← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 267

Sashe 200

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta Umaimah tayi na wani lokaci tana qoqarin ta tuna a ina ta san fuskarta amma ta kasa
"Kinga Sumayya mun ma gama bari mu tattare mata gurin mu Alkhairin ne ya kawo mu ba tashin hankali ba" daya daga cikin masu cin abincin ta fada tana miqewa ragowar suka shiga tsince wanda ya zube a qasan, Umaimah data gama tunano inda ta san wadda aka kira da Sumayya qanwar Mansur ce to uban me ya kawo su gidan kuma koma mene duk fadin gurin Hajiyar be ishe su ha se an kawo mata mutane falo kuma ba'a gaya mata ba lallai mutanen nan sun raina mata wayo.
Gani tayi Sumayyan ta juya ta haye sama abunta yanda kasan dakinta ya saka Umaimah dakatar da ita da sauri tana cewa

"Ke ina zaki, kinyi hauka ne da zaki haye mun sama se kace gidanki?"
"Nan fa daya, falo dai da kikace naki ne mun bar miki amma baki da ikon hanamu hawa Sama tunda ba mallakinki ne ke kadai ba, da dakin yar uwarmu a gun kinga kuwa babu wnada ya isa ya bamu dokar sanda zamu shiga ko ya hanamu" Sumayya ta fada kafin ta juya taci gaba da hawa saman. Wata mulmulalliyar Ashar Umaimah ta kora kafin cikin Azama tabi bayanta. Rabon data hau saman harta manta amma yanzu saboda bala'i nacin ranta tsaf ta haye har suna bangazar juna da Sumayyan kai bakace da wani kaya a jikinta ba.

Qofar part din Khalil data gani a bude kuma nan Sumayyan ta shiga babu bata lokaci ta mara mata baya, sosai ta bude ido tana kallon Falon da aka qawata yayi kyau harya gaji da haduwa, daga kan Kujeru Zuwa labulale kayan kallo da sauran kayan kwalliyar falo babu abinda ba'a saka ba masu kyau da tsari. Wasu Samari biyu suka fito daga dakin da yake matsayin Master bedroom suka kalli Sumayya suna gaya mata sun gama. Daman suna shiga da Umaiman kitchen ta wuce abinta ta dakko kaskon da suka kunna garwashi dan haka tayi musu sannu tace su sauka qasa su karbi Abinci gasu nan fitowa yanzu zasu wuce.

Showglass din turaren wuta ta bude ta debi wanda zata zuba nan da nan qamshi ya fara tashi a gurin, bata ko nuna alamar tasan da tsayuwarta ba ta shige dakin da Samarin suka fito se Umaimah ta bita kamar Jani Talo, Sumayya ta ajiye Kasko ta wuce tana gyara zaman labule kafin ta kashe fitilar dakin ta dakko kaskonta ganin Umaimah tsaye a bakin qofa kamar wadda ta samu mantuwar tunani yasa cikin gatsali tace mata
"Malama ki fita zan kulle tunda nan ba dakinki bane"

"Ke da izinin ubanwa kuka shigo mun gida sannan wadannan kayan na wanene?" Umaimah data rasa tunanin da zatayi ta fada se Sumayya ta watsa mata wani banzan kallo kafin tace
"Da izinin uban wanda ya isa, kaya kuma ki tambayi Mijinki ze fiyi miki bayani kalar wanda qaramar qwaqwalwarki zata dauka ni da Allah Malama ki fita na kulle muna da abinda zamuyi inke baki dashi" ta janyo qofar garam ta rufe har tana buge Umaimah ba tayi wata wata ba kuwa ta finciko Sumayyan duk qibarta da yake a bazata abin yaje mata se gata wanwar a qasa Kaskon hannunta ya fadi qasa ya fashe wuta ta zube a qasan. Da sauri ta matsa tana dafe qugunta daya bugu, wata Qanwar Maman Humaira da ta bi bayansu saboda tsoron abinda ka iya faruwa tayi saurin kama Sumayya ta miqe tana mata sannu.

"Kan uban nan ni kika kayar wallahi sena nuna miki na fiki hauka a gidan nan" Sumayyan ta fada tana qoqarin fincike hannunta Umaimah ta kalleta cikin ido tace
"Tun kafin raina ya gama baci ku tattara tsiyarku ku fitar da ita daga gurin nan"
"Saboda gidan ki ne ko yaya? Ke ki qaddara ma gidanko ne tunda Mijinta yace nan ze ajiyeta baki isa ki hana ba kuma kaya sun shigo kenan kamar yanda me su take tafe gobe da yardar Allah gara ma ki Adana haukarki qila tayi miki amfani a gaba" Sumayya ta mayar mata se Umaimah ta sake zabura tayi kanta tana cewa
"Zan nuna miki hauka kuwa ganin idonki karku kwashe ku jira na dawo duk se kun gane kurenku" fuuuu ta fice daga falon ta sauka qasa, bangaren Hajiya ta nufa a fusace so takeyi taje taji da izin wa za'a ajiye wata a gidanta bama zata kira Khalil ba dan tasu daban seya gane kurensa wlh.

Hajiya na zaune da wasu Aminanta da suka zo mata Allah sanya Alkhairi ana ta maida zancen yanda abu ya faru Umaimah ta diro musu kamar Kirsimeti ta cake a tsakiyar falon tana haki qirjin Hajiya ya buga dum kafin kace me zufa ta fara keto mata a ranta fadi take ta faru ta qare wai anyiwa me dami daya sata.
"Hajiya bana buqatar sanin koma su waye wadancan kwanciyar hanka kowa na gidan nan su fitar mun daga gida da duk tsiyar da suka shiga da ita idanba haka ba na rantse da Allah se rankowa ya baci a gidan nan, saboda tsabar neman bala'i me ya hana ke ki sauko daga naki saman ki bashi ya saka matar seni ana mun hassada na sakata na wala a cikin gidana za'a kawo faccala a ajiye mun to wlh qaryane kuma har gaban abada na ci gida gara ma ku cire idonku daga kai".

Yanda kasan sakarkaru haka qawayen hajiya suka bude baki da hanci suna kallonta, Hajiya Uwani guda daga ciki tayi qarfin halin cewa
"Amma dai ke wannan yarinya duk inda kika fito ba yar arziqi bace ke, uwar data Haifi Mijinki kika iya tsayawa a gabanta kina gaya mata kausasan kalamai haka saboda baki da tarbiyya? Koda yake ma sakarya ce ke baki san abinda kike fada ba naga alamar Kishi ya taba miki kwakwalwa har baki gane abinda kikeyi to ki fita daga nan tun kafin na harzuqa nayi miki dukan tsiya a nan mara kunyar banza da wofi".

Tun kafin ta idar Umaimah taja uban Tsaki tana kallonta tace
"Idan ban kasa da mutum ba karya dauka" kafin ta sake kallon Hajiya da gaba daya ta muzanta tace
"Hajiya ki tashi ki fitar dasu tun kafin nayi abinda kowa ze zo yana nadama a cikin gidan nan"
"Kinga Umaimah ki nutsu, ni Babana ba yace kina Asibiti an kwantar dake ba?" Hajiya ta fada tana nufarta se Umaimah taja da baya tana cewa
"Saboda yasan munafuncin da kuka shirya ai shiyasa ya daukeni ya kaini Asibiti zanyi maganinku gaba daya yanzu" ta juya sukayi karo da Lubna wayar dake hannun Lubnan ta fadi qasa Umaimah ta bita da kallo saboda ganin wani hoto akai kamar na Khalil akan wayar Lubna ta tsugunna ta dauka har tayi gaba kuma ganin Umaiman ta tsaya ta dawo baya tana murmushi tace

"Aa ya na ganki haka baki shirya ba ko ke ba zakije ki taya Habibin naki murna ba bayan shi gashi can saboda zumudi ya kasa zama seda yabi Amarya gurin kwalliya, kalle su ki gani dan Allah basu dace ba" Lubnan ta qarasa tana nuna mata screen din wayarta. Video Khalil ne yake tafiya rungume da wannan yarinyar ta gidan su Mansur, dukda kwalliyar data sha irin ta Amare bata kasa ganeta ba saboda irin tsanar da tayi mata a zuciyarta, Khalil din ya riqeta a jikinsa yana dariya ita kuma tana boye fuskarta a jikinsa alamar Kunya bata san sanda ta fizge wayar daga hannun Lubna ba ta dawo da video daya qare farko, yanda ta kwale ido tana kallon wayar ka rantse kwalli tayi da Attaruhu take neman iska ta shiga ta fifita mata.

Ta maida video baya bayan ya qare yafi sau nawa duk a qoqarinta nason ganin abinda take ya canza daga Khalil dinta zuwa wani mutum amma hakan ta gagara, ta ko ina Video ya tabbatar da cewar Khalil ne dan video daukar kusa ne tar fuskokinsu suka fito kamar ma magana sukeyi cire sautin akayi ga kayan da suke jikinsa dasu ya barta a Asibiti yanzu wayasa da Key din mota dake riqe a hannunsa duk ta shaidasu se kuma meya rage da zata tabbatar da cewar Khalil ne?

"Kawo na nuna miki sauran naga kina ta maidashi baya" taji muryar Lubna a tsakiyar kanta, cikin Azama ta dago a abinda be wuci second daya ba ta rotsa wayar da qasa kafin ta saukewa Lubna kyakykyawan tukuicin Mari taci kwalarta cikin wata murya tace
"Idan kina so ki tsira da ranki da lafiyarki ki bani amsa kawai, Ina Khalil kuma wacece wannan dana gansu tare?"

Lubna kuwa Mari da shaqar da tayi mata a lokaci data sun shigeta, lokaci daya ta firgice da ganin yana yin Umaiman ba tareda bata lokaci ba kuwa ta bude baki dakyar saboda shaqar data sha tace
"Yana gurin Kwalliya yaje dauko Amaryarsa daga can ze kaita gurin da zasuyi Yinin biki"
"Amaryarsa? Yinin biki?" Ta shiga maimaitawa a fili abinda yasa ta sassauta riqon da tayiwa Lubna kenan har Qawayen Hajiya da suka kawo mata dauki suka samu nasarar karbarta daga hannun Umaimah nan ta durqushe kuwa ta shiga tari dan ta dandana mata qamshin mutuwa, matsa tayi mata bata wasa ba hakan ya tuna mata da dukan data taba lakada mata shekarun baya randa suka fara zuwa gidan da Yayarta.

A sannu kuma cikin nutsuwa Umaimah taja qafafunta ta qarasa inda Hajiya take zaune kamar dutse tun shigowar Umaiman ta dauke wuta, ta bude baki yafi sau goma amma ta gagara furta abinda take so ta fada saboda yanda kalmar tayi mata nauyi a qirji, a hankali ta lumshe idonta ta hadiye wani abu kafin ta budr ta sake kallon Hajiyar cikin wani irin sauti tace
"Hajiya nasan kina jina mu me Lubna take nufi da maganarta?"
Chapter 200 · 0% Book details