← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 267

Sashe 116

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 47

KHALIL
Tun daga Nesa ya hango Hadizan tsaye da wani da be tabbatar da waye ba dan ya bashi baya. Ya samu guri ya ajiye motarsa daga dan nesa dasu kafin ya tako a qafa seda ya isa kusa dasu ya gane Musa Kallah ne. A mutunce suka sake gaisawa yana kallonsa yace
"Wato Khalil ka godewa Hadiza, badan tace ta yafe ba ina me tabbatar maka se mun daure matarka daurin da ze saka tayi hankali" se Khalil ya gimtse fuska yace

"Ban fahimta ba, da aka ce muku bata da hankaline ko yaya?"
"Idan ma tana dashi toh be kai yawan wanda ya kamata matured mutum irinta ya mallaka ba, any way Allah ya taimaketa dan da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba" Musa Kallah ya sake fada kafin ya juya kan Hadiza yace

"Kin daiji abinda na gaya miki, ki samu ki huta sosai ki kuma cire duk wata damuwa daga zuciyarki, if you need someone to talk to I'm always available for you and karki manta think about what we discussed ki kuma bani amsa da wurwuri dan bana son jira".

Kanta na qasa ta amsa masa da cewa
"In sha Allah Sir, na kuma gode kwarai Allah ya saka da alkhairi akan qoqarin da kayi mun na gode banida abinda zan saka maka dashi sedai naci gaba dayi maka addu'a Allah ya tsare gabanka da bayanka"

"Amin, amma kece kike da abida zaki biyani dashi kuwa Hadiza sedai idan kuma kai tsaye kina so kice nayi miki tsufa ne se na tattara na koma gurin tsohuwar Matata mu qarasa, bari naje, i have somethings to attended in the office se munyi magana kinji" Musa Kallah ya sake fada yana yar dariya kafin ya juya ya kalli Khalil daya cika yayi tam ya masa wani dan murmushi ya juya inda Driver sa yake jiransa.

Shiru yayi yana kallonta bayan da Musa Kallah ya bar gurin, har wani sama da qasa yaji numfashinsa yana yi masa saboda bacin rai kamar yabi shi ya shaqo wuyansa ya lallasa shi nan shi gani yakeyi ya zama wani Hero a gurinta ko? Kawai saboda yayi shishshigi daya barshi ai shi zeyi handling komai amma ya kwaso wasu qafafunsa kowa ya gayyatoshi ma oho.

"Na gaji da yawa Khalil, ko zaka bari idan ka shirya seka dawo dan naga yanzu kamar baka zo don muyi maganaba" Hadiza ta fada ba tareda ta kalleshi ba se ya sassauta fuskarsa yana qoqarin danne bacin ransa yace
"Amm nasan ba yanzu ne lokacin da ya kamata nazo ba amma na kasa samun nutsuwa ne Hadiza har yanzu ina kallon kaina a matsayin me laifi a gurinki. Nine silar duk abinda ya faru dake nina jawo miki dan Alllah...."

"Na gaya maka ka dena zargin kanka, kuma ko ba wannan ba su kansu wanda suka aikata mun laifin na yafe musu nace me yasa zaka ci gaba da damun kanka idan kuma wannan ne ya kawoka shima babh wata damuwa, zan iya shiga ciki?" Ta fada tana kallon cikin idonsa. Seya kasa ce mata komai, dukda bada fushi ko hayaniya tayi maganarta ba amma shi ya fahimci jin zafinsa a kalamanta.

Ganin bashi da niyyar sake cewa komai yasa ta fara tafiya yayi saurin dakatar da ita da cewa.
"Hadiza, ina roqon da ki bani dama ta biyu. Kuma a wannan karon da gaske nake yi idan kin Amince daganna zuwa qarshen satin nan a daura mana aure mu koma SA tare nasan a yanzu kina da buqatar kiyi nesa na dan wani lokaci kodan saboda nutsuwarki ta dawo".
Tsayawa tayi cak na kusan minti biyu kafin ta waiwayo fuskarta dauke da wani murmushi tace

" Thank you Khalil, idan da rabo wata rana ko a hanya zamu hadu mu gaisa amma daga yanzu bana buqatar ka sake takowa inda nake, ka dauka qaddara ce haduwarmu wadda ta rigada ta afku, ina kuma so kayi qoqarin manta wanzuwata a duniyarka gaba daya kamar yanda na dade da gogeka a tawa duniyar, ina yi maka fatan Alkhairi ina kuma yi maka fatan idan kana da Rabo Allah ya baka macen da zata kula da kai saboda kai mutumin kirki ne.
Tsakanin da akayi mana a Station bada matarka ne kadai ba harda kai, idan kuma kaci gaba da bibiyata" ta saki wani murmushi ta juya tana cewa
"Na barka lafiya".

Yanda kasan hoto haka ta barshi a gurin seda ya dena hangota gaba daya kafin ya iya jan qafafunsa yabar qofar gidan daman yasan da wahala, ba ita ba baya tunanin akwai macen da zata yarda ta rabe shi idan har tasan labarin ta'asar matar sa.

Kwana uku ya qara ya koma SA a lokacin an sallamo Umaimah daga Asibiti kuma har sannan magana bata shiga tsakaninsu ba. Sau daya yaje ya dubata a Asibitin se randa ze tafi daya koma shima bisa takurawar Hajiyarsa. Haushinta yakeji matuqa, dukda yanda ta koma kalar tausayi seka rantse daga sannan Ta shiryu amma shi ya tabbatar da na dan lokaci ne, idan har Umaiman daya sani ce ana nan saboda hali aka ce zanen dutse. Haka ya tattara ya koma yaci gaba da abinda yake a gabansa gaba daya ya watsar da wata Umaimah koda yake ai ita ya kamata ace ta nemeshi ta bashi haquri akan abinda ya faru kafin ya duba ya gani idan da yuwuwar katbar tuban nata.

Yanzu kammaluwar ginin gidansa daya dauko ne a gabansa, an kammala bangaren Hajiya har suna shirye shirye komawa ciki sannan a rushe daya bangaren dayake nasa danhar an shigo da qarin filin daya siya ciki. Da yaso ya dakatar da aikin zuwa wani lokaci amma a yanzu yana jin kawai ze ci gaba, idan har ya samu yanda yake so baze rufe shekarar nan ba tareda ya qara aure ba danya gaji da bala'in Umaimah, nema takeyi ta dora masa ciwon da bashi dasu.

UMAIMAH
Takunkumi Mama da Abba suka saka mata dan daman wayarta tunda Yaya Aminu ya karba ba'a maida mata ba a cewar Abba ma ta gama riqe waya tunda da ita take jaye jayen bala'i fada kuwa ta shashi da nasiha har seda taji ta tsani kanta ta tsani halinta. Babban abinda ya qara damunta yanda ta kasa samun fuska a gurin Khalil. Sau saya ya dubata a Asibiti se ranar da ze koma SA da safe Ya sake komawa shima bisa tursaswar Hajiya, da zuwansa kuma da tafiyarsa beyi minti goma ba. Magana daya ta shiga tsakaninsu ya sake maimaita mata duk abinda take da buqata ta nemi Khalifa Already daman ya biya kudin Antinatal dana haihuwa lokaci kawai ake jira sannan ya saka mata wasu kudi matsayin na siyayyar haihuwa.

Cikin kukan daya zo mata ta tsaya gabansa tana cewa "Dangirman Allah Khalil kayi haquri, wallahi....." Gani tayi ya juya ya fice daga dakin abinda ya hanata qarasa magiyar data debo kenan. Tana jiyo yanda su Anty suke masa fatan sauka lafiya da nasara akan abinda ya tafiyi yayi musu sallama ya fice daga gidan nan ta zube taci gaba da rusa kuka baji ba gani. A zatonta ai komai ya wuce tunda me afkuwa ta afku akan me ze dauki fushi da ita bayan duk ma abinda ta aikata sanadiyyar son da take masa ne da kishinsa ya janyo. Haka taci gaba da zama a gidan cikin takura da qunci, ga rashin waya ballantana ta samu ta kira Khalil din ta rarrashe shi, sau saya ta saci ta Anty ta kirashitunda yaji muryarta daga ranar kota kira baya dagawa, qarshema dena shiga tayi qilan ya tosheta ne.

A cikin haka wata rana Maman Asad tazo gidan, Umaimah na daki ta shiga ta sameta. Cikin tausayawa ta kalleta dan cikinta da ya ke wata tara yanzu harta haura EDD na daya dana biyu gaba daya ta fita hayyacinta baqiqqirin ga uwar rama saboda damuwar data saka a ra ta ta rashin magana da Khalil. Zama tayi a gefe ta kalleta tace
"Sannu Umaimah, se kizo daki ke kadai ko zauna kina faman tunani bakya ko tsoron wani ciwon ya kamaki ga tsohon ciki? Yanzu daman Anty take gaya mun abinci ma ba ci kikeyi ba, wani sa ilin yanda aka ajiye haka ake zuwa a dauka baki taba shi ba anya hakan da kika daukarwa kanki mafita ce?"

Kamar daman tana jira ta fashe mata da kuka tana cewa
"Toh daman waya damu ko jiyo ya kamani na mutu nayi rai duk damuqata ce ba taku ba ina ku kuna rayuwarku cikin walwala da farin ciki? Daga Abban har Mama babu wanda yake hade muku fuska koya hantare ku se nice ba'a tausayi ko duba halin da nake ciki ba'ayi ake mun abinda aka ga dama"
Chapter 116 · 0% Book details