuje unguwa dama kuma Alhamis ce babu islamiyya ya sanarwa da Sabon Driver daya daukar musu saboda makaranta da sun taso ya jira su shirya ze kaisu wani guri. Seda sukaje kwanciya yake gayawa Humairan gobe za'a kaisu gurin Mamansu tayi masa murmushi me kyau tana lafe a qirjinsa tace

"Ko kaifa Habibi amma ace tsahon lokaci ka raba yara da mahaifiyarsu Alhalin tana raye kasan kuwa zafin rashin uwa?"
"Shiiii" ya dakatar da ita ganin tana so ta tado da wani abu kuma kafin yaci gana da cewa
"Basu rasa uwa ba tunda suna dake kuma ai gashi nace gobe zasuje wajenta shikenan se ki dena yi mun mita"
"Toh kwana nawa zasuyi? Kaga daman gobe da Monday babu makaranta se su zauna kawai zuwa Sunday se a dakko su ko ba haka ba?" Ta sake fada seya zuba mata ido kawai ba tareda yace komai ba.

A tsahon shekara ukun nan babu abinda ta rageshi dashi da yaransa, ta karbesu da hidimarsu gaba daya a hannunta take tamkar yadda uwa zata tarbiyyantar da yaranta haka take musu babu mugunta bare qyashi ko hassada ya gamsu da cewar tsakani da Allah take riqe masa yara amma dukda hakan a kullum cikin haqurtar dashi take akan ya bari su ringa zuwa gurin Mahaifiyarsu ko Yayane.
"Ita kadai ce Alfarmar da zaka mata idan ka rabata da yaranta baka san irin taskun da zata shiga ba Yah Khalil ka ture komai kayi mata wannan Alfamar ko ba dan ita ba saboda su kansu yaran nasan duk yanda zan kula dasu tunda har sunsan mahaifiyarsu tana raye dole zasuyi qulafucinta kaga kullum cikin tambayar ina take suke ina tsoron su qara girma suyi wayo su zargeni da laifin raba su da ita Alhalin tana raye" abinda kullum take nanata masa kenan shi kuma hujjar daya riqe itace Umaiman bata damu da yaran ba tunda har ta iya dawo Masa da Iman kamar yanda ta fada sannan ko a waya tun bayan rabuwarsu bata sake waiwayarsa ba wannan abun yana masa ciwo ya kuma tabbatar da Gaske ta dena sonsa koya mutu koya rayu a gurinta dayane ballan tana ta nemi yaranta yan uwanta da suke son ganinsu ai suna zuwa su gansu in ta damu dasu itama ai zata neme sun ko yanzu kunyar idon Abba da har ya karya bille ya roqi akai su tasa ya yarda kuma ba kwana zasuyi ba, suje su wuni su dawo baze sake barwa Umaimah dansa ko daya ya kwana a gurinta ba. Washe garin kuwa yasa akakaisu, Magriba nayi yace tashirya zasuje dakko su dan baya so ma ya tura wani balle har a hanashi daukarsu yana dawowa daga Masallaci kuwa suka kama hanya Humairan nata mitar se kace za'a gutsiresu ai se su Mama suga rashin kyautawarsa ma sama da shekara biyu rabon da yaran su taka qafarsu a gidan kuma suje yanzu ko cikakkun Awa shida basuyi ba ace zasu tafi ai babu dadi.

"Aisha, idan kin fara gajiyawa da Hidimar yaran nan ki gayamun kai tsaye, zanyi miki uzuri domin nasan daman nauyin yayi miki yawa kuma ke kika dage zakiyi dan haka babu laifi yanzu idan kin gaza zan qaro musu me aiki taci gaba da kamawa Ruqayya kulawa dasu" ya fada mata fuskarsa babu alamun danuwa ko bacin rai seta kasa ce masa komai danda tasan tunanin da zeyi kenan da bata saka bakinta a maganar ya kaiwa Umaimah yaranta ba. Akan me ma ze kawo wannan tunanin a zuciyarsa ya za'ayi ta gajiya da hidimar Yayansa bayan ko a zuciyarta bata taba banbantasu da Aryaan data haifa ba kallon abu daya take musu kamar yanda suma suka mata kallon Uwa ba matar uba ba. Yanda tayi kinini da fuska bacin ran abinda ya gaya matan ya bayyana har akan fuskarta ya saka shi gangarawa bakin hanya yayi parking ya kama hannunta cikin nasa ta fizge seya janyo ta jikinsa gaba daya ta kuwa fasa masa kuka Aryaan dake baya yana wasansa ya saki da sauri ya matso jin Mamansa tana kuka
Chapter 231 · 0% Book details