← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 267

Sashe 48

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya yaci gaba dayi yana cewa
"Idan izinina kike tambaya banyarda ba idan kuma kinga zaki yi gaban kanki ne to ki tabbata idan kika tafi bazan biyo bayanki ba" ya kunna motarsa kafin ya qarasa ya bude get ya fita da motar ya dawo ya rufe har sannan tana tsaye tana hawaye.

Yana fita ta juya dakinta da gudu tana kuka, kaya ta shiga hadawa dan ita tafiya zatayi da gaske bazata zauna ba gara can a kirashi ya fadi abinda yake nufi da ita daya jingineta ita da babu a gidan matsayinsu daya.

Khalil kuwa yana fita gefen hanya ya samu ya faka motarsa ya dora kansa akan sitiyari, Allah ya sani yana son Umaimah son da shi kansa besan iyakarsa ko a yanzu daya nesanta kansa da ita shi kadai yasan irin azabar kewarta da yakeyi.
Dakyar yake iya bacci, ya tabbata ya fita shan wahalar wannan yanayin da suke ciki amma so yakeyi su dawo kan saiti suyi rayuwar aure kamar sauran ma'aurata cikin girmamawa da mutunta juna.

Baze dauki salon data zo dashi ba na zama kamar wasu haduwar bariki ya zaman bata shayin ta zageshi kota gaya masa duk maganar data zo mata amma yaga alamar sam bata da niyyar gyarawa sema qara batawa da take so tayi, ba kuma yaso ace har ta kaisu gaban magabatansu yanaso su koyi sasanta duk wani sabani daya gifta a tsakanin mu to yaya zeyi? Ya tabbatar yanzu tunda ta quduri niyyar tafiya koda yace be yarda ba sedau wani ikon Allahn amma mawuyaci ne ya koma gidan ya tarar da ita

Ji yakeyi kamar ya koma ya sauke nasa fushin ya lallabata amma yana tsoron abinda hakan ze haifar masa a gaba idan ta miqe akan sedai shi yabi ta ze sha wahala dan ba ita kadai ba hatta da yayan da zasu haifa a gaba se hakan ya shafi tarbiyyarsu, dole ya danne duk wani tasirin da take dashi a zuciyarsa ya kunna mota yaci gaba da tafiya amma ya qudurce idan ya dawo ya tarar da ita zero zaunarda ita ya nuna mata kuskurenta tunda ta kasa fahimta da kanta.

Umaimah kuwa kaya ta shiga hadawa da gaske tana kuka, kiran wayarta da akayi ya dakatar da ita ta daga ganin Anty Hafsa ce take kira ta shaida mata zata zo gidan tana hanya.
Jefa wayar tayi taci gaba da hada kaya gara ma tazo su tafi kawai ta huta da nemo Adaidaita. Tsaf ta cika akwatuna biyu da duk abinda tasan zata buqata ta kaisu palour ta ajiye, a gurguje ta watsa ruwa ta saka doguwar riga bata nemi abin kari bama taci a gida ta zauna a palour zaman jiran Anty Hafsa tana jin an buga Get kuwa ta fita da saurinta ta bude.

"Wadannan akwatunan fa Umaimah ko balaguro zakuyi tunda daman ke ba'a sanin tafiyarku balle dawowa" Anty Hafsan ta fada tana kallon akwatunan data jera, kamar tana jira kuwa ta rushe mata da kuka tana cewa

"Na gaji Anty gida zan tafi Khalil ya deba sona ya rigada ya samu abinda yake so ya hadani da kaya shine ze fara nuna mun halinsu na maza".

"Subhanallahi me ya faru? Dama kina da wata matsala ne da kikayi shiru tuntuni baki fada ba har ta kai ga kice zaki koma gida" Anty Hafsa ta fada cikin tashin hankalin irin kukan da taga Umaiman tanayi.

Dakyar ta tsagaita nan ta shiga labartawa Anty Hafsan abinda ya faru zuwansu Kaduna har zuwa yanda sukayi dashi yau da safen, ta rufe da cewa

"Daga na nuna masa nasan abinda yakeyi naganshi da karuwa shikenan ya dauki gaba dani ya fita sabgata, ina tunanin ma idan ya fita can yawon biye biyensa yake tafiya babu abinda ya shafeshi dani bare yasan damuwata".

"Ba shakka Umaimah duk inda ake neman yar bura uba mahaukaciya kin kai har kin wuce, aini wallahi be burgeni ba dabe dawo mana dake a kakkarye ba. Kamata yayi ace ya sauke miki kafada ya karya miki qafa daya sanda kika ce ya dakko karuwar su kwana tare. Banda ke bakida hankali baki san abinda yake miki ciwo ba ki kalli tsabar idon mijinki ki kirashi mazinaci koda ace da gaske ne ballantana tsabar hauka da baqin kishinki da kika dorawa kanki ne, anya kina tsoron gamuwarki da Allah Umaimah?

Toh bari kiji tun kinada sauran lokaci ko tuba kibi Allah ki kuma nemi yafiyar sa. Islamiyyar da kikayi bata amfane ki da komai ba tunda baki koyo ilimin sanin darajar miji da yanda ake zaman aure ba, idan kuma baki tuba kinbi Allah ba zaki tashi a tutar babu, ki qare rayuwa bakiji dadin zaman aure ba dan babu dan iskan da ze zauna dake kina zaginsa yanda kika ga dama idan be ringa cin ubanki ba to kuwa zakiyi rayuwar qunci da baqin ciki kamar yanda kikeyi yanzu sannan kije lahira walakiri yaci ubanki ki tafi wuta ba fata nake miki ba.

Allah ya taimakeki ya baki miji me sonki da yake ke ba yar arziqi bace ashe abin tsiyar da kike shuka masa kenan yana shanyewa ina ma ace banzo ba ki debi kayan nan kije gidan na tabbata dayau se anyi miki dakan hatsin matan qauye yanzun ma kuma daga nan gidan zani na zayyanewa Mama duk abinda ake ciki gara ta sani a san ta inda za'a taroki danna fuskanci baki da hankali ko kadan".

Tas ta silleta tayi fada tayi masifa kafin ta dora da nasiha da lallashida bata dabarun yanda zata riqe mijinta bata hanyar hauka ko rashin hankalin data daukarwa kanta ba.

Da kanta ta tayata suka gyara gidan tsaf dan shara tunda aka shiga wannan hali idan bata gaji da zaman tunani ba bi ba batayi, cikin kayayyakin gyaranta ta harhada mata wasu tasha tana cewa
"Dan uban likitan da tace ki kwashi wata biyun idan ta kashe miki aure mijinta zata baki ki aura ko ke kuma ga sauna da yace ki koma dakinki kika kwashi kaya ziqau ziqau kika tafi Allah ya ganar dake dai Umaimah.

Seda tayi mata lafiyayyen girki bayan data sakata tayi wanka ta sheqa kwalliya suka shirya komai tsaf sannan tace mata

"Ki dauki waya ki kirashi yanzu kisan yanda zakiyi duk abinda yakeyi ya baro ya taho gidan nan, idan yazo saura ki sauka daga layin dana doraki, ki sauke kanki ki bashi haquri ki nuna masa kin gane kuskurenki ba zaki sake maimaitawa ba ba kuma wai ya zama iya fatar baki ba Aa har zuciyarki nake so ki yarda kinyi kuskure kuma kodan gaba ki kiyaye, ki sani duk abinda kika aikata masa na rashin kirki kanki kikayiwa saboda shi Allah babu ruwansa ze kamaki da laifin qin yiwa miji biyayya. Gara ace shi ya cuceki se Allah ya saka miki da ace ke ce kika cuce shi kikai kanki wuta a banza, kuma idan na koma zanyo miki aiken ingantattun magunguna dana samo a gurin *SUMAYYA'S HERBAL APHRODISIACS AND COLLECTION*, idan kika gwada magungunanta babu ke babu sake siyan duk wasu jigari jigarin magungunan mata da baki san dame aka hada su ba.

Jikin Umaimah yayi laqwas, Anty Hafsa bata tafi ba seda ta kirashi a wayar tana numfashi kamar wadda ake yankawa wai cikinta, Khalil dake Tsakiyar aiki a wani Site babu shiri ya kamo hanya dan daman gaba dayan ranar tana maqale a ransa yana ta tunanin ta tafin ko tana nan.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 23

Cikin yan mintuna ya isa gidan a ransa yana ta taraddadin abinda zeje ya tarar, meya sameta? Shine tambayar da yake tayiwa kansa har ya qarasa qofar gidan ya kashe motar ya barta a waje tunda sake fita zasuyi ya kaita Asibiti.

Turus yayi yana qarewa yar madaidaiciyar harabar gidan kallo, ko ina yayi qal hatta da interlocks din dake shimfid sunsha wanki da kallo daya zaka musu ka hango tas din da sukayi. Qara bude hanci yayi yana shaqar daddadan turaren wuta dana Airfreshner ga kuma sanyayyar iskar yamma se suka hadu suka bada wata Atmosphere me sanyi da sanyaya zuciya.

Be qarasa suman tsaye ba seda ya shiga palour, tana zaune akan kujerar dake fuskantar qofar shigowa. Riga da skirt ne na wani Yellow Lace irin yellow nan me kamar butter da yayi bala'in karbar fatarta da bata da haske sosai ta kashe daurin gaban goshi irin yanda yake sonsa wani kallo ta watsa masa tana raurau da ido kamar me shirin yin kuka be san sanda ya dage zuciyarsa da hannu biyu ba ya lumshe ido saboda yanda kallon nata ya tasirance shi.

Cikin wata irin tafiya taso babu inda baya motsawa a jikinta tana zuwa ta fada jikin Khalil daya zama mara amfani na wani lokaci ta sakar masa kukan zallar shagwaba da kissa.
Fitinannan Qamshin ta ya kai masa ziyara, qafafunsa sunyi sanyin da bazasu iya daukarsu ba se yayi saurin dafe bango da hannu daya ya riqeta gam a jikinsa da daya hannun ya gagara ce mata komai se ajiyar zuciya yake saki kamar Jaririn daya kwana besha Nono ba.

Qasa ta tafi zata tsugunna ya yi yunqurin tarota ta zame seda ta ajiye guiwoyinta a qasa ta dafa nasa da hannu biyu hawaye na bin fuskarta tace
"Bazan iya cigaba da jure fushinka ba Khalil na tuba ka yafe min, nayi nadamar duk abinda na aikata maka a kuma shirye nake da karbar duk wani hukunci daga gareka amma banda na qaurace mun, Allah kadai yasan irin quncin dana shiga na rashinka. Muna rayuwa guri daya amma ka nesanta kanka dani baka san yanda nakeji ba

Kuma Wallahi duk abinda ya faru sharrin shaidan ne yayi amfani da tarin sonka da kishinka da nakeyi ya makantar dani amma yanzu na fita daga cikin duhu na dawo haske, in sha Allahu bazan sake kwatanta makamancin abinda ya faru ba bazan sake ba, ka yafe mun kaji Ibbahna, mu koma rayuwar mu irin tada me cike da qauna da Aminci".
Chapter 48 · 0% Book details