← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 267

Sashe 194

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zancen banza ma kenan yanzu kana nufin yarinyar tana gidan iyayenta kenan saboda kana tsoro ka gayawa matarka tayi tashin hankali ka gwammace ka fara nuna rashin Adalci a tsakaninsu tun gabanin su zauna tare ko? Dan ubanta ita ba'a aure ka aureta kake kuma zaune da ita duk mugun halinta shine har zaka gwammace ka cutar da wata saboda kar ran Umaimah ya sosu to yanzu da menene shirinka? Idan iyayenta basuyi magana ba kenan haka zaka bar musu ya tayi ta zama da aure akanta ko?"
Girgiza kai yayi kawai saboda jin yanda Abban yake magana cikin fusata se yaci gaba da cewa
"Saboda Allah Khalil se yaushe zaka zama namiji a cikin gidanka? Kayi aure haka Allah yaso kaima ba tsarinka bane se kuma meya faru da bazaka iya zaunar da ita ka gaya mata ba har se kazo kana rara gefe kana neman wanda ze tayaka gaya mata ita ba musulma bace ai tasa san lamarin aure abune da babu me shiryashi haka babu me hana faruwarsa idan Allah ya kawo shi shi se anyi babu makawa ni gaba daya ma kai ka bata mun rai yanda kake wani karya murya kana fadar kayi mata laifi cika umarnin ubangiji ne laifin da kayi mata kome?

To ko Abubakar be dauki Amarya ya kai mata ba ni ubanta zanje da kaina na dakko yarinyar na kai cikin gidan domin duk muna da Yaya idan kuma wani ya aure su ya jingine mana su haka ba zamu ji dadi ba dan haka babu ta yanda za'ayi mu bada goyon baya ayiwa yar wasu haka. Ka tashi ka tafi duk ma yanda zakayi a yau ka sanarwa da Umaimah kayi aure kuma idan har iyayen Amaryar a shirye suke a gobe su kai yarsu dakinta babu abinda za'a jira zan kira Abubakar din yanzu ina gaya masa" Abban ya qarasa maganar a fusace se Khalil ya daga kai ya kalleshi yana zare ido jin wani zazzafan hukunci daya zarce na Baba Abu.

Shida ya rugo gurinsu da fatan samun Agajin gaggawa amma shine za'a sake yi masa turin jeka ka mutu da wane qarfin guiwar ze doshi Umaimah kai da Alama Abba ya manta akan wa ake magana gaskiya. Maganar Mama Malika ce ta cece shi da taja numfashi ta ajiye tace
"Alhaji da akalama baka fahimci abinda yake nufi ba, aure fa aka daura masa yau sati daya Matarsa bata da labari, kamar ka manta wadda ake magana akai kake cewa gobe zaka saka akai yarinyar mutane gidan haba Alhaji kadai tsaya ka duba wannan abu dakyau tabbas qarin aure ba laifi bane amma yanda al'amarin ya afku kowa cece hakan ta fada akanta dole taji babu dadi kuma zata buqaci a bata lokaci ta samu nutsuwar zuciya"

Wani Kallo Abban dake danna waya yana neman number Baba Abu ya watsa mata kafin yace
"Tunda batun kishiya akayi ai dole yau ki rikida kibi bayan yarki, duk iya shegen da ta ringa tata masa ina keda bakinki kinsha ce masa yayi auran ashe duk maganar ba taje zuci ba kenan iya fatar baki kike yinta yanzu kuma da ubangiji ya zartar da hukuncinsa zaki ce wani ba'a kyau ba saboda ku mata akan kishiya duk bakinku daya toh aure dai an daura amarya kuma zata tare a gidan Mijinta kuma dole tayi haquri ta karbi qaddara a yanda tazo mata yawwa" yana gama fadar haka ya miqe yana sake jaddadawa Khalil akan ze kira Abubakar. Dakinsa ya shige ya bar Mama da Khalil daya zabga tagumi dana sanin zuwa gidan ya kamashi tunda gashi ya zama sanadin da Mata da Miji auran sama da Shekara Arba'in suna Musayar yawu a dalilinsa.

Kallonsa Mama tayi cikin sanyi tace
"Kace bata san da kayi aure bako?"
"Bata sani ba Mama kuma wlh ni ban boye mata da wata manufa ba tsoron yanda zata karbi abun ya saka har yanzu ban gaya mata ba, kuma auran a yanda ya faru nima babu sanina a ciki Allah ne yayi" Khalil ya fada cikin yanayina karaya se Mama ta daga masa hannu tace
"Na sani Khalil kuma koda kayi hakan da niyya ba kayi laifi ba, Umaimah tayi maka abubuwa da yawa da ta cancanci hukunci amma ka haqura ka jure, yanzu da ubangiji ya saukar da qudurarsa yayi mata sakamako da abinda take qi wanda shine silar duk abubuwan da ta aikata hausawa sukace gudun qaddara guzurin taradda ita ai ba yinka bane yin Allah ne kuma bata isa taja da hukuncinsa ba dan haka duk abinda zatayi dole tayi ta haqura, babu damuwa yanzu kaje gida kamar yanda Alhaji ya gaya maka ka sameta kayi mata magana ta yanda zata fahimta, nasan abin da wahala amma ciwon da zataji idan ta tsinci maganar a bakin wani ze ninka wanda idan kaine da bakinka ka gaya mata in sha Allahu kuma ina fatan ta karbi qaddararta da kyakykyawan yaqini, yanzu kaje gidan jimawa kadan idan Allah ya yarda zanzo".

Kallon Mama yake da idanunsa da suka bayyana tsoro qarara kamar ba Namiji ba yace
"Wlh Mama bazaniya ba, ranar dana gaya mata ina neman aure a mota muna tafiya ta fizgi kan sitiyari badan muna da sauran kwana a gaba yanzu da wata maganar akeyi, kiyi haquri Mama bana nufin cin fuska a gareki amma Umaimah bata da tunani akan Halin kishinta idanunta rufewa sukeyi a shirye kuma take da tayi fito na fito da kowa da komai haka duk matsayin mutum bata tunawa a sanda zuciyarta ta qeqashe, ta rantse mun yafi sau nawa akan seta kashe duk wadda tayi gangancin aurena. Ni kaina tasha maimaita mun cewar zata kasheni kuma ta kashe kanta ina tsoro Mama ina tsoron kar wani abu ya sameta a yanzu bazan yafewa kainaba saboda nine sila" ya qarasa maganar kamar ze fashe mata da kuka Mama kuwa tsabar kidima kasa ce maaa komai tayi se dafe qirji tayi da hannu biyu tana kallonsa.

Tabbas a halin da Umaimah take ciki bata buqatar tashin hankali ballan tana taji baqin labari akan abinda idan aka ajiye mata zabin mutuwa ko kishiya tabbas zata iya zabar ta mutu da dai ta hada Miji da wata yanzu yaya zatayi ta fahimtar da ita ta kuma samu ta sassauta zuciyarta ta karbi abun da kyakykyawar zuciya?
Numfasawa tayi ta kalli Khalil dake zabga zufa tace
"Babu abinda ze faru da yardar ubangiji kaje gida zanzo din"
"Toh Mama" ya fada yana yunqurawa, yanda kasan kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya ringa tafiya ji yakeyi gaba daya ma kamar ya sake dagula komai.

Khalil na fita Mama ta miqe cikin sanyin jiki ta iske Abban a daki yana waya data tabbatar da Baba Abu qanin Mahaifin Khalil ne bayan ya kashe wayar ya kalleta fuska a daure yace
"Ya akayi?"
Seda ta zauna a gefen gadon kafin tace
"Alhaji ina ganin kamar yanda yaron nan ya fada da za'ayi haquri zuwa ta sauka saboda kaga ba'a so me ciki ta ringa fuskantar tashin hankali. Sannan idan ka kalli Ita Umaimah a karan kanta ba abune me sauqi a gurinta ba aje mata da maganar kishiya, a baya kasan duk abubuwan da suka faru, a wai wai take jin Mijinta yana kulasu kaga irin tijara da diban Albarka babu wanda bata yiwa yaran mutane ba haka shima Khalil din be tsira ba, yanzu haka yace tace zata kashe duk wadda ta aure shi, ban yarda zata aikata ba amma zuciya sharrinta yana da yawa musamman idan ta hadu da fushi, gudun kar azo ana abun da be kamata ba kuyi haquri a barshi ya raba musu gida kamar yanda ya tsara wata biyun kamar yau ne hakan ze rage kaifin duk wata fitina da zata taso sannan ita kanta yarinyar se tafi samun nutsuwa dashi"

"Yaushe kika zama me son kai Malika? Yanzu a duniya har akwai abinda Yaron nan zeyiwa Umaimah da zakiga rashin kyautawarsa? Nawa tayi masa kafin wannan kuma idan kika kalli abun nan meye ma laifinsa a ciki? Daman ita jarabawar ubangiji babu ta inda bata zuwar wa mutum, Allah yakan jarabceka da abinda kake so kamar yanda shi ta zamar masa jarabawa haka nan idan yaga dama ya jarabceka da abinda kake qi ga Misali nan akan ita Umaiman dukka idan skayi haquri kayi tawakkali se kiga ka dace da rabauta a duniya da lahira kawai abinda ya rage miki a matsayinki na uwarta ki nuna mata muhimmancin haquri da tawakkalo sannan ta maida lamarinta ga Allah duk wani tashin hankali da zatayi babu abinda ze canza, babu wanda yasan Abinda Allah ya boye game da wannan auran idan ta matsa rabo yayi Ajalinta ai shikenan". Yanda Abban yake magana tamkar babu abinda ya dameshi, ganin baze fahimce ta ba yasa ta fita ta bashi guri jiki a matuqar sabule ta qarasa ayyukan da zatayi duk yanda Anty take ta rara gefe da son jin meya faru tayi mata banza, karyawar da bata iya yi ba kenan ta zauna jiran ya qarasa abinda yakeyi su fita fatanta Ubangiji ya sanyaya Zuciyar Umaimah ya bata haquri da juriya akan wannan al'amari daya fado mata.

Ita kadai ta fita saboda Abba wasu maqotansu da sukazo gurin Abba dan su tafi daurin auran tare da yake bikin Yaron wani maqocinsu ne ada dukda ya tashi daga layin amma har yanzu suna zumunchi sosai musamman shi Abba da yake kasuwarsu daya dan haka yana gaya mata uzurin nasa yace ko zata jira ya dawo tace Aa haka kuwa akayi da wuri ta fita dan ta rigashi barin gidan. Kai tsaye gidan Qanwarta Laure data daura aure babu jimawa satinta uku da tarewa kenan ta nufa. Sama sama suka gaisa da Angon Anty Lauren daya bude mata qofa,ta kalli qanwar Tata data ci uwar kwalliya da qananan kaya yanda kasan wata Titin Lagos ita a dole ga Amarya wani sabon takaici ya qumeta taja tsaki ta zauna akan kujera kawai ta rafka tagumi, data Sani Hafsa ta kira ko Hajiyayye sukaje tare.
Chapter 194 · 0% Book details