← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 267

Sashe 137

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali da kanta kuma se gashi ta fara sakkowa tana kulashi, tun yana dari dari har ya fahimci dagske ta sauka daga fushin nata ya saki jiki suka koma sabgoginsu kamar da, yanda bata daga maganar Zahra ba shima beyi mata ba ya kuma qara toshe duk wata kafa da zata bata damar fahimtar wani abu dan wani sa'in ma daya dawo yake kashe layinsa da Zahran ta sank dan tunda ta fahimci bata samunsa idan ya koma gida ta chanza lamba, randa ta kira ya shiga kuwa yasha mitar Bala'i akan me yake blocking dinta yace saboda baya so ta kira a gaban matarsa, ta kuwa samu nayi har Dadynta seda ya shiga maganar yayi masa tatas yana kuma sake jaddada masa yabi a sannu dole ya chanza taku a haka dai ake ta lallabawa.

UMAIMAH
Kallonsa kawai takeyi da yanda yake raina mata hankali yana daukar bata san abinda yakeyi ba amma ta zabi tayi shiru kamar yanda suka sake shawartawa da Safina tace ya nuna masa komai ba komai na ta shammace shi hakan kuwa akayi, dukda ya chanza password abinda ya qara baqanta mata rai zarginta ya tabbata akansa kenan amma seda tasan ta yanda ta gano sabon daya saka.

Ranakun Lahadi yana gida throughout be fiya fita ba seda kwakwkwaran dalili. Da rana suna yin lunch ita dashi, Bibi sun tafi gidan Jamila da Habiba kusan satinsu daya tunda Habiban ta samu Hutu Mu'ayyad yana islamiyya. Abinci sukeci suna yar hira jefi jefi wayarsa dake ajiye tayi qara yanda ya zabura seda ta zura masa ido kawai tana kallonsa ganin haka ya sakashi daidaita nutsuwarsa ya dauki wayar cikin borin kunya yake cewa
"Namanta shaf na qaro qarar wayar dazu yayi yawa har na firgita"
"Uhm" ta iya ce masa kafin ta mayar da kai taci gaba da tura abincin da gaba daya ya fita a ranta.

Be amsa kiran ba seda wani ya sake shigowa shima gudun zargi ya sakashi amsawa a gaggauce yace
"Abinci nake ci idan na gama zan kiraku please" bata san me aka ce masa ba daga can bangaren ya sake cewa
"Toh, naji" kafin ya kashe yana jan tsaki yace
"Anwar ne, haka kawai wai sun shirya mana walima akan kwangilar dana baki labari bayan ko gama kammaluwa batayi ba. Bayanda banyi dashi ba akan ya bari ba yanzu ba amma wai ya rigada ya sanarda duka Employees dinmu yau za'ayi qarfe hudu nidan bazanje ba se suyi abinsu su kadai"

"Aiko dai da kaje" ta fada tana kallonsa, yanda yayi maganar da bata san abinda yake shiryawa ba tsaf zata yarda amma ina ta gama rafko shi babu ta yanda ze layance mata.

"Gaskiya bazanje ba tunda yaqi jin maganata ya bari ba yanzu ba se suyi su kadai, ni yanzu ma so nakeyi mu shiga daga ciki na gaya miki wani abu" ya fada yana zagayowa ta bayanta yayi kissing wuyanta. Janye jikinta tayi ta miqe tana cewa
"Gara dai kai tafi dan ni nan me kitso nake jira kaina ya dameni gara tazo ta lallabe mun shi" ta qarasa tana tattare kwanukan da suka bata. Shiya tayata suka kwashe komai suka kai kitchen kafin suka fito ta wuce dakinta shima ya tafi nasa dan shiryawa ransa qal da ya samu damar fita ba tareda ta zargi wani abu ba.

Zahra ce ta addabeshi, tun farkon satin nan take gaya masa qawayenta zasu zo yau daga kuma tana so ya hadu dasu su gaisa dan duk ta basu labarinsa. Baya son su samu wata matsala a ritsin shiyasa ya amince yana ta lalubo abinda ze fitar dashi daga gidan ita kuma gata da shegen gajen haquri se kiransa take tana tambayar yaushe ze zo. Wanka ya shiga, Umaimah data biyo bayansa ta labe seda ta tabbatar ya shiga wankan kafin ta dauki wayarsa a gaggauce ta kwafi number Zahran daya chanzawa suna zuwa Engineer Z tsabar sa idonta yasa ta gano shi, har ta mayar da wayar saqo ya shigo daga Zahra. Budewa tayi ta karanta
"Dear kazo da wuri saboda su ganka a cikin hasken rana suga irin zaben mijin da nayi, Love you" abinda ta rubuta kenan. Goge saqon Umaimah tayi zuciya tazo mata wuya, a hasale ta qarasa jikin qofar bandakin cikin rashin Sa'a muqullin qofar ta ciki aka sakashi dan da so tayi ta kulle shi a ciki taga ta inda ze fita se kuma meta tuna ta fice daga dakin da sauri zuwa nata.

Khalil daya jiyo qarar rufe qofa cikin Sauri ya dauraye jikinsa ya fito ko gama daura towel din dakyau beyi ba ya tsaya yana dube dube bega kowa ba, ya qarasa inda wayarsa take ya duba tana nan yanda ya ajie dan haka yayi tunanin kunnensa ne yajiyo masa badaidai ba saboda ba a nutse yake ba.
Wankan yakoma ya qarasa. A gurguje ya shirya cikin Wani baqin Wandon Jeans da Farar Long sleeve shirt da aka rubuta 'I'm all yours' a jiki saboda garin akwai sanyi sanyi anyi ruwa da safe.

Tsaf ya feshe jikinsa da turarukansa masu qamshin gaske, ya gyara gashin kansa da Gemu shida kansa yasan yayi kyau ya fito kamar wani qaramin saurayi ba zaka ganshi kace yana da shekaru Talatin da takwas a duniya ba. Yana cikin daura Agogo Umaimah ta shigo dakin da sallama ya kalleta ganinta cikin shirin fita Ta saka Baqar Abaya tayi rolling da mayafinta ga qaramar Jaka da waya a hannunta. Kallonta yake harta qaraso gabansa yace
"Kinyi kyau, se ina haka kuma?"

Umaimah da wani hadarin kishi ke haduwa a zuciyarta tayi qarfin halin cewa
"Kaima kayi kyau, amma dai babu mata a gurin da zakaje ko?"
"No haba dai kema kinsani ai, iya mune babu mata kuma badan kin matsa bama ba zanje ba ni" ya fada yana janyota jikinsa ya rungumeta ta bata saboda cikin jikinta.

"Zakaci abu ta kazan ubanka ne" Umaimah ta raya a ranta tana kallo ya daga wayarsa yayi musu hoto yana ta doka uban murmushi ita dai fuska babu yabo babu fallasa ta kalle shi tace
"Na kira me kitson wai ba zata samu zuwa ba ko zaka saukeni a Salon idan yaso in kun gama se ka biyo ka daukeni"
"Ok, babu damuwa muje yama fi sauqi dan ni daman banaso ayi kitso a gida duk gashi ya bata ko ina kayi ta tsintarshi a abinci" ya bata amsa yana yin gaba ta bishi a baya.
Dakinta ta koma ta dakko Jakar data zuba kayan kitson, a palour qasa ta tarar dashi yana waya yana hangota ya kashe ya qarasa inda take ya riqe mata hannu Umaimah dai murmushi kawai tayi masa ita kadai tasan me take shiryawa a ranta. Seda suka shiga bangaren Hajiya suka gaidata, basu jima ba suka kama hanya suna tafe yana mata hira ita dai amsa biyu take bashi Eh ko Aa dan gaba daya hankalinta yayi gaba.

A wani guri da bata san me akeyi ba ya tsaya yace mata minti biyu yana zuwa, wayarta tayi saurin dauka bayan ya fita ta shiga kiran Harun, wani yaro ne dan unguwarsu yana jan Adaidaita Sahu yawanci idan zata fita bada mota ba shi take kira ya kaita ko ya dakkota daga inda zataje. A taqaice tace zata turo masa da Address yanzun, idan yana kusa da gurin kuma ze iya qarasawa a wasa da minti goma yayi mata Reply kawai karya kirata. Address din Salon din da zataje ta tura masa, yana gani yace mata ai yana ma kusa da gurin yanzu ya ajiye customer ya tafi se tayi saurin kiransa tace ya koma ya jirata gata nan zuwa daidai sannan Khalil ya dawo motar ya bude Sit din baya ya ajiye babbar Ledar daya taho da ita ya shiga mazaunin sa ya dora mata wata qarama a jiki yana cewa
"Anwar matsala ne, wai Icecream zasu sha kamar wasu mata dan Allah, ni banma san gurin nan abinda suke siyarwa ba kenan se yau, bari zamu samu lokaci muzo da su Bibi bakiga ciki ba yayi kyau sosai"

"Allah ya kaimu" kawai ta iya cewa ta sauke ledar daya dora mata a qasa, har suka isa Salon din bata sake magana ba shima ya kama kansa ganin kamar ta fusata kome aka mata oho. Dubu goma ya zaro a Aljihunsa ya bata, ta karba ba tareda tace komai ba dan in ta bude baki tsaf zata rusa shirinta ta bude murfin motar ta fice ba tareda ta dauki ledar Icecream din ba ta shige gurin.

Khalil na tsaye har seda yaga ta shiga an rufe qofar, seda ya qara minti biyar a tsaye haka nan yakeji gabansa na faduwa ya dai daure ya tayar da mota dan yana jin wayarsa dake aljihu se vibrating takeyi yasan kuma Zahra ce take kira.

Yana Juya kan motar Umaimah dake tsaye tuntuni ta fito sanye da dogon Hijabi har qasa ta dora Niqab akai,tsayuwar da yayi ya bata lokaci tayi mata amfani dan ta samu ta shirya duda daman tana shiga ta kira Harun tace ya saka mata ido akan motar Khalil din, idan ma ya tafi ya bishi zasuyi waya duk inda suka nufa zata biyo su. Da sauri ta shige Napep din tace yabi bayansa. A sannu a sannu Harun ke binsa ta yanda baze taba gane cewar wani na biye dashi ba har suka isa unguwar YanKaba ya karya kwanar wani layi data ga an rubuta 'Dr Sabitu Bashir Street' a jikin wani dan Allo take cikakken sunan Zahran data gani a truecaller ya dawo mata.

A farkon Layin tace ya tsaya, ta sauka ta taka da qafa ta shiga a qofar wani katafaren gida ta hango motar Khalil din a ajiye taci gaba da tafiya harta wuce gidan Get din yana kulle dan haka bata ga komi ba ta wuce qarshen layin inda ta hango Hasumiya da alama Masallacine a gurin.
A qofar masallacin ta zauna, mutum biyu ta hango a ciki suna karatu ta zauna shiru gaba daya kwakwalwarta ma ta tsaya cak ta dena aiki. Tunani takeyi ta shiga gidan ne suyi aran gama taji abinda ze gaya mata ko kuwa ta jira ya gama abinda yakeyi ya tafi kafin ta shiga taci uwar yarinyar?
Chapter 137 · 0% Book details