← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 267

Sashe 95

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uhm banji ba nika baccine ya fara kwasata, kuma tsabar iskanci duk gidan nan ki rasa a ina zakiyi wa mutane Amai se a cikin palour na, to ki tashi ki gyara gurin wallahi kafin raina ya baci nayi miki abinda ba zakiji dadi ba" Mama ta fada tana kallon Umaimah dake mayar da numfashi se Anty tayi saurin cewa

"Haba Mama bakiga halin da take ciki bane kiyi haquri kin fa san yanayin Amai idan ya taho ba'a iya tare shi"
"Nata ai na iskanci ne masifarta ce ta janyo shi, wallahi Umamaih kibi duniya a hankali idan ba haka tam" Maman ta sake fada tana juyawa ciki Anty ta bita da kallo gaba daya kanta ya daure da maganar Maman seta juya kan Umaimah dake sabon kuka qasa qasa, 'uhm' ta fada kafin ta kamata ta miqe daga cikin Aman tana cewa
"Ki shiga ki gyara jikinki bari na gyara nan" ta shigar da ita dayan spare dakin Mama ita kuma ta fita dakko paker da tsintsiya.

A cikin daki Mama kasa zama tayi ta juyo ta dawo palour ganin Anty na kwashe amai yasa ta tambayeta tana ina ta nuna mata dakin da take seta ta wuce ciki kaitsaye daidai sanda Umaiman ta fito bayan ta wanke fuskarta.
"Zonan Umaimah" ta fada tana juyawa waje. Dakinta ta koma ta zauna akan gado tana jiranta se gata ta shigo kamar munafuka ta samu can gefe ta rabe kai kace mabaraciya ce.

"Ki dawo nan ki zauna magana zamuyi dake" Maman ta fada tana nuna mata gefenta, seda ta daka mata tsawa sannan ta taso bata zauna kan gadon ba ta zauna a qasa, Mama ta hadiye abinda kw taso mata cikin muryar limana tace
"Ki fadamun meye matsalarki Umaimah"

Cikin rashin fahimta ta kalli Maman, Mama ta sake maimaita mata ta qara da cewa
"Ki fada mun idan akwai wata cutarwa da Khalil yakeyi miki a zaman auranku"

"Babu komai Mama, ni babu wani abu da yakeyi mun" ta bata amsa tana kallon qasa.
"Kin tabbatar babu wani abu a idan da akwai ki gaya mun kinsan dai babu abinda zaki boye mun ko?"

"Wallahi Mama babu abinda yakeyi mun, wani ya ce miki anayi mun wani abun ne?" Ta fada cikin sigar tambaya se Maman ta girgiza kai alamar Aa kafin tace

"Idan babu cutarwa a zaman ku me yasa kike gudun haihuwa dashi, ko yana da wani mugun hali da bamu sani ba da yasa baki so ki hada zuri'a dashi?"

Kamar tace tayi kuka sega hawaye sha sun fara zuba, seta daga mata hannu tace
"Ba kuka nace kiyi mun ki bude baki kiyi mun magana kinji koh"

"Ni Mama babu abinda yake dashi kawai haihuwar ce yanzu bana so. Gaba daya fa shekarar Mu'ayyad daya da wata biyu kuma ance inda ciki har wata uku fa Mama Kwanika fa kenan ni gaskiya bana so se kace wata Matar qauye kawai ina goyo se a ganni da ciki ai se mutane suyi mun dariya ma..." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta ya sakata yin shirun dole hawayenta kuma suka qara qarfi kamar an kunna Famfo.

Nunata Mama tayi da yatsa cikin bacin rai tace
"Ai daman idan bakiyi haka ba baki cika tantiriya mara mutunchi ba, yanzu abin naki har ya zarce kan mu mu ababen halitta kin koma kina fito da mahaliccinki ko, ubanki ne yake raba cikin balle kice saboda sanayya ce tasa ya baki?
Mata nawane suke neman Allah ya azurtasu da haihuwar, zasu iya sadaukar da komai nasu dan su samu abinda suma zasu kira Ya ko dan su amma ke ubangiji ya zabeki cikin Miliyoyi yayi miki baiwa shine kike kiran bakyaso bazaki iya haifarsa ba ko? Toh karki fasa, kiyi duk yanda kika ga dama da cikin idan Ajalinki ne kinga seki janyo shi kusa, a garin salwantar dashi seki salwantar da taki rayuwar ki bishi ku tafi tare.

Kuma idan Ubangiji ya qadarta zuwansa doron qasa ke kinyi kadan ki hana faruwar hakan, kina ji kina gani se ki mutu shi ya rayu shasha sha da baki san ciwon kanki ba. Ba'a haihuwa aka haifeki gashi nan tunda kikazo baki bar mutane sun huta ba kullum da kalar sabon jidalin da zaki tattarowa mutane. Ina jiye miki tsoron duniya Umaimah ki taka a sannu karki ga Allah ya ara miki dama kina yanda kika ga dama lokaci daya idan yaso ze iya canza komai ki dawo abin tausayi dan haka kibi a sannu ki kuma yiwa kanki guzurin Arziqi"

Tunda Maman ta fara magana take kuka kamar ranta ze fita, ita sam bata ga aibun abinda tayi ba amma shine har Mama zata ce tana fito na fito da ubangiji ita a wa? Amma a duba mata mana, yanzu da yaro daya ma yaya takeyi kullum cikin yi mata carin tana qazanta bata kula da yaron ake yi ballantana ace ta sake haihuwa nan kusa sun zamar mata jarirai biyu kenan. Kuma da zata ce zata mutu idan Allah yayi Haihuwa ce Ajalinta ai dole ta mutu kuma ko babu komai tayo shahada, duk baqaqen maganganu da bakin da suke mata a wanke mata su ta tafi lahira salin alin abinta.

Tsawar da Maman ta katsa mata akan ta fita ta bata guri ce ta dawo da ita hayyacinta ta miqe jiki na rawa ta bar dakin gaba daya ta tafi dakin Anty. A can ta dasa mata rashin mutunchin da bata samu damar yiwa Maman ba tana birgima tana kuka kamar yarinyar goye tana cewa ita dai a rabata da wannan cikin bazata iya ba.

Anty dai ganin abin tayi kamar ba'a hayyacinta take ba seta miqe ta tafi dakin Mama ta gaya mata, Umaimah na jiyo muryarsu a tsakar gida Antyn na ce mata tazo ta ga abinda takeyi anya lafiya tana jin motsinsu ta miqe da gudu ta afka dakin Anty ta banko qofa.
"Da ki tsaya mana da yau sena sauke miki duk wani iskanci da yake miki yawo akai yar banza me qeqashashshiyar zuciya kamar ta mutanen farko" ta fita ta bar Anty na jimami.

Yanzu Nuratu kuma tace me ita da nata cikin ya kai kusan wata shida yanzu idan ma befi ba gashi tana aiki ga hidimar gidan Amma daga ita har Mijinta farinciki suke da qaruwar da suka samu har ta yaye yarta Maman Mijin ta dauke mata ita kafin ta haihu se ita me zaman banza babu cas babu As ita ce zata ce bata son haihuwa kuma ta tabbatar da shi Khalil din baze ce baya so ba. "Kai wannan Umaimah dai jidalinta se Allah" ta fada a fili kafin ta koma tsakar gida taci gaba da ayyukanta.

Qarshe wunin daki tayi ranar dan abinci ma kamar wata yar birsin ta window ta saka Salma ta miqa mata shima seda taji Yunwa na neman ta halakata Anty ko duk uzurinta na cikin daki se haqura tayi dasu. Bayan an idar da sallar Magriba Ummu-salma tayi kiranta inji Abbansu. Badan tana jin tsoronsa ba da bazatajeba danta tabbayar da Mama ta gama karanta masa komai. Haka ta zura Hijabin Anty ta fito kanta a qasa ta wuce bangaren Abban.

A zaune ta tarar dasu, Abban, Mama, Khalil se Yaya Aminu. Ta samu can gefe daga bakin qofa ta zauna kafin tayi musu kudin goro gaba daya ta gaishe su.
"Yaya jikin naki?" Abba ya tambayeta cikin kulawa yana kallonka kafin ma ta amsa Mama tayi hanzarin cewa
"Alhaji tambayarta ma kakeyi yaya jikinta kamar ban sanar dakai abinda ta gama yi dazu ba?
Nida na zata tana zuwa zaka kwashe mun yar banza da Mari ka tumurmusata idan ka gama Yayanau ya dora nasa"

Seya yi murmushi yace
"Haba Mamansu ayi mata haquri badan ita ba ko dan abinda yake jikin nata" ya sake juyawa kan Umaimah yace
"Umaimah kiyi haquri kinji ko, ita haihuwa ce baiwace da kudi ko wata isa basa bawa mutum Allah ke bayarwa ga wanda yaso a sanda yaso. Karki sake furta bakyason kyautar da Allah yayi miki kije ki raine cikin ki ki haifa kiyi fatan Allah ya baki me Albarka wanda zeji qanki kinji ko?"

Seta daga masa kai hawaye nabin fuskarta. Nasiha ya sakeyi musu gaba daya Mama dai ta cika fam qiris take jira ta fashe, haka ya gama ya saka musu Albarka kafin yace su tashi su tafi dare yayi, Umaimah ce ta fara yin gada da sauri ta shige dakin Mama ta kwaso tarkacenta tana fitowa suka ci karo a bakin qofa. Aminu da Khalil na daga gefe suna magana Maman ta kalleta sama da qasa kafin ta juya kansu tace

"Ku zama shaida, idan har wani abu ya damu cikin jikin yarinyar nan bisa gangancinta ban yafe mata ba".
"Haba Mama haba Mama kalmar tayi tsauri da yawa kiyi haquri ko sauqaqa mata akwai fa qaddara zata iya fadawa akai" Aminu yayi saurin fada yana matsowa gaban Maman, seda ta harari Umaimah da ta daskare a gurin kafin ta sake kallonsa tace

"Na fika saninqaddara kuma nasan kuma san halin Umaimah sarai da kafaffiyar zuciyarta tunda ta furta bata so na san tabbas seta salwantar dashi toh taje na kuma fada idan har tayi sanadin cikin nan da kanta ban yafe mata ba" tana gama fada ta shige daki ta barsu a nan Umaimah ta fashe da kuka tana sakin kayan hannunta tace

"Tsine mun fa tayi Yaya" Aminu ya make bakinta yace
"A ina ta tsine mikin ke da bakinki babu abinda ya sani se janyo masifa, sharadi ta baki idan kuma kika saba kinji abinda ta fada. Ku wuce kuje zan lallabata idan ta huce ke kuma ki kula da abinda ta fada"

Tana Kuka Khalil ya kama hannunta suka fita shi gaba daya kansa ma ya rufe ya rasa bakin Magana, wannan tsakanin da Mama tayi mata ya masa dadi dan yasan tashin hankalin da ze sha akan cikin nan se Allah idan da ba'ayi haka ba amma kuma Maganar tata tayi tsauri da yawa.
Seda suka shiga mota aka fito da Mu'ayyad da yayi bacci Anty da kanta ta kawo shi, tana dakinta duk budurin da akayi dazu taqi fita ta gaji da lamarin Umaimah kullum babu sauqi se qarin ciwon kai.
Chapter 95 · 0% Book details